"PDP ba Ta Rabu ba," Sanata Abba Moro na Neman Rikita Lissafin Gwamnoni 2 a Najeriya

"PDP ba Ta Rabu ba," Sanata Abba Moro na Neman Rikita Lissafin Gwamnoni 2 a Najeriya

  • Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Abba Moro ya ce babu rabuwar kai na shugabanci a jam'iyyar PDP
  • Abba Moro mai wakiltar Kudancin jihar Benuwai ya ce rikicin da PDP ke fama da shi banbancin ra'ayi ne da sabani tsakanin yayanta
  • Ya ce a baya jam'iyyar PDP ta taba rabuwa gida biyu amma a yanzu babu wannan sabanin da zai sa mutum ya sauya sheka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Sanata mai wakiltar Benue ta Kudu, Abba Moro, ya ce jam'iyyar PDP a dunkule take karkashin shugabanci guda, ba ta rabe gida biyu ko sama da haka ba.

Sanata Abba Moro ya ce duk da akwai rikicin cikin gida a jam'iyyar PDP amma dai ba ta rabe ba kamar yadda ake gani a wasu jam'iyyun adawa.

Kara karanta wannan

PDP ta sacewa magoya bayan Jonathan da Obi guiwa da aka kafa kwamitin karba karba

Sanata Abba Moro daga jihar Benuwai.
Abba Moro ya ce PDP a dunku'e tale, babu inda ta rabu gida biyu Hoto: Abba Moro
Asali: Twitter

The Cable ta rahoto cewa babbar jam’iyyar adawa a halin yanzu na fama da rikice-rikicen cikin gida da suka haifar da damuwa kan hadin kanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan matsalar ta samo asali ne daga gwagwarmayar neman iko da bambancin ra’ayi tsakanin bangarori daban-daban a cikin jam’iyyar.

Abba Moro ya musanta rabuwar PDP gida 2

Da yake magana a shirin Prime Time na tashar Arise TV a ranar Laraba, Abba Moro, ya bayyana cewa ana samun rabuwar kai ne idan akwai shugabanci biyu daban-daban, abin da ya ce ba ya faruwa a PDP.

“Babu rabuwar kai a jam'iyyarmu ta PDP. Matsalar PDP ba ta kai matsayin ta dare zuwa kashi-kashi ba.
"Abin da zai sa gwamna ko mamba ya bar jam’iyya zuwa wata, bisa tanadin kundin tsarin mulki, shi ne idan shugabancin jam’iyyar ya kasu gida biyu, watau idan aka samu shugabanci biyu daban-daban.

- Inji Sanata Abba Moro.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya yi wa matasa albishir, ya faɗi tanadin da gwamnatinsa ta yi masu

Idan ku na biye, gwamnonin jihohin Delta da Akwa Ibom sun bar PDP zuwa APC tare da magoya bayansu bisa dalilin rikicin cikin gida da ke faruwa.

Wane irin rikici ake fama da shi a PDP?

Sanata Abba, wanda shi ne shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa ya ce a shekarun baya PDP ta fuskanci matsalar rabuwa gida biyu, amma yanzu babu irin haka.

“A da akwai sabuwar PDP da kuma PDP ta asali, wannan ita ce rabuwar kawuna, domin sabuwar PDP ta na da dukkan kayan aiki da ta tambarin PDP, yayin da daya bangaren ke da na shi shugabancin jam'iyya.
"Amma saboda muna fama da rikici ko rashin jituwa tsakanin ‘ya’yan jam’iyya, wannan ba zai zama rabuwar kai ba. Shi ya sa na dinga jaddada cewa PDP ba ta rabu ba," in ji shi.

Ya jaddada cewa matsalolin da PDP ke fuskanta a yanzu “kawai sabani ne na ra’ayi da tsari” wanda bai kai matsayin rarrabuwar kawuna na dindindin ba.

Kara karanta wannan

Ana batun rashin lafiyar Tinubu, Gwamna Radda zai tafi jinya domin duba lafiyarsa

Jam'iyyar PDP na fama da rikici.
Abba Moro ya ce PDP na fama da rikici amma ba ta rabu gida 2 ba Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Facebook

PDP ta fara yunkurin hukunta Wike

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta bayyana shirinta na ladabtar da ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike.

Shugaban kwamitin rikon kwarya na yankin Kudu maso Kudu na jam’iyyar PDP, Emmanuel Ogidi, ne ya bayyana hakan, ya ce abubuwan da Wike ke yi sun fara wuce gona da iri.

Ya ce kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) zai duba ayyukan Wike kuma zai dauki mataki kansa a makon gobe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262