2027: An Ji Ra'ayin Jonathan kan Fafatawa da Shugaba Tinubu

2027: An Ji Ra'ayin Jonathan kan Fafatawa da Shugaba Tinubu

  • Batun sake takarar kujerar shugaban kasa na Goodluck Ebele Jonathan na kara girma a fagen siyasar Najeroya
  • Wani abokin tsohon shugaban kasan ya bayyana cewa ya amince ya fafata da mai girma Bola Tinubu a zaben 2027
  • Aminin na Jonathan ya nuna cewa tsohon shugaban ya fara tattaunawa da manyan shugabanni kan batun takarar tasa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan, na daga cikin manyan 'yan takarar da ake sa ran za su kara da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a zaben 2027.

Wani amininsa na kusa ya ce tsohon shugaban kasan yana daga cikin wadanda za su fafata da Shugaba Tinubu.

Jonathan zai yi takara a 2027
Jonathan zai fafata da Tinubu a 2027 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Goodluck Jonathan
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce wani aminin tsohon shugaban kasan ne ya tabbatar mata da hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jonathan ya amsa tayin takara da Tinubu

Kara karanta wannan

Tinubu: Gwamnati ta kashe N26.38bn a kan jiragen shugaban ƙasa a cikin watanni 18

Aminin na Jonathan, wanda shi ma dan PDP ne, ya bayyana cewa shirin dawo da Jonathan takarar shugabancin kasa a ƙarƙashin jam’iyyar ya yi nisa, kuma ya karɓi tayin.

Ya kara da cewa Jonathan ya yanke shawarar shiga takarar ne domin neman hanyoyin da za su rage fatara, wahala da kuncin rayuwa da ya addabi 'yan Najeriya cikin ‘yan shekarun nan.

Majiyar ta ce wannan aiki na dawo da Jonathan domin gyara Najeriya ana jagorantarsa ne daga manyan shugabanni da dattawan kasar waɗanda suka yi imani cewa Jonathan ya daidaita Najeriya da tattalin arzikinta a lokacin mulkinsa na shekaru shida.

Majiyar ta ce, kokarin da ake yi na ceto kasar da kuma dawo da martabarta ta tattalin arziki shi ya sa dattawan jam’iyyar PDP da wasu shugabanni suka fara roƙonsa da ya yi la’akari da takarar shugaban kasa a 2027 don ya kara da Tinubu.

Kara karanta wannan

2027: Yadda aka samu shugabanni 2 ko fiye a ADC da wasu jam'iyyun adawa a Najeriya

Wasu suna ganin cewa bai wa Jonathan damar yin takara domin ya yi wa’adin shekara hudu kadai, ita ce hanya mafi sauki da za ta mayar da mulki Arewa a shekarar 2031.

Aminin na Jonathan ya ce dan siyasar wanda ya fito daga garin Otuoke, ya riga ya gana da wasu manyan shugabanni a cikin da wajen jam’iyyar PDP don neman shawara da goyon baya game da takararsa a 2027.

Jonathan ya amsa kira kan takara da Tinubu
Jonathan ya amince ya yi takara a 2027 Hoto: @GEJonathan, @DOlusegun
Asali: UGC

Jonathan ya gana da Janar Babangida

A cewarsa, Jonathan ya gana da tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya), a karshen makon da ya gabata a gidansa da ke Minna, jihar Neja, inda ya sanar da shi burinsa na tsayawa takara don yin wa’adi daya a 2027.

Ko da yake majiyar ba ta bayyana abin da Janar IBB ya ce ba, amma ta nuna cikakken kwarin gwiwa cewa an yi wa yankin Arewa cikakken bayani game da wannan tsari, kuma ana ganin za su goyi bayan hakan.

Kara karanta wannan

APC ta yi watsi da kalaman El Rufai, ta fadi dalilin da zai sa Tinubu yin tazarce a 2027

Bashir Ahmad ya yi magana kan Jonathan

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon hadimin Muhammadu Buhari, ya bayyana wani shiri da ake yi kan Goodluck Jonathan.

Bashir Ahmad ya bayyana cewa wasu 'yan siyasa na kokarin jawo Jonathan domin ya yi takara a zaben 2027.

Ya nuna cewa ana yin wannan shirin ne domin samun kuri'un 'yan Arewa saboda zai yi wa'adin mulki daya ne kawai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng