"Arewa ba Ƙorafi," Hadimin Shugaban Ƙasa Ya ce ana Jin Daɗin Mulkin Tinubu
- Hadimin Shugaban Ƙasa a kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala ya ce yankin Arewacin Najeriya na jin daɗin salon mulkin Bola Tinubu
- Wannan na zuwa ne a matsayin martani ga tsohon jigo a gwamnatin Muhammadu Buhari, wato Babachir Lawal kan halin da ake ciki
- Bwala ya yi ikirarin cewa shugaba Tinubu na magance matsalolin ba tare da ya ɓata lokaci ba, kuma jama'ar yankin shaida ne a kan ayyukan
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Hadimin Shugaban Ƙasa na musamman kan sadarwar, Daniel Bwala, ya ce yankin Arewa na gamsuwa ƙwarai da salon mulkin Bola Ahmed Tinubu.
Ya kuma ƙaryata ikirarin tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, da ya ce Arewa na shirin adawa da Tinubu a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
"Alalh ya taimake ni": Babachir Lawal ya fadi abin da zai hana shi aiki a gwamnatin Tinubu

Source: Twitter
Jaridar Punch ta ruwaito Babachir Lawal ya zargi Tinubu da watsi da Arewa, yana cewa yankin bai samun manyan ayyukan gwamnatin tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalaman da su ka jawo martanin hadimin Tinubu
Tashar Channels Television ta wallafa cewa Babachir Lawal ya ce fitattun ‘yan siyasar Arewa sun shirya tattauna matsalolin yankin da tsara dabarun siyasa kafin 2027.
Kalaman sun yi wa Bwala ɗaci, wanda ke ganin babu ƙorafin da ake da shi a Arewa da har zai sa a yi adawa da Tinubu.
Ya ce:
“Arewa na jin daɗin salon mulkin Shugaban Ƙasa ƙwarai, ko ka san dalili? Yana magance matsalolin yankin. Ana ganin ƙoƙarin gwamnati ta hanyoyi daban-daban.”

Source: Twitter
Da aka tambaye shi ko fadar shugaban ƙasa na sauraron koke-koken jama’a kan wahalar rayuwa, Bwala ya ce:
“Lamura a yankin sun riga sun fara inganta.”
Koken jama'a: Abin da hadimin Tinubu ya ce
Bwala ya ƙara da cewa akwai bambanci tsakanin koke-koken jama’a da kuma shirye-shiryen da ‘yan adawa ke ƙirƙira don su ɓata gwamnati.
A cewarsa, jam’iyyun adawa na cikin damuwa saboda yawan nasarorin da Bwala ya ce gwamnatin Tinubu ta samu tun bayan kama mulki a 2023.
Ya bayyana cewa ƙoƙarin da gwamnatin Tinubu ke yi na haifar da ɗa mai ido kuma jama'a su na sane da aikin da ya ke tuttuɗowa Arewacin kasar nan.
Bwala ya bukaci jama'a su yi fatali da dukkanin abin da ƴan adawa za su fada da ke nuna gazawar gwamnatin Bola Tinubu, musamman wajen inganta Arewacin Najeriya.
Bola Tinubu zai bar Najeriya
A baya, kun samu labarin cewa ana tsaka da ake ta rade-radin cewa Shugaba Bola Tinubu ba shi da lafiya, fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa zai bar Najeriya.
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Tinubu zai bar Najeriya zuwa kasashen Japan da Brazil, inda zai tsaya a Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa, kafin ci gaba da tafiya.
Tinubu zai isa Japan domin halartar Taron Tokyo karo na tara kan cigaban Afirka (TICAD9) wanda zai gudana a birnin Yokohama daga 20 zuwa 22 ga watan Agusta, 2025.
Asali: Legit.ng
