"Da Yanzu Shi ne Shugaban Kasa": Jigo a PDP Ya Fadi Kuskuren Atiku a Zaben 2023

"Da Yanzu Shi ne Shugaban Kasa": Jigo a PDP Ya Fadi Kuskuren Atiku a Zaben 2023

  • Yayin da aka fara maganganu kan zaben shekarar 2023, wani kusa a PDP ya tuna kuskuren da Atiku Abubakar ya yi a lokacin takara
  • Tsohon mataimakin sakataren yada labaran na kasa na PDP, Diran Odeyemi, ya nuna cewa Atiku ya yi kuskure kan rashin yin aiki tare da Peter Obi
  • Hakazalika ya bayyana cewa jam'iyyar ADC tana karkashin akalar tsohon mataimakin shugaban kasan ne tare da mutanensa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin sakataren yada labarai na kasa na jam’iyyar PDP, Diran Odeyemi, ya yi magana kan tasirin Atiku Abubakar a ADC.

Diran Odeyemi ya bayyana cewa Atiku Abubakar da makusantansa ne suke juya jam'iyyar ADC.

Jigo a PDP ya yi maganganu kan Atiku
Diran Odeyemi ya ce Atiku ya yi kuskure a zaben 2023 Hoto: @atiku
Asali: Facebook

Diran Odeyemi ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin Politics HQ na tashar News Central.

Kara karanta wannan

Rikicin cikin gida: PDP ta amince da bukatun Wike, an gano dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi kalamai kan alakar Atiku da ADC

Jigon na PDP ya ce Atiku Abubakar ya tura makusantansa na siyasa zuwa cikin jam’iyyar ADC.

"ADC, idan kuna son sani, na nufin 'Atiku Disciples Congress'."
“Ya tura mutanensa zuwa wurin. Don haka idan wani ɗan takara ko mai sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa ya shiga ADC yau, to hakan zai zama karshen hulɗarsa da jam’iyyar.”

- Diran Odeyemi

Jigon PDP ya fadi rashin lissafin Atiku a 2023

Ya ce Atiku Abubakar zai iya lashe zaben shugaban kasa na 2023 da ya zabi Peter Obi a matsayin mataimakinsa.

“Da Atiku ya kasance mai hikima da ya rike Peter Obi a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban kasa, da yanzu shi ne shugaban kasa a yau."

- Diran Odeyemi

Diran Odeyemi ya ƙara da cewa rashin amincewar Atiku Abubakar da bukatun gwamnonin G5, wanda ya haɗa da cire Iyorchia Ayu daga kujerar shugaban jam’iyyar PDP na kasa babban kuskure ne.

Kara karanta wannan

2027: Komai na iya faruwa da takarar Atiku da ake hasashen Jonathan zai dawo ADC

“Idan da shi mutumin da zai iya yanke hukunci ne ya ce ‘ga abin da na tsaya a kai’, da an cire Ayu a lokacin kamar yadda gwamnonin G5 suka nema."

- Diran Odeyemi

Jigon PDP ɗin ya ce bai da tabbacin cewa masu ba Atiku Abubakar shawara suna yin nazari kan siyasa kafin a dauki muhimman matakai.

“Ba ni da tabbacin cewa mutanen da ke tsara masa dabaru suna kallon halin da ake ciki kafin ya fara ɗaukar wasu matakai."

- Diran Odeyemi

Atiku da Peter Obi sun yi takara a zaben 2023
Diran Odeyemi ya nuna cewa ya yi kuskure kan kin daukar Peter Obi a 2023 Hoto: @atiku, @PeterObi
Asali: Facebook

Jonathan zai sa Atiku ya bar ADC

Game da yiwuwar Goodluck Jonathan ya dawo siyasa, Odeyemi ya ce Atiku zai bar ADC idan tsohon shugaban kasan ya shiga jam’iyyar.

“Abin da nake so na gani yanzu shi ne kawai idan Jonathan zai shigo ADC. Kuma idan Jonathan ya shigo, Atiku zai bar ADC, ku ɗauki wannan a matsayin tabbaci."

- Diran Odeyemi

Atiku ya soki cafke Tambuwal

Kara karanta wannan

2027: Peter Obi ya yi hangen nesa, ya gano hanyar kwace mulki a hannun APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi kalamai masu zafi kan kamun da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), ta yi wa Aminu Waziri Tambuwal.

Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da matakin da hukumar EFCC ta dauka na tsare tsohon gwamnan na jihar Sokoto.

Ya bayyana cewa kamun ba komai ba ne wani yunkuri na hana 'yan adawa sakat saboda ya kasance mamba a cikin hadaka karkashin jam'iyyar ADC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng