Gwamna Sule Ya Tsage Gaskiya kan Batun wanda Yake So Ya Gaje Shi a 2027
- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya fito ya yi magana kan jita-jitar da k. Cewa akwai dan takarar da yake goyon baya a zaben 2027
- Abdullahi Sule ya bayyana cewa bai goyon bayan wani dan takara da ke cikin masu neman kujerar gwamnan jihar
- Ya bayyana cewa abin da zai kalla kafin ya goya baya ga daya daga cikin 'yan takarar da ke son darewa kan kujerar mulkin jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya yi magana kan batun cewa akwai dan takarar da yake goyon baya don ya gaje shi.
Gwamna Abdullahi Sule ya ce babu wanda ya fifita a cikin ‘yan takarar kujerar gwamna na zaɓen 2027 a jihar.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce Gwamna Sule ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a Lafia, yayin da yake karɓar bakuncin mambobin kungiyar tsofaffin shugabannin kananan hukumomi tare da mambobin kungiyar tsofaffin kansiloli a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce zai mara baya ne kawai ga ɗan takarar da ke da kwarewar ci gaba da ayyukan ci gaban da yake yi a jihar bayan shekarar 2027.
Gwamna Abdullahi Sule ya ce gwamnatinsa ta yi aiki sosai wajen tabbatar da ci gaban jihar.
Gwamna Sule ya ce bai goyon bayan kowa
Gwamnan ya yi watsi da jita-jitar cewa yana goyon bayan wani daga cikin masu shirin takarar gwamna 28 da ke neman maye gurbinsa a 2027.
Ya musanta zargin cewa yana da wani ɗan takara da yake so, yana mai kiran irin waɗannan zarge-zarge a matsayin jita-jita kawai.
"Shiyasa idan wani ya gaya muku cewa ina goyon bayan wannan ko wancan, magana ce kawai ta banza."
"Mutane ne kawai suke ba da labarin su. A wani lokaci suna cewa ina goyon bayan Akanta Janar. Daga baya kuma suka ce Wadada nake goyon baya."
"Sai kuma wani lokaci su ce Faisal ne. Idan kuka ga mutane suna kai-komo irin haka, ku san babu gaskiya a cikin wannan magana. Ƙarya ce kawai."

Kara karanta wannan
Abba Gida Gida ya yi wa matasa albishir, ya faɗi tanadin da gwamnatinsa ta yi masu
- Gwamna Abdullahi Sule
Wane dan takara Gwamna Sule zai goyawa baya
Gwamnan ya ce zai goyi bayan ɗan takarar da yake da ƙwarewar ci gaba da gudanar ayyukan raya jihar da gwamnatinsa ta aiwatar.

Asali: Facebook
A cewarsa, jihar na da manyan damarmakin samun ci gaba, don haka zai mara baya ne ga wanda yake da ƙwarewar amfani da waɗannan damarmakin yadda ya kamata.
Gwamna Sule ya fadakar da Peter Obi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya tunatar da tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi, kan sharrin mulki.
Gwamna Abdullahi Sule ya ja kunnen Peter Obi kan alkawarin da ya yi na yin wa'adi daya kacal idan ya samu damar zama shugaban kasan Najeriya.
Ya bayyana cewa mulki na tare da kalubale da dama wanda zaj sanya cika alkawarin yin wa'adi daya kacal ya zama mai wahalar cikawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng