2027: Peter Obi Ya Yi Hangen Nesa, Ya Gano Hanyar Kwace Mulki a Hannun APC

2027: Peter Obi Ya Yi Hangen Nesa, Ya Gano Hanyar Kwace Mulki a Hannun APC

  • Peter Obi wanda ya nemi takarar shugaban kasa a zaben 2023, ya bukaci 'yan adawa su hada kai don tunkarar jam'iyyar APC
  • Jigon na jam'iyyar LP ya nuna cewa sai 'yan adawa sun sauya yanayn siyasarsu idan suna son raba APC da madafun ikon kasar nan
  • Kiraye-kirayen da Peter Obi ya yi dai na zuwa ne yayin da 'yan adawa ke ci gaba da kokarin zama a waje daya don tunkarar zaben 2027

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya yi kira ga 'yan adawa kan batun raba APC da mulkin Najeriya.

Peter Obi ya sake nanata kira ga 'yan adawa kan su haɗa kai da sauya yanayim siyasar ƙasa, idan suna son kwace mulki daga hannun jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya gana da Peter Obi, ya miƙa buƙatar da ka iya tarwatsa haɗakar ADC

Peter Obi ya ba 'yan adawa shawara
Peter Obi na son 'yan adawa su hada kai Hoto: @PeterObi
Asali: Facebook

Jaridar Tribune ta ce Peter Obi ya yi wannan magana ne a ranar Juma’a yayin wata ziyarar aiki zuwa ofishin gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Obi ya ba 'yan adawa shawara

Tsohon dan takarar shugaban kasan ya godewa Gwamna Bala Mohammed kan irin tarbar da ya samu.

"Mai girma gwamna, bari na ci gaba da gode maka saboda tarbar da ka yi min da kyakkyawar alakar da ke tsakanin mu."
"Na zo Bauchi ne don ziyartar makarantu biyu na koyon aikin jinya, amma ban tsaya a nan ba, na zo na haɗu da ɗan’uwana domin mu tattauna kan matsalolin jama’a da kuma yadda za mu magance su tare."
"A gare mu ‘yan adawa gaba ɗaya, yana da muhimmanci mu yi aiki tare. Ba batun kanmu kaɗai ba ne batun ƙasarmu ne. Dole siyasar mu ta sauya. Ta zama siyasar ci gaba, ƙwarewa, iya aiki da kuma tausayi."

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar malaman Kano zai nemi gwamna, zai kara da Abba a 2027

- Peter Obi

Ya jaddada cewa yin aiki tare ba wai don amfanin cimma muradun kai ba ne, illa don samu mafita ga Najeriya da ‘yan Najeriya.

"Idan muka yi aiki tare, abubuwa za su yi kyau kuma su ƙara inganta a nan gaba."

- Peter Obi

Peter Obi ya je ziyara jihar Bauchi
Peter Obi ya bukaci 'yan adawa su hada kai Hoto: @PeterObi
Asali: Facebook

An bukaci Peter Obi ya dawo PDP

A martaninsa, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya yi kira a fili ga Peter Obi da ya koma PDP, yana mai cewa dole ne ‘yan adawa su haɗa kai domin ceto Najeriya daga gazawar gwamnatin APC.

Bala Mohammed ya yaba wa Peter Obi bisa abin da ya bayyana a matsayin “sabuwar siyasa” da ta mayar da hankali kan tattaunawa mai amfani, mulkin da ke kula da jama’a, da kuma sa ido kan harkokin gwamnati.

Jigo a APC ya yi magana kan Peter Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar APC, Alwan Hassan, ya ce 'yan Arewa ba za su zabi Peter Obi ba a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya gano dalili 1 da zai hana 'yan Arewa zabar Peter Obi a 2027

Jigon na APC ya bayyana cewa 'yan Arewa ba za su zabi Peter Obi ba ne saboda sana'arsa ta shigo da giya.

Ya nuna cewa mutanen yankin ba za su zabi mutumin da yake da sana'ar da ta sabawa al'ada da addininsu ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel