'A Kula': Gwamnatin Tarayya Ta Tura Gargaɗi ga Ma'aikata kan Shiga Siyasa

'A Kula': Gwamnatin Tarayya Ta Tura Gargaɗi ga Ma'aikata kan Shiga Siyasa

  • Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Walson-Jack, ta gargadi ma’aikata kan shiga lamarin siyasa a Najeriya
  • Walson-Jack ta bukaci su guji shiga harkokin siyasa yayin da suke ofis, tare da kuma kiyaye ka’idojin aikin da suke yi
  • Ta ce hukuncin kotu ya amince ma’aikata su rike katin jam’iyya, amma hakan ba ya nufin su shiga harkar siyasa kai tsaye

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Yayin da zaben 2027 ke gabatowa, Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Esther Walson-Jack, ta gargadi ma’aikata.

Walson-Jack ta gargade su da su guji shiga harkokin siyasa yayin aiki musamman da aka doshi zaben 2027.

Tinubu ya gargadi ma'aikata kan lamarin siyasa
Bola Tinubu yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

An tunawa ma'aikata dokar hana su siyasa

Hakan na kunshe a wasikar gargadi da Walson-Jack ta bayar yayin taron tattaunawa da jama’a a Abuja, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Fasinjoji 58 sun gamu da matsala, an hana su shiga jirgin sama a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai doka a Najeriya da ta hana ma'aikatan gwamnati shiga lamuran siyasa ko su nuna ɓangaren da suke goyon baya.

Wannan doka ita ke takawa ma'aikata birki domin kare kansu daga shiga matsala musamman lokutan siyasa a Najeriya.

Kokarin da shugabar ma'aikata ke yi

Shugabar ma'aikata a Najeriya, Walson-Jack kullum tana kokari wurin tabbatar da cewa ma'aikata sun bi ka'idojin aiki.

Ko a kwanakin baya ma, ta gargadi kowane ma'aikaci ya tabbatar ya iya rera sabon taken ma'aikata da aka kawo kasar.

Gwamnatin Tarayya ta dawo da sabon taken ma'aikatan domin kara musu kaimi da kishin kasa.

Shugabar ma'aikatan, Walson-Jack ta tabbatar da haka inda ta ce hakan yana da fa'ida..

Walson-Jack ta gargadi ma'aikata kan shiga siyasa
Walson-Jack yayin wani taro a Abuja. Hoto: Didi Walson-Jack.
Asali: UGC

Siyasa: Wace rawa aka yarda ma'aikaci ya taka?

Walson-Jack ta jaddada cewa ma’aikatan gwamnati dole su kasance masu adalci da bin dokokin aikin gwamnati.

Ta yi bayani kan hukuncin kotun koli, inda ta ce an amince ma’aikata su iya rike katin jam’iyyya don kare hakkinsu.

Kara karanta wannan

Tsohuwar hadimar Buhari ta rubuta masa wasika a kabari, ta fadi yadda APC ta lalace

A cewarta:

“Hukuncin tsoho ne, har yanzu yana aiki, amma ya gargadi cewa dole ma’aikata su kiyaye sharuddan da ka’idojin aikin gwamnati.
"Kowa ya san ma’aikacin gwamnati ya zama ba ya cikin siyasa. Babban aikinka shi ne zama mai adalci da yin aikinka.”

Ta yi gargaɗi cewa ma’aikata ba za su shiga harkar siyasa kai tsaye ba, dole su yi wa gwamnatin da ke kan mulki aiki.

Walson-Jack ta ce duk wanda ya karya wannan ka’ida za a hukunta shi gwargwadon dokokin da ke cikin tsarin aikin ma’aikatan gwamnati.

Tinubu zai kashe N3.6trn kan gadar Legas

Mun ba ku labarin cewa gwamnatin tarayya ta ce gyaran gadar 'Third Mainland' zai ci Naira tiriliyan 3.8, yayin da ginin gadar zai ci Naira tiriliyan 3.6.

Gwamnati ta ce babbar gadar ta lalace ne sakamakon tono yashi da ake yi ba bisa ka’ida ba, zaizayar ƙasa, da lalacewar ƙarfe.

A taron majalisar FEC, an amince a gaggauta gyaran wasu gadoji a Najeriya, ciki har da gadar Jalingo, Keffi, Mokwa da Jebba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel