"Ba Tinubu ba ne," Sakataren Gwamnatin Tarayya a Mulkin Buhari Ya Fadi Wanda Ya Ci Zaben 2023
- Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya ce a bayanan da ya tattara, ba Bola Ahmed Tinubu ne ya ci zaben shugaban kasar 2023 ba
- Babachir ya yi ikirarin cewa dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi ne ya samu nasara amma aka canza sakamakon zaben
- Ya kuma bayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin mutum mai girman kai, yana mai cewa shi ne ya masa laifi tun farko
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya yi ikirarin cewa Peter Obi ne ya lashe zaben shugaban kasa na 2023.
Babachir Lawal ya bayyana cewa a bayanan da ya samu bayan kammala zaben 2023, APC ce ta sha kasa a hannun dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP.

Source: Facebook
Tsohon sakataren gwamnatin ya yi wannan ikirari ne a wata hira da aka yi da shi a cikin shirin Politics Today na tashar Channels tv ranar Litinin, 11 ga watan Agusta, 2025.

Kara karanta wannan
An kwantar da shugaban Majalisar Dattawa a wani asibiti a Landan? An samu bayanai
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babachir Lawal ya fadi 'wanda ya ci' zaben 2023
Babachir Lawal ya ce, bisa alkaluman da yake da su, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP ne ya ci zaben, amma aka bayyana Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa na 16 a Najeriya.
Lawal, wanda ya kasance mai sukar wannan gwamnati, ya ce Shugaba Tinubu bai ci zaben ba, yana mai cewa, “sakamakon da yake hannuna a lokacin ya nuna ba ahi ya yi nasara a zaben 2023 ba.”
Idan zaku iya tunawa, Babachir Lawal ya rike kujerar sakataren gwamnatin tarayya a gwamnatin tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2017.
Sai dai babu wasu hujjoji da ke tabbatar da ikirarin da 'dan siyasar yake yi. Hukumar INEC da duk wasu kotuna sun ba Bola Tinubu nasara a zaben na 2023.
Abin da ya hada Babachir Lawal da Tinubu
“Matsalar Bola Tinubu ita ce yana tunanin ni ne na yi masa laifi. Ban yi masa laifin komai ba, shi ne ya yi mani laifi, kuma shi mutum ne mai cike da girman kai.
"Yanzu yana ganin shi ne wai mai girma shugaban kasa, ina da yakinin cewa ba shi ne ya ci zaben da aka yi a 2023 ba.
- Babachir Lawal.
Yayin da yake kare ikirarinsa, Lawal ya ce sun bibiyi zaben, sun tattara bayanai kuma sun sa ido kan sakamakon daga wuraren kada kuri’a a fadin Najeriya.

Source: Facebook
Ana zargin Tinubu na da girman kai
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya ya ce tun a rumfunan zabe, aka canza alkaluman kuri'un da al'umma suka kada, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Da aka tambaye shi menene laifin da Tinubu ya yi masa, Lawal ya ce, “Yana da girman kai. Wannan mutumin yana da wani irin girman kai da ba a iya bayyana shi.”
Fasto ya hango faduwar Bola Tinubu a 2027
A wani labarin, kun ji cewa Fasto Bomadi Serimoedumu ya yi hasashen cewa Goodluck Jonathan zai koma fadar shugaban kasa a zaben 2027.
Fitaccen malamin addinin kirista ya ce tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan zai yi nasara idan ya tsaya takara a zaɓen da za a gudanar a 2027.
Faston ya yi ikirarin cewa ya hango tutar PDP ka tashi a fadar shugaban kasa bayan kammala zaben 2027, sannan kuma ya ga Jonathan na daga hannu.
Asali: Legit.ng
