Jam'iyyar APC Ta Lallasa PDP a Zaben Cike Gurbi na Dan Majalisar Jigawa da Ya Rasu

Jam'iyyar APC Ta Lallasa PDP a Zaben Cike Gurbi na Dan Majalisar Jigawa da Ya Rasu

  • Jam'iyyar APC ta samu nasara a zaben cike gurbi da aka gudanar a mazabar Garki/Babura da ke jihar Jigawa
  • Dan takarar APC, Alhaji Rabiu Mukhtar, ya yi nasarar lallasa abokin hamayyarsa na PDP bayan ya samu mafi yawan kuri'u
  • An dai gudanar da zaben ne bayan dan majalisar da ke kan kujerar, Hon. Isa Yaro, ya rasu a watan Mayun shekarar 2024

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Jigawa - Ɗan takarar jam'iyyar APC, Alhaji Rabiu Mukhtar, ya lashe zaɓen cike gurbi na kujerar majalisar wakilai ta Garki-Babura a jihar Jigawa.

Yayin da Auwalu Isah Manzo na jam’iyyar PDP ya zo na biyu a zaben da aka gudanar ranar Asabar, 17 ga watan Agustan 2025.

APC ta lashe zaben cike gurbi a Jigawa
Alhaji Rabiu Mukhtar tare da Auwalu Isah Manzo a wajen yakin neman zabe Hoto: Malamin Zawiyyah, Abba Sarki Garki
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa jami'in tattara sakamakon zaben, Farfesa Salisu Ibrahim, ne ya bayyana hakan.

Kara karanta wannan

Kano: Duk da lashe kujera, NNPP ta yi fatali da sakamakon zaben Ghari, Tsanyawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa zaɓen ya kasance wanda babu rigima mai cike da gaskiya kuma sahihi.

Dan takarar APC ya lallasa na PDP a Jigawa

Dan takarar APC, Alhaji Rabiu Mukhtar ya samu kuri'u 38,449 yayin da na PDP, Auwal Isah Manzo ya samu kuri'u 13,519, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.

"Ni, Farfesa Sani Ibrahim Isma’il, na tabbatar cewa ni ne jami’in tattara sakamakon zaɓen cike gurbi na kujerar Babura-Garki da aka gudanar a ranar 16 ga watan Agusta, 2025."
"An fafata a zaɓen, kuma ’yan takara sun samu ƙuri’u kamar haka, Bilkisu Bashiru ta jam’iyyar A ta samu ƙuri’u 11, Ibrahim Habiba ta jam'iyyar AA ta samu ƙuri’u 5, Umar Bashiru na jam'iyyar ADC ya samu ƙuri’u 48 da Sale Sani na AAA ya samu kuri’u 446."
"Muktar Rabi’u Garki na APC ya samu kuri’u 38,449, Adamu Dahiru na APGA ya samu kuri’u 77, Umar Muhammad Gana na APM ya samu kuri’u 37, Abdullahi Usman na APP ya samu kuri’u 31, Sabo Salisu na NNPP ya samu kuri’u 2,931,Isa Auwalu na PDP ya samu kuri’u 13,519 da Muktar Babangida na ZLP ya samu kuri’u 31."

Kara karanta wannan

APC, PDP sun sha kashi a zaben cike gurbin Sanata Ubah da ya rasu

- Farfesa Sani Ibrahim Isma'il

Zaɓen, wanda aka gudanar a ranar Asabar, ya samu halartar jama’a da yawa tare da tsauraran matakan tsaro.

Alhaji Rabiu Mukhtar ya yi godiya

Alhaji Rabiu Mukhtar ya gode wa jama’a bisa zabarsa, inda ya yi alkawarin cika manufofin yakin neman zaɓensa.

APC ta samu nasara a zaben cike gurbi a Jigawa
Alhaji Rabiu Mukhtar wanda ya lashe zaben Garki/Babura a jihar Jigawa Hoto: Majidadin Rabiu Mukhtar Garki
Source: Facebook

Ya kuma roƙi waɗanda suka sha kaye da su yi haƙuri, tare da haɗa hannu wajen bunƙasa mazabar ta hanyar ayyukan ci gaba daban-daban.

Zaɓen dai ya gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da wata tashin hankali ba a rumfunan zaɓe da dama.

Zaɓen cike gurbin dai ya biyo bayan rasuwar tsohon wakilin mazabar, Hon. Isa Yaro, wanda ya rasu a ranar 10 ga watan Mayu, 2024, yana da shekaru 46.

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta tsara gudanar da zaɓen a ranar 16 ga watan Agusta, 2025, domin cike gurbin kujerar.

APC ta lashe zabe a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta samu nasara a zaben cike gurbi na mazabar Ghari/Tsanyawa a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Bayani dalla dalla: Yadda NNPP da APC suka lashe zabukan cike gurbi a jihar Kano

Dan takarar APC, Ya'u Garba Gwarmai ya lallasa abokin hamayyarsa na jam'iyyar NNPP, Yusuf Ali Maigado, bayan ya samu mafi yawan kuri'u a zaben.

An dai sanar da sakamakon zaben ne da safiyar ranar Lahadi, 17 ga watan Agustan 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng