'Abin da Ya Sa Ya Kamata Goodluck Jonathan Ya Marawa Peter Obi Baya a 2027'

'Abin da Ya Sa Ya Kamata Goodluck Jonathan Ya Marawa Peter Obi Baya a 2027'

  • Ana ci gaba da maganganu kan zaben shugaban kasa na shekarar 2027, duk da cewa akwai sauran lokaci kafin zuwansa
  • Shugaban tafiyar Obidients na kasa, ya yi kira ga Goodluck Jonathan ya marawa Peter Obi don zama shugaban kasa Najeriya
  • Yunusa Tanko ya bayyana cewa Peter Obi shi ne wanda ya fi shahara daga cikin 'yan takarar da ke neman kujerar shugaban kasa a zaben 2027

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban tafiyar Obidients na kasa, Yunusa Tanko, ya mika kokon bararsa ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kan Peter Obi.

Yunusa Tanko ya roki Goodluck Jonathan da ya mara wa burin Peter Obi na zama shugaban kasan Najeriya baya.

An bukaci Jonathan ya marawa Peter Obi baya
Yunusa Tanko ya bukaci Jonathan ya goyi bayan Peter Obi Hoto: @PeterObi, @GEJonathan
Asali: Twitter

Jagoran na Obidients ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin 'Daily Politics' na tashar Trust Tv.

Kara karanta wannan

"Bai damu ba": Peter Obi ya ragargaji Tinubu yayin da ya shirya tafiya kasashen waje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me aka bukaci Jonathan ya yi wa Peter Obi?

Yunusa Tanko ya ce ya kamata Jonathan ya gane cewa Peter Obi shi ne ɗan takara mafi shahara cikin masu neman kujerar shugaban kasa.

Hakazalika ya ce ya kamata ya rama biki saboda goyon bayan da Peter Obi ya nuna masa a lokacin da ake kokarin cire shi daga kan mulkin shugaban kasa.

Ya bayyana cewa bai kamata ya bari wasu su yi amfani da shi ba, domin sauya abin da jama'a suke so ba kafin zaben 2027.

"Ko tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya ce Peter Obi shi ne gwamnan da ya mara wa Shugaba Goodluck Jonathan baya lokacin da ake ƙoƙarin cire shi. Peter Obi ne kadai ya tsaya masa."
“Yanzu ne lokacin da Shugaba Jonathan zai rama wannan kyakkyawan aiki ta hanyar kira ga kowa da kowa da ya mara wa Peter Obi baya."

- Yunusa Tanko

Kara karanta wannan

"Ina da tabbaci," Bwala ya hango yadda za ta kaya tsakanin Jonathan da Tinubu a 2027

Jagoran Obidients ya ba Jonathan shawara

Yunusa Tanko ya gargadin cewa wasu 'yan tsiraru da suka jefa kasar nan cikin talauci, suna kokarin amfani da Jonathan domin cimma manufar siyasarsu.

Ya kara da cewa irin wannan yunkuri na iya sanyawa a tauye muradun ‘yan Najeriya.

Peter Obi na shirin yin takara a 2027
Peter Obi zai sake jaraba sa'arsa a 2027 Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Ya jaddada cewa Obi shi ne ɗan takara mafi shahara a 2027, kuma akalla jam'iyyun siyasa takwas ne suke zawarcinsa.

"Ba saboda shi ne mafi kyau a fuska ko mafi wayo ba, amma saboda yana wakiltar muradun matasan Najeriya, yana tsaya musu, kuma yana magana da harshensu."

- Yunusa Tanko

Kalaman Yunusa Tanko dai na zuwa ne yayin da ake rade-radin cewa Goodluck Jonathan zai fito takara a zaben 2027.

Peter Obi ya soki Shugaba Bola Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi, ya yi kalamai masu kaushi kan mai girma Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

'Za mu more': An faɗi dalilai da ke nuna Jonathan ne mafi dacewa da bukatun Arewa

Peter Obi ya soki shugaban kasan ne kan tafiya zuwa kasashen waje inda zai kwashe kwanaki kafin ga dawo gida Najeriya.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana cewa abin da ya fi dacewa inda Shugaba Tinubu shi ne ya ziyarci jihohin kasar nan don ganin halin da jama'a ke ciki, maimakon zuwa wasu kasashen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng