Asiri Ya Tonu: An Kama Wakilin PDP a Otal Dauke da Kusan Naira Miliyan 26 a Kaduna

Asiri Ya Tonu: An Kama Wakilin PDP a Otal Dauke da Kusan Naira Miliyan 26 a Kaduna

  • Yan sanda da jami'an DSS sun cafke wani mutumi da ake zargin wakilin PDP ne dauke da kudi ₦25,963,000 a jihar Kaduna
  • An kama dan PDP, Shehu Fantagi a wani fitaccen otal a cikin garin Kaduna yayin da ake shirin gudanar da zaben cike gurbi na yan Majalisa
  • Rundunar yan sanda ta gargadi mazauna Kaduna cewa babu wanda za ta daga wa kafa idan aka kama shi da hannu a yunkurin lalata tsarin zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Hukumar Tsaro ta DSS da ’Yan Sanda sun kama wani da ake zargi ɗan jam’iyyar PDP ne, mai suna Shehu Fantagi, dauke da kusan Naira miliyan 26 a Kaduna.

Ana zargin cewa mutumin wakilin PDP ne kuma zai yi amfani da wadannan kudade wajen sayan ƙuri’u a zaben cike gurbi da za a gudanar a Jihar Kaduna yau Asabar.

Kara karanta wannan

An gano masu kudin da jami'an tsaro suka kama a hannun wakilin PDP a Kaduna

Jami'an DSS sun yi kamu a Kaduna.
Hoton jami'an DSS a bakin aiki, tare da wakilin PDP da aka kama da kudin sayen kuri'u a Kaduna Hoto: @OfficialDSSNG
Source: Twitter

The Nation ta ruwaito cewa an cafke Shehu Fantagi a daren Juma’a a wani otel da ke cikin birnin Kaduna, awanni kafin fara zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an tsaro sun kama dan PDP a otal

Rahotanni sun ce dan PDP ya shiga hannu ne a daidai lokacin da yake tsara yadda za a rarraba kuɗin da aka tanada don sayen ƙuri’a a zaben dan Majalisar Tarayya na Chikun/Kajuru.

Wata majiya daga jami’an tsaro ta tabbatar da cewa an kama shi dauke da kuɗaɗe da suka kai miliyoyi, da ake kyautata zaton an shirya su ne domin lalata sahihancin zabe.

Yadda aka kama wakilin PDP da kusan N26m

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, a wata sanarwa da ya fitar, yau ranar Asabar ya ce:

"A wani ci gaba da aka samu sakamakon haɗin gwiwar hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa zabukan cike gurbi a Jihar Kaduna sun gudana cikin lumana, ’yan sanda da DSS sun yi nasarar kama wani mai sayen ƙuri’u."

Kara karanta wannan

Matasa sun lakadawa wakilin PDP duka kan zarginsa da rike musu katunan zabe

"Da misalin ƙarfe 03:30 na yau Asabar, an kama wani Shehu Aliyu Patangi a wani fitaccen otal da ke kan titin Turunku a cikin birnin Kaduna, inda aka gano jimillar kuɗi har ₦25,963,000 a wurin wanda ake zargi.
"Ana zargin cewa wadannan kudade an tanade su domin sayen kuri'un jama'a a zaben cike gurbi."
Dakarun yan sandan Najeriya.
Hoton yan sandan Najeriya sun motsa jiki a kusa da ofishinsu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Rundunar yan sanda ta yi gargadi

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, CP Rabiu Muhammad, ya godewa sauran hukumomin tsaro bisa haɗin kai da gaggawar daukar mataki.

Ya kuma gargadi jama’a da cewa duk wanda aka samu da hannu a yunƙurin lalata tsarin zabe, komai matsayinsa, zai fuskanci cikakken hukunci, Daily Trust ta rahoto.

An sa dokar hana zirga-zirga a Kaduna

A wani labarin, kun ji cewa rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta sanar da sanya dokar haramta zirga-zirga a wasu kananan hukumomi hudu.

Dokar haramta zirga-zirgar za ta fara ne daga ƙarfe 12:00 na dare ranar Asabar a kananan hukumomin Sabon Gari, Zariya, Chikun da Kajuru da Kaduna.

Kakakin ‘Yan sandan ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin tsare-tsaren tsaro da aka dauka kafin zabukan cike gurbi a yankunan da abin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262