An Samu Rudani a Sakamakon Zaben Akwatun Ministan Tsaron Najeriya, APC Ta Sha da Kyar
- Sakamakon zaben cike gurbi a mazabar dan Majalisar Wakilai mai wakilantar Garki da Babura, jihar Jigawa ya fara fitowa
- A ranar Asabar, 16 ga watan Agusta, 2025, hukumar INEC ta gudanar da zaben cike gurbi a mazabu daban-daban a fadin Najeriya
- An yada labarin cewa PDP ta samu nasara a rumfar zaben da ministan tsaro ya kada kuri'arsa a Babura, amma labarin ba haka yake ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Jigawa - An samu rudani kan sakamakon zaben akwatun da ministan tsaron Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar ke kada kuri'arsa a jihar Jigawa.
Da farko an fara yada labarin cewa jam'iyyar adawa ta PDP ta samu nasara da gagarumin rinjaye a rumfar zabe ta 001 da ke makarantar Firamare ta Babura Kofar Arewa.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa a wannan rumfar zabe ne Badaru, tsohon gwamnan Jigawa ya kada kuri'arsa a zaben cike gurbin dan Majaliaar wakilai na Garki/Babura.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai mazauna karamar hukumar Babura musanta wannan labari, inda suka ce ba a wannan rumfar zabe Badaru ke kada kuri'a ba.
A shafinsa na Facebook, Adamu Bala Babura ya tabbatar da cewa rumfar zabe ta 002 da ke makarantar Arewa firamare ce akwatun zaben minista.
Ministan tsaro ya kada kuri'arsa a Jigawa
A jiya Asabar, 16 ga watan Agusta, 2025, hukumar INEC ta kasa ta gudanar da zabukan cike gurbi a mazabun yan Majalisar tarayya da na jihohi a fadin Najeriya.
Ministan tsaro na yanzu, wanda jigo ne a jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan Jigawa ya kada kuri’arsa a mazabarsa dake Babura cikin tsauraran matakan tsaro.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa ya bar rumfar zaben ba tare da ya yi magana da manema labarai ba, kamar yadda Punch ta rahoto.o

Kara karanta wannan
Jam'iyyar APC ta lallasa PDP a zaben cike gurbi na dan majalisar Jigawa da ya rasu
Sakamakon da INEC ta sanar da akwatun Badaru
A sakamakon da INEC ta sanar rumfar zaben nasa, APC ce ta samu nasara da kuri’u 188, yayin da PDP ta tashi sa kuri'u 164.
An gudanar da zaben a duk fadin mazabar cikin tsauraran matakan tsaro domin tabbatar da komai ya tafi cikin lumana.
Jami’an ’Yan Sanda, NSCDC, Hukumar Shige da Fice (NIS) da wasu jami’an tsaro sun kasance a wuraren zabe daban-daban da muhimman wurare a ƙananan hukumomin Babura da Garki domin tabbatar da tsari da kwanciyar hankali.

Source: Facebook
Karamar ministar ilimi ta yi jawabi a Jigawa
A rumfar Primary Yamma (005), Karamar Ministar Ilimi, Hajiya Suwaiba Ahmad, ta yaba da yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, sannan ta nuna kyakkyawar fatan cewa APC za ta yi nasara a ƙarshe.
Sai dai, wasu mazauna yankin sun ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum, inda ake gudanar da kasuwanci a wasu sassan mazabar.
Haka kuma, yawancin rumfunan zabe sun shaida fitowar jama’a da yawa wajen kada kuri’a. Yanzu dai ana dakon sakamakon karshe a mazabar Garki/Babura.

Kara karanta wannan
APC ta sha kasa a zaben cike gurbi, PDP ta kwato kujerar majalisar wakilai a Ibadan
Rikici ya mamaye zaben cike gurbin Sanata
A wani rahoton, kun ji cewa rigingimu da zanga-zanga sun mamaye zaben cike gurbin Sanatan Anambra ta Kudu, Andy Ubah wanda ya rasu.
An rahoto cewa zaben na ranar Asabar a mazabar Anambra ta Kudu cike yake da rikici da tarzoma, lamarin da ya kai ga kama wasu ’yan jam’iyyar APC.
Wannan lamari ya sa wasu matasa a yankin suka fantsama zanga-zanga bisa zargin gwamnatin Anambra ta jam’iyyar APGA da cin zarafin yan adawa.
Asali: Legit.ng
