'Na Gano Shi a 'Aso Rock': Malami Ya Faɗi wanda Zai Zama Sabon Shugaban Ƙasa a 2027

'Na Gano Shi a 'Aso Rock': Malami Ya Faɗi wanda Zai Zama Sabon Shugaban Ƙasa a 2027

  • Malamin addinin Kirista a Najeriya ya yi hasashen wanda zai dare kujerar shugaban kasa a kasar a shekarar 2027
  • Fasto Bomadi Serimoedumu ya yi hasashen tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan zai koma 'Aso Rock' a 2027 idan ya tsaya takara kuma zai yi nasara
  • Malamin ya ce a hangensa ya ga Jonathan yana daga tutar PDP sama, zai yi shugabanci shekaru hudu cikin farin ciki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Fitaccen Fasto a Najeriya ya bayyana abin da ya hango kan zaben shekarar 2027 da ke tafe.

Fasto Bomadi Serimoedumu, ya yi hasashen komawar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan zuwa 'Aso Rock' a 2027.

An yi hasashen wanda zai lashe zaben 2027
Fasto ya faɗi wanda zai zama sabon shugaban ƙasa a 2027. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Goodluck Jonathan.
Asali: Facebook

Fasto ya yi hasashen zaben 2027

Faston ya bayyana hasashen yayin hudubar Lahadi a 'Paradise City Zion', cibiyar cocin a Bomadi a jihar Delta da ke Kudu maso Kudi, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Rikici ya kaure tsakanin Dogo Gide da hatsabibin dan bindiga, an kashe wasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da yake hasashen, malamin ya ce Goodluck Jonathan zai yi nasara idan ya tsaya takara a zaɓen da za a gudanar a 2027.

Ya ce, a hangensa, ya ga tutar jam’iyyar PDP tana tashi sama da sauran, Jonathan na daga ta da hannu, alamar nasara.

Ya kara da cewa Jonathan zai yi mulki na shekaru hudu kuma zai kawo ci gaban tattalin arziki da farin ciki ga jama’a.

Ya ce:

“Ina ganin shugaban kasa Goodluck Jonathan a Aso Rock yana jagorantar kasar nan. Idan ya tsaya a 2027, zai dawo shugaba, za a samu arziki, mutane kuma za su yi murna."
Gargadin da Fasto ya yi ga Tinubu
Fasto ya fadi irin sakwannin da ya turawa Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Gargadin da Fasto ya yi ga Tinubu

Malamin ya ce a watannin baya ya yi sakonni ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana gargadi kan tashin hankali da karuwar rashin tsaro.

Ya bayyana wani hangensa lokacin zaben 2023, inda ya ce Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima sun ziyarce shi a mafarki don neman goyon bayan annabci.

Kara karanta wannan

2027: Komai na iya faruwa da takarar Atiku da ake hasashen Jonathan zai dawo ADC

“A hangen, Tinubu yana zaune a kujera, Shettima kuma a kasa a gefensa, Tinubu ya yi alkawarin wa’adin mulki daya ne kawai kuma ya nemi goyon bayana.
"Na amince, amma na lura mataimakinsa bai yi farin ciki da ra’ayin wa’adi daya ba."

- Cewar Serimoedumu

Ya bayyana wadannan hangen a matsayin “abubuwan boyayyu masu ban mamaki,” yana kara jaddada rawarsa a matsayin “Mai Bayyana Sirrin Yankin Niger Delta.”

Wannan hasashen mai tayar da kura na kara cusa jita-jita kan zaben 2027, musamman kan ko Jonathan, wanda ya jagoranci Najeriya daga 2010 zuwa 2015, zai dawo siyasa.

Malami ya hango nasarar Atiku a 2027

A baya kuma, kun ji cewa wani malamin gargajiya da ya yi hasashen nasarar APC a 2023, yanzu ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai sha kasa zaɓen 2027.

A wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta, an ga malamin yana kulumboto, tare da cewa Atiku Abubakar ne zai lashe zaben shekarar 2027 mai zuwa.

Hasashen malamin dubar ya jawo cece-kuce, yayin da 'yan Najeriya suka zura ido suka ko hasashensa zai zama gaskiyar kamar na baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel