PDP Ta Sacewa Magoya bayan Jonathan da Obi Guiwa da Aka Kafa Kwamitin Karba Karba

PDP Ta Sacewa Magoya bayan Jonathan da Obi Guiwa da Aka Kafa Kwamitin Karba Karba

  • Jam’iyyar PDP ta kafa kwamiti kan kujerun takara a zaɓen 2027, tana musanta tattaunawa da wasu manyan yan siyasa
  • Jam'iyyar ta musanta magana da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da Peter Obi kan dawowa jam’iyyar da ke adawa a Najeriya
  • Wasu shugabannin PDP sun ce jam’iyyar na da ‘yan takara masu cancanta kamar Seyi Makinde da Bala Mohammed

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta shirya kaddamar da kwamitin rabon kujeru na zaben 2027 yau a Abuja.

Wannan mataki na zuwa ne duk da sabani tsakanin manyan shugabanni yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

PDP ta musanta tattaunawa da Jonathan da Obi
Jam'iyyar PDP ta kafa kwamitin raba kujerun takara a zaɓen 2027. Hoto: Peter Obi, Goodluck Jonathan.
Asali: Getty Images

PDP ta musanta tattaunawa da Jonathan, Obi

Wasu cikin kwamitin NEC sun ce Jonathan ya bar jam’iyyar a lokacin da ake bukatarsa, yayin da Obi ya bar PDP a zaben 2019, abin da ya cutar da ita cewar Punch.

Kara karanta wannan

"PDP ba ta rabu ba," Sanata Abba Moro na neman rikita lissafin gwamnoni 2 a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu kuma sun yi maraba da dawowar su, amma sun jaddada cewa PDP na da ‘yan takara masu kwarewa kamar Seyi Makinde da Bala Mohammed.

Majiyoyi daga shugabancin PDP sun tabbatar cewa babu tuntuba kai tsaye da Goodluck Jonathan ko Obi, sai dai tattaunawa ta kashin kai daga wasu mutane.

Kakakin PDP, Debo Ologunagba, ya ce za a kaddamar da kwamitin rabon kujeru yau, jam’iyyar kuma na da wadatattun ‘yan takara na shugaban kasa.

PDP ta yi magana kan dawowar Jonathan da Obi cikinta
PDP ta musanta maganar tattaunawa da Jonathan, Obi. Hoto: People's Democratic Party.
Asali: Twitter

PDP ta yanke shawarar taron NWC

PDP ta fito daga rikicin cikin gida da ya dauki watanni, wanda ya jawo ficewar manyan ‘yan siyasa zuwa APC da ADC, TheCable ta ruwaito.

A kokarin farfadowa, PDP ta yanke shawarar yin babban taron zabe a Ibadan ranar 15 zuwa 16 ga Nuwamba don zaben sababbin mambobi 19 na NWC.

Kwanan nan, Bala Mohammed ya gana da Jonathan da Obi kan yiwuwar komawarsu PDP, inda wasu shugabanni suka nemi su dawo.

Kara karanta wannan

Tsugunne ba ta kare ba: Sabuwar rigima ta kunno kai a jam'iyyar PDP

Wasu ‘yan Najeriya na tantama kan cancantar Jonathan saboda gyaran kundin tsarin mulki na 2018 da ke takaita wa’adin wadanda suka rike ofis sau biyu.

Matsayar Obi a baya kan komawa ADC

A baya, Peter Obi ya ce yana nan a jam’iyyar LP tare da kawancen ADC, yayin da Jonathan bai tabbatar ko musanta dawowarsa PDP ba.

Wani jigo a PDP ya ce za a karbi Goodluck Jonathan da Obi idan suna so saboda barin jam’iyyar a lokacin da ake bukata da suka yi.

Ya kara da cewa dole su bi ka’idojin jam’iyya, su yi fafatawa cikin gaskiya ba tare da neman mulki ta hanyoyin kashin kai ba.

An fadi dalilin dacewar Jonathan a 2027

Kun ji cewa wani jigon PDP ya bayyana amfanin da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan zai yi wa Najeriya idan ya koma mulki.

Umar Sani, ya ce tsohon shugaban kasa, Jonathan na da dabarar farfado da tattalin arzikin Najeriya idan ya samu nasara.

Sani ya bayyana cewa Jonathan ba zai yi fiye da wa’adi daya ba, saboda doka ta hana hakan, kuma hakan zai amfanar da Arewa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.