Mamba Ya Rikita Majalisa, An Yi Masa Barazana da Ya Yi Zargin Biyan N3m kan Kuduri

Mamba Ya Rikita Majalisa, An Yi Masa Barazana da Ya Yi Zargin Biyan N3m kan Kuduri

  • Majalisar wakilai ta bukaci Hon. Ibrahim Auyo ya kawo hujja kan zargin cewa ana biyan kuɗi kafin gabatar da kudiri
  • Auyo ya ce 'yan majalisa na biyan har Naira miliyan uku kafin gabatar da kudiri, tare da bin kafa daga sauran mambobi
  • Kakakin majalisar ya ce idan Auyo bai gabatar da hujja ba, za a kai shi gaban kwamitin ladabtarwa na majalisar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta kalubalanci mambanta daga jihar Jigawa kan zargin da ya yi mata.

Majalisar ta bukaci Hon. Ibrahim Usman Auyo ya gabatar da hujjoji kan zargin da ya yi cewa ana biyan kuɗi kafin gabatar da kudiri.

Majalisa ta titsiye mambanta kan zarginta da cin hanci
Yan majalisa yayin da suke zama a birnin Abuja. Hoto: House of Representatives.
Asali: Facebook

Zargin da Hon. Auyo ya yi ga majalisa

Hakan ya biyo bayan zargin da dan majalisar ya yi kan cewa sai an biya kudi kafin a bar mamba ya gabatar da kudiri, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara shirin rage bashin N4trn ga kamfanonin wutar lantarki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Auyo, dan jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar Hadejia/Auyo/Kafin Hausa, ya yi zargin ne a gaban yan mazabarsa.

Ya shaida cewa 'yan majalisa na biyan har Naira miliyan uku kafin su gabatar da irin waɗannan abubuwa a zauren majalisar.

Ya kara da cewa tun daga 2015 da aka zabe shi, babu wani daga Auyo, Hadejia ko Kafin Hausa da ya taba ba shi kudiri don gabatarwa.

Majalisa ta bukaci mambanta ya kawo hujja kan zargin da ya yi
Hon. Tajudden Abbas yayin zaman majalisa a Abuja. Hoto: House of Representatives.
Asali: Facebook

Zargin da Hon. Auyo ya yi wa Majalisa

Hon. Auyo ya ce har ma waɗanda ake gabatarwa ana biyan kuɗi kafin su shiga, inda ake cajin Naira miliyan uku, biyu ko ɗaya.

Bayan haka kuma, ya ce dole sai an yi ta bin kafa kan sauran mambobi 360 kafin a amince da kudirin.

Wannan magana ta jawo suka daga wasu daga mazaɓarsa bisa rashin yawan gabatar da kudiri a majalisa wanda ya saka shi zargin.

Barazanar da majalisa ta yi ga Hon. Auyo

Kara karanta wannan

Ana batun rashin lafiyar Tinubu, Gwamna Radda zai tafi jinya domin duba lafiyarsa

A wata sanarwa da kakakin majalisar, Akin Rotimi, ya fitar da shafin majalisar ya wallafa a X, ya ce idan Auyo bai gabatar da hujjoji ba, za a mika batun ga kwamitin ladabtarwa.

Rotimi ya ce majalisar tana da tsari da doka na gaskiya da bayyani wajen gabatar da kudiri da ƙudirin ƙuduri, bisa tsarin kundin tsarin mulki da dokokin majalisar.

Ya ce zargin cewa ana ɗaukar irin waɗannan abubuwa a matsayin aikin kwangila na cin hanci, ya saba wa tsarin majalisar, kuma dole ne a fayyace shi.

Rotimi ya kara da cewa majalisar wakilai tana da niyyar kiyaye mutunci da haɗin kai tsakanin mambobi.

Dan majalisa ya gyara makabartu a Zamfara

Mun ba ku labarin cewa dan majalisar wakilan Najeriya mai wakiltar Tsafe da Gusau a jihar Zamfara ya dauki nauyin gyaran makabartu a mazabarsa.

Hon. Kabiru Maipalace ya kaddamar da aikin makabartun har guda 80 domin su kasance cikin yanayi mai kyau inda mutane suka yaba masa kan wannan kokari na shi.

'Dan majalisar ya bayyana cewa aikin gyaran makabartun yana da matukar muhimmanci domin yana kare bala'o'i da ke faruwa a wuraren da ke zama barazana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.