Zabe Ya Dauki Zafi, Ana Zargin An Sace Yar Takarar Majalisar Tarayya da Wasu 25 a Kaduna

Zabe Ya Dauki Zafi, Ana Zargin An Sace Yar Takarar Majalisar Tarayya da Wasu 25 a Kaduna

  • Jam'iyyar PDP ta zargi gwamnatin Kaduna da musgunawa mambobinta yayin da zaben cike gurbi ya kankama yau Asabar
  • PDP ta yi zargin cewa jami'an tsaro sun yi garkuwa da yar takarar kujerar Majalisar Wakilai a mazabar Chikun/Kajuru da wasu 25
  • Ta bukaci jami'an tsaro su gaggauta sakin Princess Esther Ashivelli Dawaki da sauran wadanda suka kama ba tare da sharadi ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna -Jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna ta zargi jami’an tsaro da yin garkuwa da yan takararta ta Majalisar Wakilai a zaben cike gurbi na Chikun/Kajuru, Princess Esther Ashivelli Dawaki, tare da magoya baya 25.

Shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Sir Edward Percy Masha, ne ya yi wannan zargi a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 16, ga watan Agusta, 2025.

Kara karanta wannan

An gano masu kudin da jami'an tsaro suka kama a hannun wakilin PDP a Kaduna

Yan takarar PDP tare da magoya bayanta a Kaduna.
Hoton yar takarar majalisar wakilai tare da magoya bayanta a lokacin da take kamfe a mazabar Chikun/Kajuru Hoto: Comr Abdulmalik Yusuf
Source: Facebook

Jam'iyyar PDP ta zargi Gwamnatin Uba Sani

PDP ta yi zargin cewa dakarun tsaron hadin gwiwa na gwamnatin jihar Kaduna da ake kira “Operation Fushin Kada” ne suka aiwatar da wannan aikin, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam’iyyar adawar ta bayyana cewa jami’an tsaron sun kutsa cikin otal din City Den da ke Malali, suka karya kofar ɗaki suna neman shugaban kwamitin kamfen PDP, Hon. Hussein Ahmed-Kero.

"Saboda ba su same shi ba, sai suka kama yar takararmu, Dawaki da sauran mutane suka tafi da su," in ji PDP.

PDP ta bayyana wannan abin da aka yi a matsayin “tsananin cin zarafi, razana da rashin hankali”, wanda take zargin an shirya shi ne ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani.

PDP ta bukaci saki mambobinta da aka kama

Jam’iyyar PDP ta nemi a saki 'yar takararta da magoya bayanta da aka kama nan take ba tare fa gindaya wani sharadi ba.

Kara karanta wannan

Matasa sun lakadawa wakilin PDP duka kan zarginsa da rike musu katunan zabe

Har ila yau, PDP ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Darakta Janar na DSS, Babban Hafsan Sojoji da Babban Hafsan Tsaron Najeriya da su shiga cikin lamarin.

Ta kuma yi kira ga kungiyoyin farar hula da “duk masu kishin dimokuraɗiyya” da su tashi tsaye wajen adawa da abin da ta kira kutse da mulkin danniya a Kaduna.

Gwamna Kaduna, Malam Uba Sani.
Hoton Gwamna Uba Sani a fadar gwamnatinsa da ke Kaduna Hoto: Uba Sani
Source: Twitter

'Alamu sun nuna jam'iyyar APC ta tsorata'

A cewar PDP, wannan abin da ake zargin jam’iyyar APC ta yi na nuna girman yadda ta tsirata kuma take fargabar faduwa zaben da ake yi yau Asabar, in ji rahoton Vanguard.

PDP ta tabbatar wa ’ya’yanta da magoya bayanta cewa za ta ci gaba da bayyana yadda lamarin ke tafiya, tare da jaddada aniyar ta na tsayawa tsayin daka wajen kare haƙƙoƙin dimokuraɗiyya a Kaduna.

Jami'an tsaro sun kama wakilin PDP a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa yan sanda da jami'an DSS sun cafke wani mutumi da ake zargin wakilin PDP ne dauke da kudi ₦25,963,000 a Kaduna.

Ana zargin cewa za a yi amfani da wadannan kudade wajen sayan ƙuri’u a zaben cike gurbin da aka fara yau Asabar a jihar.

Rahotanni sun ce dan PDP ya shiga hannu ne a daidai lokacin da yake tsara yadda za a rarraba kuɗin da aka tanada don sayen ƙuri’a a zaben dan Majalisar Tarayya na Chikun/Kajuru.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262