Rigima Ta Ɓarke tsakanin Shugaba Tinubu da Ganduje ana Shirin 2027? An Samu Bayani

Rigima Ta Ɓarke tsakanin Shugaba Tinubu da Ganduje ana Shirin 2027? An Samu Bayani

  • Malam Muhammed Garba ya yi bayani kan halin da ake ciki tsakanin tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje da Bola Tinubu
  • Tun lokacin da Ganduje ya yi murabus daga shugabancin APC, aka fara yaɗa jita-jitar cewa alaƙarsa da Shugaba Tinubu ta yi tsami
  • Tsohon shugaban ma'aikatan Ganduje ya ƙaryata labari, yana mai cewa har yanzu akwai kyakkyawar fahimta tsakanin shugabanni

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Tun bayan saukar Dr. Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin jam'iyyar APC aka fara yaɗa jita-jitar cewa alaƙarsa da Shugaba Bola Tinubu ta yi tsami.

Wasu na ganin cewa shugaban ƙasar ne ya umarnci Ganduje ya ajiye muƙamin shugaban APC na ƙasa saboda wasu dalilai da suka shafi dabarun zaɓen 2027.

Tsohon shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje
An musanta zargin alaƙa ta yi tsami tsakanin Shugaba Tinubu da Ganduje Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

Rigima ta shiga tsakanin Tinubu da Ganduje?

A wata hira da jaridar Daily Trust, Malam Muhammed Garba ya musanta wannan raɗe-raɗi, inda ya ce Ganduje ne ya yanke shawarar ajiye shugabancin APC bisa ra'ayin kansa.

Kara karanta wannan

Babu ɓoye ɓoye, an ji halin da tsohon shugaban APC, Ganduje ke ciki a Landan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhammed Garba, tsohon shugaban ma'aikatan shugaban APC na ƙasa, ya ce tsohon gwamnan Kano na da kyakkyawar alaƙa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu

A cewarsa, mutane na da ƴancin faɗar duk abin da suke so, amma babu wani saɓani da ya shiga tsakanin Ganduje da Tinubu.

Abin da ya faru kafin Ganduje ya yi murabus

Da yake musanta zargin cewa tilastawa Ganduje aka yi ya ajiye shugabancin APC, Malam Muhammed Garba ya ce:

"Babu wanda ya tilastawa Ganduje, ya yi murabus ne bayan kammala kusan kashi 90% na ayyukan da shugaban kasa ya ɗora masa, kowa ya san wannan, ba ƙarya ba ne."
"Kawai ya ga yana buƙatar ya huta bayan gama aiki da ke gabansa, kuma idan ka duba ka san APC ta ƙara samun ci gaba fiye da yadda ya tarar.
"Kafin ya yi murabus daga shugabancin APC sai da ya nemi shawarar shugaban ƙasa, Tinubu ya ce masa tun da ya riga ya yanke shawara ba zai hana shi ba.

Kara karanta wannan

Kungiyoyin Arewa sama da 1,000 sun tsaida wanda za su zaɓa tsakanin Tinubu da Atiku a 2027

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu tare da Ganduje.
Ganduje yana zaune lafiya da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

'Mutane na yaɗa ƙarya kan Ganduje da Tinubu'

Dangane da batun cewa rigimar siyasa ta shiga tsakanin Ganduje da Shugaba Tinubu, Muhammed Garba ya ce babu wani abu makamancin haka.

"Wa ya faɗa muku? Ka ga, mutane na iya faɗar duk abin da suke so bisa yadda suka fahimta. Amma ku ji daga bakina, babu wani abu makamancin saɓani tsakanin Ganduje da shugaban ƙasa Tinubu.
"Mutane suna ƙirƙirar abubuwan da ba gaskiya ba, kuma su yi ta yaɗa labaran ƙarya kan abubuwan da ba su san komai a kai ba."

- Malam Muhammed Garba.

Me ya hana Ganduje tarbar Tinubu a Kano?

A baya, kun ji cewa Ganduje bai je wurin tarbar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ba lokacin da ya kai ziyara jihar Kano domin ta'azuyyar rasuwar Aminu Ɗantata.

Rashin ganin Ganduje ya ja hankalin jama'a amma hadiminsa, Muhammed Garba ya tabbatar da vewa ba ya ƙasar a lokacun da Shugaba Tinubu ya je Kano.

Ya ce Ganduje ya yi ƙoƙarin sauya jadawalin tafiyar domin ya dawo a kan lokaci ya tarbi Shugaba Tinubu a Kano amma hakan bai samu ba saboda wasu matsaloli.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262