Kanada: An Ta da Jijiyoyin Wuya da Kotu da Ayyana PDP da APC Ƙungiyoyin Ta'addanci

Kanada: An Ta da Jijiyoyin Wuya da Kotu da Ayyana PDP da APC Ƙungiyoyin Ta'addanci

  • Wata kotun Kanada ta yanke wani hukunci kan manyan jam'iyyu biyu a Najeriya da suka hada da APC mai mulki da PDP
  • Kotun kasar wajen ta ayyana jam’iyyun APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci, abin da PDP ta ce rashin hujja ne
  • Jam'iyyar PDP ta ce babu shaidar da ke nuna mutanenta ko APC kungiyoyin ta’addanci ne, ta nemi Kanada ta yi hankali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta yi Allah-wadai da hukuncin wata kotu a kasar Kanada game da ita da kuma APC.

Jam'iyyar PDP ta nuna damuwa bayan kotun ta ayyana jam'iyyar da APC a matsayin kungiyoyin ta’addanci.

PDP ta soki hukuncin kotun Kanada kanta da APC
PDP ta caccaki hukuncin kotun kasar Kanada. Hoto: People's Democratic Party.
Asali: Twitter

Kotu ta ayyana PDP, APC kungiyoyin ta'addanci

Rahoton Vanguard ya ce wannan mataki ya tayar da hankula musamman a bangaren jam'iyyar PDP mai adawa.

Kara karanta wannan

PDP ta sacewa magoya bayan Jonathan da Obi guiwa da aka kafa kwamitin karba karba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun Tarayyar Kanada ta tabbatar da hukuncin da ya bayyana APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci, ta hana Douglas Egharevba neman mafaka.

Hukuncin, wanda aka yanke ranar 17 ga Yuni 2025, ya nuna dangantaka da kungiyoyin da ake zargi na iya haifar da rashin karɓuwa.

Rahotanni sun ce Ma’aikatar Tsaro ta Kanada ta danganta jam’iyyun da tashin hankali na siyasa, lalata dimokuraɗiyya, da zubar da jini a zaɓe a Najeriya.

Egharevba ya kasance ɗan PDP daga 1999 zuwa 2007 kafin ya koma APC har 2017, lokacin da ya tafi Kanada ya bayyana tarihin siyasarsa.

Hukumomin shige-da-fice na Kanada sun danganta shi da rahotannin leƙen asiri, suna cewa jam’iyyun sun yi amfani da tashin hankali da kashe ’yan adawa.

Kotun ta dogara da halayen jam'iyyar PDP a zaɓen jihohi na 2003 da ƙananan hukumomi na 2004 inda ake zargin ta yi maguɗi da tayar da hankali, Daily Post ta ruwaito.

Kara karanta wannan

EFCC ta yi martani da jam'iyyar ADC ta kira ta 'karen farautar Tinubu'

Alkalin ya tabbatar cewa kasancewa mamba na ƙungiya da ake danganta da ta’addanci ya isa ya sa a hana mutum shiga ƙasar Kanada.

An ayyana PDP da APC a matsayin kungiyoyin ta'addanci
Jiga-jigan PDP sun yi martani da aka ayyana ta da APC a matsayin kungiyoyin ta'addanci. Hoto: Professor Nentawe Yilwatda, People's Democratic Party.
Asali: Facebook

Jiga-jigan PDP sun caccaki kotun Kanada

Jami’in PDP, Timothy Osadolor, ya ce babu wata hujja ko rubutu da ke tabbatar da PDP ko APC a matsayin kungiyoyin ta’addanci.

Mataimakin shugaban matasan ya ce akwai yiwuwar wasu jami’an gwamnati na APC na da alaƙa da ta’addanci, amma hakan bai kamata a ɗaura wa jam’iyya gaba ɗaya ba.

Ya ba da misalin inda aka kama tsohon shugaban Boko Haram a gidan wani babban ɗan gwamnati amma hakan bai shafi jam’iyyar gaba ɗaya ba.

Tsohon jami’in NNPC, Olufemi Soneye, ya bayyana damuwarsa, yana gargadin wannan hukunci na iya kawo matsala ga dimokuraɗiyya fiye da iyakar Kanada.

Ya ce hukuncin ba kawai ya shafi Egharevba ba ne, amma yana zama matsala ga tsarin siyasa da ’yancin dimokuraɗiyya na ƙasashe gaba ɗaya.

Kara karanta wannan

Tinubu: Jam'iyyar PDP ta faɗi dalilin EFCC na kama Tambuwal

Rigima ta sake ballewa a jam'iyyar PDP

Kun ji cewa rikicin shugabanci ya sake kunno a jam'iyyar PDP a jihar Imo bayan da aka shigar da kara a kotu.

Wasu mambobin jam'iyyar sun maka shugaban PDP, hukumar zabe ta INEC kan zaben da aka gudanar a shekarar 2024.

Daga cikin bukatun da suke nema har da cire shugabannin jam'iyyar daga kan mukamansu saboda ba a yi zabe na gaskiya ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.