2027: Gwamna Bago Ya Nada Kansa Mukami a Shirin Tazarcen Shugaba Tinubu

2027: Gwamna Bago Ya Nada Kansa Mukami a Shirin Tazarcen Shugaba Tinubu

  • Gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago ya ba kan shi mukami domin tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Mai girma Umaru Bago ya ba kansa mukamin shugaban kamfen din Tinubu don zaben shugaban kasa na shekarar 2027
  • Hakazalika, ya soki 'ya'yan jam'iyyar APC wadanda suke kananan maganganu kan gwamnatin Shugaba Tinubu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Neja - Gwamnan jihar Neja, Umar Bago, ya nada kansa mukami domin tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Gwamna Bago ya ayyana kansa a matsayin shugaban kamfen din tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓe mai zuwa.

Gwamna Bago na son tazarcen Tinubu a 2027
Gwamna Bago ya nada kansa mukami saboda Tinubu Hoto: @DOlusegun, @HonBago
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a taron shugabannin jam’iyyar APC na jihar a ranar Litinin a Minna, babban birnin jihar Neja.

Gwamna ya ba kansa mukami a tafiyar Tinubu

Kara karanta wannan

Magana ta kare, bidiyon Shugaba Tinubu ya bayyana ana tsaka da jita jitar ba shi da lafiya

Gwamna Bago ya bayyana jihar a matsayin cibiyar kamfen din shugaban ƙasa domin zaɓen 2027.

“Ni ne yanzu shugaban kamfen din Asiwaju Tinubu na 2027, wanda na naɗa kaina. Jihar Niger ita ce cibiyar kamfen din Asiwaju 2027."

- Gwamna Umaru Bago

Gwamna Bago ya soki ’yan siyasa da ke adawa da batun Kudancin kasar nan ya ci gaba da rike mulki a 2027, yana roƙonsu da su mutunta tsarin raba mulki tsakanin Arewa da Kudu.

“Mu ’yan Najeriya ne, muna kaunar Najeriya. Akwai fahimtar juna da ba a rubuta ba a wannan kasa cewa mulki ya rika zagagawa daga Arewa zuwa Kudu, sannan daga Kudu zuwa Arewa. Wannan ya kawo zaman lafiya mai ɗorewa a kasar nan."
"Shekaru kusan biyu kenan da suka gabata muka kammala mulkin shekaru takwas na marigayi shugaban kasa Muhammadu Buhari (Allah ya gafarta masa), kuma Asiwaju yana cikin shekararsa ta biyu a yanzu."

- Gwamna Umaru Bago

Gwamna Bago ya soki 'yan APC

Gwamna Bago ya kuma soki ’yan jam’iyya “marasa godiya” da suka koma wasu jam’iyyu ko suka janye goyon bayansu ga APC, yana kiran su marasa biyayya, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Da gaske ba shi da lafiya? Gwamna ya fadi halin da ya tarar da Shugaba Tinubu a Aso Rock

Ya ce bai kamata a dora wa shugaban ƙasa laifin halin da kasar nan ke ciki ba, domin matsalolin gadarsu aka yi, kuma ana ɗaukar matakai don magance su.

Gwamna Bago ya tabo batun tazarcen Tinubu
Gwamna Bago na son tazarcen mai girma Bola Tinubu a 2027 Hoto: @chiefpressngs
Source: Twitter
“Meyasa mutanen wannan yankin suke haifar da rikici? Musamman waɗanda suka fito daga APC? Kun ci moriyar APC. APC ita ce ta ba ku damar da kuka samu."
"Wasu daga cikinku sun yi gwamnoni, ministoci, masu ba da shawara, da kwamishinoni, kuma kun yi shekaru takwas a kan kujeru. Yanzu kuna hutun siyasa, amma kun haɗu don kawo tangarda ga gwamnati."
"Kun yi magana kan tituna marasa kyau, Asiwaju ba shi ya lalata titunanku ba, ya gada ne, kuma yana gyarawa."
"Asiwaju bai lalata makarantunku ba, ya gada ne, kuma yana gyarawa. Haka ma asibitoci. Kuma kuna son amfani da wannan don adawa da mu? Wannan rashin kunya ne."
"Abin da muke tsammani daga gare ku shi ne godiya da biyayya, domin mulki ya wuce daga APC zuwa APC, ba abin da kuke yi yanzu ba."
"Mun san masu haddasa matsalolin tattalin arzikin kasa. Na san abin da na gada, amma ban taba yin magana ko binciken kowa ko neman maida kuɗi ba. Don Allah, a bar maganar da ta wuce ta wuce."

Kara karanta wannan

Zai koma APC ne? An ga gwamnan adawa ya sanya hula mai tambarin Tinubu a Aso Rock

"Asiwaju ko Bago ba su jawo wannan matsalar tsaro ba, amma yanzu mutanen yankinku suna iya yin barci lafiya saboda muna aiki."

- Gwamna Umaru Bago

Ministan Tinubu ya ja kunnen Gwamna Bago

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar, Umaru Mohammed Bago, ga samu sakon gargadi daga wajen ministan yada labarai, Mohammed Idris.

Mohammed Idris ya gargadi gwamnan kan shiga hurumin da ba na shi ba, bayan ya umarci a rufe wani gidan rediyo.

Ministan ya bayyana cewa Gwamna Bago bai da hurumin ba da umarnin a rufe wani gidan rediyo, domin alhakin hakan bai rataya a wuyansa ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng