Abin da Muka Sani game da Jita Jitar Matsala tsakanin Ganduje da Barau Jibrin
- Ana ta hasashen cewa akwai rarrabuwar kai cikin APC a jihar Kano, inda magoya baya suka kasu tsakanin jiga-jigan jam'iyyar
- Ana zargin barakar ta samu ne tsakanin ɓangarorin Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Barau Ibrahim Jibrin da wasu mutanensu
- Wasu masanan siyasa sun ce buƙatu tsakanin manyan jam’iyya na iya haddasa rarrabuwar kai idan ba a sami daidaito ba kafin zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa akwai alamar rigima a jam'iyyar APC da ke jihar Kano a Arewa maso Yamma a Najeriya.
Alamun rarrabuwar kai sun bayyana a jam’iyyar, inda aka shata layi tsakanin magoya bayan tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje da Sanata Barau Jibrin.

Source: Twitter
Majiyar BBC Hausa ta ce ɓangaren Ganduje na da magoya bayansa, haka kuma ɓangaren mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganduje/Barau: Abin da ake zargin ya jawo baraka
An fara hango wannan ɓaraka lokacin wani taro a Kano da ba a ga Barau da ƙaramin ministan gidaje, Yusuf Abdullahi Ata a wurin ba.
Rahotanni sun nuna cewa APC Kano ta kafa kwamitoci uku don shawo kan ‘ya’yan da suka ji an yi musu rashin adalci, a daidaita matsalolin cikin gida.
Yusuf Abdullahi Ata ya ce rashin halartar taron ya biyo bayan ayyukan ofis a Abuja, ba saboda wani rabe-rabe a jam’iyyar ba.
Ya bayyana cewa kwanaki kafin taron ya sanar da shugaban jam’iyyar jihar Kano cewa ba zai samu damar halarta ba saboda ayyukan gwamnati.

Source: Twitter
Kano: Martanin APC kan rahoton rigima a cikinta
Shugaban APC Kano, Abdullahi Abbas, ya ce ba matsala a jam’iyyar, sai dai bambancin ra’ayi da ake ƙoƙarin shawo kansa kafin babban zaɓe.
Ya ce a siyasa rashin samun abin da ake buƙata kan haifar da ƙorafi, amma suna ƙoƙarin haɗa kai saboda manufarsu ɗaya ce.
Masanin siyasa, Yusuf Musa ya ce siyasa kasuwar buƙata ce, kuma karo tsakanin manya yakan jawo rabuwar kai idan ba a shawo kansa ba.
Ya bayyana cewa muradin Barau na neman gwamnan Kano na iya karo da burin wasu manya, lamarin da zai iya raba jam’iyyar gida biyu.
Masana suna ganin cewa Barau zai nemi takarar gwamnan Kano a APC wanda ba dole ya samu goyon bayan wasu jiga-jigai ba duk da tasirinsa.
Ƙaramin minista daga jihar, Yusuf Abdullahi Ata ya tabbatar da haka a wata hira inda ya ce Barau zai tsaya takarar gwamna a 2027.
A zaben da ya gabata, APC ta tsaida Nasiru Gawuna ne da Murtala Sule Garo wanda ya fito daga yanki guda da mataimakin shugaban majalisar.
Dantata: Ganduje, Barau sun hadu a Madina
Mun ba ku labarin cewa dage jana'izar fitaccen dan kasuwa kuma attajiri, Alhaji Aminu Dantata ya ba wasu fitattu a Najeriya damar halarta.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin da Abdullahi Ganduje sun tashi daga Abuja zuwa Madina domin jana’izar marigayin.
Barau ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da misalin karfe 9:00 na daren ranar Litinin 30 ga watan Yunin 2025.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

