INEC Ta Sanar da Sakamakon Zaben Cike Gurbi na Dan Majalisar Dokoki a Jihar Kano

INEC Ta Sanar da Sakamakon Zaben Cike Gurbi na Dan Majalisar Dokoki a Jihar Kano

  • Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kammala tattara kuri'un da aka kada a zaben cike gurbin dan Majalisar Shanono/Bagwai a Kano
  • Dan takarar NNPP, Ali Lawan Alhassan ne ya samu nasara da kuri'u mafi rinjaye a zaben da aka gudanar jiya Asabar, 16 ga watan Agusta, 2025
  • A sakamakon da INEC ta sanar, NNPP mai mulki ta samu kuri'u 16,198 yayin da jam'iyyar adawa watau APC ta samu kuri'u 5347

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Jam'iyyar NNPP ta lallasa babbar abokiyar hamayyarta watau APC a zaben cike gurbin da aka gudanar a mazabar dan Majalisar Shanono/Bagwai a Kano.

Sakamakon zaben ya nuna cewa NNPP mai mulkin Kano ta samu nasara a zaben dan majalisa mai wakiltar Shanono/Bagwai a majalisar dokokin jihar.

Hon. Ali Lawan Alhassan.
Hoton zababben dan Majalisar dokokin Kano mai wakiltar Shanono/Bagwai, Ali Lawan Alhassan Hoto: Ali Lawan Alhassan
Asali: Facebook

Gidan rediyon Freedom da ke Kano ta tabbatar da hakan a shafinsa na Facebook da safiyar yau Lahadi, 17 ga watan Agusta, 2025.

Kara karanta wannan

Babu labarin Fintiri da Atiku, INEC ta sanar da sakamakon zaɓen cike gurbi a Adamawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan baku manta ba, hukumar zabe ta kasa watau INEC ta gudanar da zabukan cike gurbi a mazabu daban-daban a fadin Najeriya ciki har da guda biyu a Kano.

NNPP ta samu nasara a Shanono da Bagwai

A mazabar Shanono/Bagwai, dan takarar jam'iyyar NNPP, Ali Lawan Alhassan ya samu nasarar zama zababben dan Majalisar jihar da kuri'u 16,198.

Dan takarar ya lallasa abokin adawarsa na jam'iyyar APC, wanda ya zo na biyu da kuri'u 5,347.

Hukumar INEC ce ta sanar da sakamakon bayan kammala tattara kuri'un da jama'a suka kada daga mazabun kananan hukumomin Shanono da Bagwal.

A sakamakon zaben da INEC ta sanar a hukumance, wanda shafin Kwankwason Tuwita ya wallafa a X, jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 159 yayin da ADC ta tashi da kuri'u 16.

Sai kuma jam'iyyar LP wacce ta samu kuri'u 18 da kuma SDP da ta samu kuri'a 4 kacal a zaben da aka kammala.

Kara karanta wannan

An samu rudani a sakamakon zaben akwatun Ministan Tsaron Najeriya, APC ta sha da kyar

Sakamakon zaben Shanono/Bagwai

ADC - 16

APC - 5,347

LP - 18

NNPP - 16,198

PDP - 159

SDP - 4.

Baturen zaben Shanono/Bagwai, Farfesa Hassan Adamu Shitu ne ya bayyana wannan sakamakon da misalin karfe 12:36 na safiyar yau Lahadi.

Ya ayyan adan takarar NNPP, Ali Lawan Alhassan Kiyawa a matsayin wanda ya samu nasara da kuri'u mafi rinjaye bayan da ya cika duk sharuddan doka.

PDP ta lallasa APC a akwatun ministan tsaro

A wani labarin, kun ji cewa PDP ta samu nasara a rumfar zaben da ministan tsaron Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar ya kada kuri'a a Babura, jihar Jigawa.

Mazabar dan Majalisar Garki da Babura a Majalisar Wakilai ta Tarayya na daya daga cikin mazabun da aka gudanar da zaben cike gurbinsu ranar Asabar da ta wuce.

Rahotanni sun nuna cewa APC ta sha kaye a hannun PDP a rumfar zabe ta 001 da ke makarantar Firamare ta Babura Kofar Arewa, wurin da Badaru ya yi zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262