2027: El Rufa'i Ya Yi Martani a Fusace da aka Ce Siyasar Shi Ta Zo Karshe

2027: El Rufa'i Ya Yi Martani a Fusace da aka Ce Siyasar Shi Ta Zo Karshe

  • Nasir El-Rufai ya maida martani ga wani mutum da ya ce labarin tsohon gwamnan a siyasar Najeriya ya zo karshe
  • El-Rufai ya ce da mutumin da ya ajiye wannan maganar da ya yi a kusa har zuwa 1 ga Maris, 2027, lokacin da zai gane gaskiya
  • Tsohon gwamnan bai fayyace ko zai yi magana a matsayinsa na mai nasara ko na wanda ya sha kaye ba a zaben 2027

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna – Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya maida martani ga wani mai amfani da kafar sada zumunta da ya ce yanzu ba shi da katabus a siyasa.

Hakan na zuwa ne yayin da Nasir El-Rufa'i ya fice daga APC ya koma SDP kuma ya ke shirin jagorantar hadaka a ADC.

Kara karanta wannan

'A murƙushe su kawai': Shehi ya faɗi hukuncin Musulunci kan irinsu Bello Turji

Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i. Hoto: Kaduna State Government
Source: Twitter

Wani mai amfani da X da ke amfani da sunan Eureka ya yi ikirarin cewa yanzu ba a maganar El-Rufai a siyasa, kuma yanzu yana ɓuya ne a bayan ra’ayoyin wasu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta gano Eureka ya rubuta cewa:

“Labarin El-Rufai ya zo karshe. Siyasar sa ta ƙare. Yanzu yana ɓoye a bayan rubuce-rubucen wasu da maganganun su. Duk surutunsa a baya, yanzu El-Rufai yanzu ba ya iya magana.”

Wace amsa El-Rufai ya ba Eureka?

A martaninsa, El-Rufai, wanda ya bar jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar SDP kuma ya zamo daya daga cikin masu suka ga gwamnatin Bola Tinubu, ya ce Eureka zai tuna maganarsa bayan 2027.

Tsohon gwamnan ya bukaci Eureka ya ajiye wannan sako har zuwa 1 ga Maris, 2027, lokacin da zai fitar da ra’ayinsa game da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

El-Rufai ya rubuta:

“A mafarkinka kenan… lokacin da zan fara magana, za ka tuna maganarka… ka ajiye wannan saƙo har ranar 1 ga Maris, 2027 in sha Allah.”

Kara karanta wannan

Borno: Hankula sun tashi, an samu gawar mji, mata da 'ya'yansu a wani yanayi

Martanin ‘yan Najeriya kan lamarin

Bayan maganar El-Rufai, wasu daga cikin ‘yan Najeriya sun bayyana ra’ayoyinsu a sashen sharhi, inda wasu suka yaba da jajircewarsa yayin da wasu kuma suka nuna shakku.

Legit ta rahoto cewa Chidi ya rubuta cewa:

“Shi ne kaɗai ɗan Arewa da zan iya kaɗa masa ƙuri’a. Zan yi hakan ne ba don dadin zance ba, sai don abin da ya tabuka a FCT da a matsayin gwamna.
"Duk da akwai inda ya kamata ya gyara kamar nuna son addini, amma baya ga haka, mutum ne mai fasaha, mai basira.”

NED ya ce:

“Ni Ibo ne, zan iya zabenka, zan kaɗa maka ƙuri’a. Matsalata ɗaya da kai kawai ita ce wariyar addini. Bayan haka, kai ne mafi cancanta.”
Nasir El-Rufa'i da 'yan adawa a wani taro
Nasir El-Rufa'i da 'yan adawa a wani taro. Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Facebook

Engr Jay Umar ya rubuta:

“Ranar 1 ga Maris, 2027, in sha Allah, kai za ka yi kuka kana ihu kana cewa an yi maguɗi. Za ka tuna wannan, ranka ya daɗe.”

Kara karanta wannan

'Najeriya ka iya wargajewa kafin zaɓen 2027': Tsohon minista ya yi hasashe

Adedayo ya ce:

“Kana magana kamar kai ne Allah. A 2027, babu wani abu da zai faru. Ko ka ci zabe ko ka yi ritaya gaba ɗaya.”

2027: APC ta yi wa El-Rufa'i martani

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi wa tsohon gwamnan jihar Kaduna martani kan siyasar 2027.

APC ta ce kokarin da El-Rufa'i ya ke na hada 'yan adawa su kara da shugaban kasa Bola Tinubu a 2027 ba zai yi nasara ba.

Kakakin jam'iyyar APC, Felix Morka ne ya bayyana haka yayin hira da manema labarai a Abuja, inda ya ce za su yi nasara a zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng