An Gano Masu Kudin da Jami'an Tsaro Suka Kama a Hannun Wakilin PDP a Kaduna
- Jam'iyyar PDP reshen jihar Kaduna ta amince cewa makudan kudin da aka kama a hannun Shehu Aliyu Pantagi mallakin ta ne
 - Shugaban PDP na jihar Kaduna ya ce sabanin zargin da ake yi, jam'iyyar ta tanadi wadannan kudi ne domin harkokin zabe da alawus na wakilai
 - Ya zargi gwamnatin Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani da yunkurin danne yan adawa ta hanyar amfani da jami'an tsaro
 
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - PDP reshen Jihar Kaduna ta kare ɗan jam’iyyar, Shehu Aliyu Pantagi, wanda jami’an tsaro suka kama da kuɗi kusan Naira miliyan 26.
Babbar jam'iyyar adawa ta jaddada cewa kuɗin an ware su ne kawai domin harkokin gudanar da zaɓe da alawus ɗin wakilan PDP, ba don sayen ƙuri’u ba.

Source: Facebook
Shugaban PDP na jihar, Sir Edward Percy Masha, ne ya bayyana hakan yayin da yake hira da yan jarida a Kaduna a yau Asabar, kamar yadda The Nation ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa zargin da aka dora wa Shehu Pantagi ba komai bane face “ƙarya, mummunan ƙage da kuma bita da kullin siyasa."
Me PDP za ta yi da kudi har N26m?
A cewaraa, kuɗin da aka kwace daga hannunsa, an tanade su ne domin taimaka wa aikin wakilan PDP da jami’ai a lokacin zaben cike gurbi da ake yi a fadin Kaduna.
Ya ce duk wata jam’iyya tana ɗaukar wakilai, masu sa ido da masu tattara sakamakon zaɓe a kowane mataki tun daga rumfunan zabe, kuma irin waɗannan tsare-tsare suna buƙatar kuɗi.
Shugaban PDP ya ce:
“Kuɗin nan da aka kwace na harkokin gudanar da zaɓe ne. Muna da mazabu 169, idan aka ninka adadin wakilai, masu sa ido da masu tattara sakamako da alawus ɗinsu, za a samu fiye da Naira miliyan 30.
"Wannan shi ne gaskiya. To yanzu an ce wai don sayen ƙuri’u ne, wannan yaudara ce kuma raina hankali ga ’yan Najeriya.”

Kara karanta wannan
Zabe ya dauki zafi, ana zargin an sace yar takarar majalisar tarayya da wasu 25 a Kaduna
Kaduna: PDP ta koka da abubuwan da ke faruwa
Sir Percy Masha ya koka cewa jam’iyyar PDP ta jima tana fama da tsangwama daga jami’an tsaro da suke aiki, “bisa umarnin gwamnatin Jihar Kaduna.”
Ya zargi jam’iyya mai mulki APC da amfani da hukumomin gwamnati wajen razana ’yan adawa

Source: Facebook
Shugaban PDP ya bayyana cewa yawan kama mutane da kwace kuɗaɗe alama ce ta damuwa da tsoron faduwa daga ɓangaren APC, rahoton Tribune Nigeria.
"Idan APC na da tabbacin abin da ta aikata, su fito filin zaɓe su bar mutane su yanke hukunci. Yin amfani da dabarun kama-karya da yaudara yana nuna tsoron faduwa ne.”
Ana zargin srace 'ya takarar PDP a Kaduna
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta yi zargin cewa jami'an tsaro sun yi garkuwa da yar takarar kujerar Majalisar Wakilai a mazabar Chikun/Kajuru da wasu magoya baya 25.
PDP ta yi zargin cewa dakarun tsaron hadin gwiwa na gwamnatin jihar Kaduna ne suka aiwatar da wannan aikin, sai dai ba a samu wata hujjar zancen ba.
Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da manyan hafoshin tsaro da shugaban yan sanda su kawo dauki a Kaduna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
    