'Tinubu Ya Cancanci Samun Goyon Bayan Manyan 'Yan Siyasar Arewa', Jigon APC Ya Kawo Dalili
- Jigon jam'iyyar APC a jihar Osun, Olatunbosun Oyintilohe ya mika kokon bararsa ga manyan 'yan siyasar Arewa kan shugaban kasa Bola Tinubu
- Oyintilohe ya bukaci manyan 'yan siyasar da su marawa Tinubu baya domin samun tazarce a zaben shekarar 2027 da ake tunkara
- Jigon na APC ya bayyana cewa shugaban kasan ya yi kokarin da ya kamata ya sanya ya samu goyon baya daga gare su
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Osun - Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya nemi manyan 'yan siyasar Arewa su goyawa Shugaba Bola Tinubu baya.
Olatunbosun Oyintiloye ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya yi isasshen aiki da zai sa manyan ‘yan siyasar Arewa su ba shi goyon baya kafin zaben shekarar 2027.

Asali: Twitter
Jaridar The Cable ta rahoto cewa jigon na APC ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da ‘yan jarida a Osogbo, babban birnin jihar Osun a ranar Lahadi, 10 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon APC ya roki 'yan Arewa kan Tinubu
Oyintiloye ya bayyana Tinubu a matsayin abokin Arewa wanda kullum yake mara wa yankin baya wajen cimma burin siyasarsa.
Ya ce irin wannan amana da sadaukarwa ya dace a mayar da biki ta hanyar cikakken goyon baya ga neman wa’adin mulki na biyu na shugaban kasan.
Sai dai, tsohon dan majalisar ya zargi wasu ‘yan kadan daga cikin manyan ‘yan Arewa da shirya makirci domin kawo cikas ga shugabancin Tinubu.
Ya ce wannan rukuni na ‘yan tsiraru kan bayyana ne duk lokacin da wani daga Kudu yake kan mulki, inda suke amfani da barazana da matsin lambar siyasa domin raunana karfin fadar shugaban kasa.
"Ana maimaita wannan lamari akai-akai, kuma tarihin siyasar kasar nan ba zai manta da irin tsangwamar da shugabannin kasa daga Kudu suka sha a hannun wasu ‘yan Arewa kalilan wadanda kullum ke kaurin suna wajen nuna adawa da neman wa’adin mulki na biyu na irin wadannan shugabanni ba."
"Amma a game da Shugaba Bola Tinubu, ya yi isasshen kokari da zai tabbatar masa da goyon bayan manyan masu tasiri na Arewa."
"Saboda haka, lokaci ya yi da yankin zai kara mayar da wadannan ‘yan tsiraru zuwa inda suka dace, tare da kawar da makircin da suke kitsa wa shugaban kasa.”
Wadannan mutane sun nada kansu a matsayin shugabannin Arewa, don haka bai dace manyan shugabannin siyasa da sarakunan gargajiya na Arewa su ci gaba da kallo suna barin shirin batanci da ake yi wa Tinubu ya samu karbuwa ba.”
- Olatunbosun Oyintiloye

Asali: Facebook
Amaechi: Gwamnatin Buhari ta fi ta Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya auna gwamnatocin Muhammadu Buhari da ta Shugaba Bola Tinubu a sikeli.
Rotimi Amaechi ya bayyana cewa gwamnatin marigayi Buhari ta yi wa ta Shugaba Bola Tinubu fintinkau.
Tsohon ministan ya koka kan yadda rayhwa ta yi tsada karkashin mulkin Tinubu da yadda talaka bai amfana da cire tallafin man fetur da aka yi.
Asali: Legit.ng