Wa'adi 1 a Ofis: Gwamnan APC Ya Fadawa Peter Obi Sharrin Mulki da Bai Sani ba
- Gwamna Abdullahi Sule ya gargadi Peter Obi cewa matsin lamba na siyasa na iya hana cika alkawarin wa’adin mulki daya
- Injiniya Sule ya yaba da kokarin Bola Tinubu wajen farfado da tattalin arziki da karawa Najeriya kudaden ajiyar kasa
- Ya bukaci gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi su yi amfani da karin kudaden shiga wajen rage wahalar da jama’a ke fuskanta
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lafia, Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi martani kan kalaman Peter Obi game da wa'adin mulki.
Gwamna Sule ya gargadi dan takarar shugaban kasa na LP a 2023 kan alkawarin yin mulki wa’adi daya kacal inda ya samu dama.

Source: Twitter
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin hira da yan jaridu inda ya ce matsin lamba na siyasa da rikitarwar mulki na iya hana cika irin wannan alkawari, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalaman Peter Obi kan wa'adi 1 a mulki
Hakan ya biyo bayan kalaman Obi cewa wa'adin mulki na shekara hudu kacal ya ishe shi aiwatar da abubuwan alheri a kasa.
Yan siyasa da dama sun soki wannan fahimta ta shi da cewa wa'adin mulki daya ba zai samar da abin da ake so ba a Najeriya.
Peter Obi ya sake jaddada aniyarsa bayan shan suka daga wasu bangarori inda ya ce har yanzu yana kan bakarsa.
Ya kuma bukaci sauya fasalin tsarin mulki wanda zai zama wa'adi daya amma na tsawon shekaru biyar.

Source: Facebook
Gwamna Sule ya kore maganar wa'adin mulki 1
Gwamna Sule ya ce ko shugaban kasa yana da niyyar yin mulki na shekara hudu kawai, ba zai iya warware kashi kadan na matsalolin Najeriya ba.
A cewarsa, idan shugaban ya hau mulki, manyan masu ruwa da tsaki za su matsa masa lamba da barazanar shari’a domin ya ci gaba da mulki.
Kusan dai da wahala a samu wani mai mulki a Najeriya da ya bar ofis bayan shekara saboda ganin damarsa, sai dai fadi zabe, juyin mulki, rashin lafiya ko a tsige shi.
Gwamnan Nasarawa ya yabi Shugaba Tinubu
Yayin da yake magana kan gwamnatin Tinubu, Sule ya yaba da kokarinta wajen farfado da tattalin arziki da kuma inganta harkar tsaro a kasa.
Ya ce gwamnatin ta kara kudaden ajiyar kasa zuwa kusan dala biliyan 40 da kuma karin samar da danyen mai daga miliyan 1.1 zuwa 1.8 a rana.
Sule ya amince akwai kalubale na tsaro musamman a Arewa, amma karin kudaden shiga na bai wa gwamnati damar fuskantar matsalolin, Daily Post ta ruwaito.
Ya bukaci gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi su yi amfani da karin kudaden shiga wajen taimaka wa talakawa da ke cikin wahala.
A karshe, ya jaddada cewa shugaban kasa Tinubu kansa ya amince akwai kalubale, don haka ake bukatar hadin kai wajen magance su.
Obi ya ba Islamiyya kyautar kudi a Bauchi
Kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a 2023, Peter Obi ya ba da kyautar N15m ga kwalejin jinya da makarantar islamiyya a Bauchi domin tallafa wa fannin kiwon lafiya da ilimi.
Yayin da ya ce yana ziyartar akalla makarantun jinya 70 a shekara, Peter Obi ya ce malaman jinya su ne ginshikin al'umma.
Shugabannin makarantun Malikiya da Intisharu sun gode wa Obi, tare da alkawarin amfani da kudin don inganta harkokin karatu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


