El Rufai: Gwamnatin Kaduna Ta Karyata Zargin ADC ana Shirin Zaben Cike Gurbi

El Rufai: Gwamnatin Kaduna Ta Karyata Zargin ADC ana Shirin Zaben Cike Gurbi

  • Gwamnatin Kaduna ta karyata zargin shirin tafka maguɗin zaɓe a Chikun/Kajuru, Zariya da Sabon-Gari yayin shirin zaben cire gurbi
  • Gamayyar ADC da SDP ta zargi gwamnati da cin hanci, amfani da ‘yan daba da kuma shirin dagula tsaro a lokacin zaben ranar Asabar
  • Gwamnatin Uba Sani ta ce gamayyar ta san za ta sha kaye, ta gargadi masu yaɗa ƙarya kuma ta shirya ɗaukar matakin shari’a a kansu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Gwamnatin jihar Kaduna ta yi watsi da zargin da gamayyar jam’iyyun ADC da SDP suka yi cewa tana shirin tafka maguɗin zaɓe a zaɓen cike-gurbi.

Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta kammala shirin gudanar da zabe da Chikun/Kajuru da kuma mazabun majalisar jihar a Zariya da Basawa a yankin Sabon-Gari.

Kara karanta wannan

"Ba gudu, ba ja da baya," Naja'atu ta karfafa gwiwar tambuwal bayan kamen EFCC

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Channels TV ta wallafa cewa gwamnatin, wannan ikirari abin dariya ne daga ragowar ‘yan siyasar tsohon gwamna Nasir El-Rufai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani taron manema labarai da aka yi a Kaduna, jagoran gamayyar kuma mataimakin shugaban ADC na yankin Arewa maso Yamma, Jafaru Sani, ya zargi gwamnatin APC a Kaduna da shirin tafka maguɗin zaɓe.

Gwamnatin Kaduna ta soki 'yan adawa

Daily Post ta wallafa cewa gamayyar ta kuma zargi cewa ana bai wa manyan jami’an INEC filaye a matsayin cin hanci.

Haka kuma ta zargi INEC da naɗa wani tsohon Sanata da aka taɓa tuhuma da tayar da rikicin zaɓe don jagorantar rabon kuɗin sayen ƙuri’u da karya tsaro.

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani da Nasir El Rufa'i
Hoton gwamna Uba Sani da El Rufa'i a lokuta mabambanta Hoto: Uba Sani Nasir El Rufa'i
Source: Facebook

Ya ce:

“Za mu ƙi zama shiru yayin da ‘yan siyasa masu neman damar da ba su samu ba ke ɓata sunan gwamnatinmu tare da zagin jami’ai marasa laifi da zarge-zargen banza ba tare da hujja ba.”
“A halin yanzu, gwamna yana Chikun yana ƙaddamar da aikin gina titin Romi–Karatudu — wani gari da aka yi watsi da shi kuma aka rusa shi a ƙarƙashin mulkin El-Rufa’i na tsawon shekaru takwas.”

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya yi wa matasa albishir, ya faɗi tanadin da gwamnatinsa ta yi masu

Gwamnati: "Za mu dauki matakin kan 'yan adawa"

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Ahmed Maiyaki, ya bayyana zargin a matsayin marar tushe kuma cike da makirci.

Ya ce gwamnati ba ta da wani hurumi wajen gudanar da zaɓe saboda aikin hukumar INEC ne kawai, tare da gargadin cewa gwamnati ba za ta zauna lafiya a ci gaba da ɓata sunanta ba.

Ya ƙara da cewa gwamnati ta umarci lauyoyinta su binciki wannan zargi don ɗaukar matakin shari’a da zai iya shafan mutanen El-Rufai.

El Rufa'i ya tsinewa gwamnatin Kaduna

A wani labarin, mun wallafa cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya bayyana dalilinsa na sukar gwamnatin jihar a ƙarƙashin Gwamna Uba Sani.

Ya bayyana cewa yana da shakku kan yiwuwar gudanar da adalci a zaɓukan da gwamnatin jihar, inda ya nemi hukumar INEC da ta yi zaben gaskiya ranar Asabar a jihar Kaduna.

A hirar, tsohon gwamnan ya yi alfahari da yadda gwamnatinsa ta gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci a lokacinsa har ya bai wa sauran jam’iyyu hakkinsu bayan samun nasara a zaɓe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng