Shekarau Ya Yi Karatun Ta Natsu, Ya Gano Hanyar Kifar da Tinubu a 2027

Shekarau Ya Yi Karatun Ta Natsu, Ya Gano Hanyar Kifar da Tinubu a 2027

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya fayyace kalamansa kan hadakar 'yan adawa
  • Shekarau ya bayyana cewa hadakar daidaikun mutane ba ta jam'iyyu ba, ba za ta iya raba Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mulki ba a 2027
  • Ya kawo misalin yadda suka koyi darasi a baya bayan sun yi yunkurin kafa hadaka don kifar da Goodluck Jonathan a shekarar 2011

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar PDP, Ibrahim Shekarau, ya yi magana kan hadakar kifar da Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Ibrahim Shekarau ya jaddada cewa hadakar kawai da za ta iya kayar da Shugaba Tinubu a shekarar 2027, ita ce wadda jam’iyyu suka hadu kai tsaye, ba daidaikun mutane ba.

Shekarau ya yi magana kan hadaka
Shekarau ya ce hadakar jam'iyyu za ta iya kifar da Tinubu Hoto: Ibrahim Shekarau, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Twitter

Shekarau ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

2027: Peter Obi ya yi hangen nesa, ya gano hanyar kwace mulki a hannun APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shekarau ya fadi hanyar kifar da Tinubu

Ya bukaci dukkan jam’iyyun adawa da su binciki hanyoyi da dabarun farfaɗo da dandalin siyasa da ake da shi domin cimma irin wannan buri.

Shekarau ya kawo misalin yadda shi da wasu ‘yan kishin ƙasa suka yi ƙoƙarin kafa haɗaka a shekarar 2011 domin kifar da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan daga mulki.

Tsohon gwamnan ya yi nuni da maganganunsa na baya kan yunƙurin wasu manyan ‘yan siyasa na haɗuwa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC domin kwace mulki daga hannun APC mai mulki a shekarar 2027.

A cewarsa, bai ce ba zai yiwu a tumɓuke APC a 2027 ba, sai dai don irin wannan yunƙuri ya yi nasara, dole masu jagorantar shi su kasance jam’iyyu da aka kafa kuma suke da tsari, ba mutanen da ke neman mulki ba.

Yayin da yake fayyace matsayinsa kan wannan batu, Shekarau ya ce:

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya samo mafita ga PDP kan mutanen da suka yi mata zagon kasa a 2023

“Wasu ba su fahimci saƙona daidai ba. Don bayyana gaskiya, ban ce haɗaka ba za ta iya kayar da Tinubu a 2027 ba. Abin da na ce shi ne haɗakar ‘mutane’ ba tare da jam’iyyu ba, ba zai yiwu ba."

Shekarau ya tuna baya kan hadaka

Ya kawo misalan ƙoƙarin da wasu jam’iyyu da yanzu sun shuɗe irin su ACN, CPC da ANPP suka yi a 2011 domin tabbatar da maganarsa.

Ya ƙara da cewa abin da yake nufi shi ne shiga tsakani na jam’iyyu da aka yi rajista, waɗanda suke da gwamnati da ‘yan majalisa da aka zaɓa, tare da samun goyon bayan jama’a a matakin ƙasa lokacin da suka shiga yunƙurin haɗaka.

"Ina daya daga cikin jagororin yunƙurin haɗaka a 2011, kasancewata ɗan takarar shugaban ƙasa na ANPP a lokacin. Mun yi taruka da dama a gidan Shugaba Tinubu a Abuja a shekarar 2011."
"A wani lokaci, (marigayi tsohon Shugaba Muhammadu) Buhari, (Nuhu) Ribadu da ni, a matsayin ‘yan takarar CPC, ACN da ANPP, mun haɗu a gidan Buhari a Abuja don ci gaba da tattaunawa kan haɗaka. Amma bai yi nasara ba. Daga karshe kowannenmu ya shiga zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyarsa.”

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar malaman Kano zai nemi gwamna, zai kara da Abba a 2027

"Wannan darasi ne a garemu da jam’iyyunmu. Daga bisani, a 2012, jam’iyyun CPC, ACN da ANPP suka amince su sake gwada yin haɗaka"

- Ibrahim Shekarau

Shekarau ya ba 'yan hadaka shawara
Shekarau ya yi magana kan kafa hadaka Hoto: Ibrahim Shekarau
Source: Facebook

Ya ce, tsarin da aka yi amfani da shi a 2015 ya kawo nasara ne saboda shugabannin da suka shiga wannan yunkuri sun fi fahimtar muhimmancin yin tattaunawa ta hanyar jam’iyyunsu, ba a matsayin mutane kaɗai ba.

Ya ƙara da cewa tattaunawar haɗaka ba tare da jam’iyyun adawa da aka kafa da suke da ‘yan majalisa da aka zaɓa irin su PDP, LP da SDP ba, to lallai za ta gaza cimma nasara.

Amaechi ya cika baki kan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya cika baki kan takara da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Amaechi ya bayyana cewa zai iya kifar da Shugaba Tinubu idan ya samu tikitin takara a karkashin jam'iyyar ADC.

Ya bayyana cewa ya san raunin shugaban kasan, kuma zai yi amfani da shi don samun nasara a kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng