Wike Ya Kai PDP Makura, An Sanya Lokacin Hukunta Ministan Tinubu

Wike Ya Kai PDP Makura, An Sanya Lokacin Hukunta Ministan Tinubu

  • Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar PDP a yankin Kudu maso Kudu, Emmanuel Ogidi, ya nuna takaicinsa kan ayyukan Nyesom Wike
  • Emmanuel Ogidi ya bayyana cewa jam'iyyar adawa ta PDP ta gaji da abubuwan da Wike yake yi kuma za ta dauki mataki a kansa
  • Ya nuna cewa kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na PDP zai zauna domin gano matakin da ya kamata a dauka kan Wike

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Rivers - Shugaban kwamitin rikon kwarya na yankin Kudu maso Kudu na jam’iyyar PDP, Emmanuel Ogidi, ya yi magana kan batun ladabtar da Nyesom Wike.

Emmanuel Ogidi ya bayyana cewa kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) zai duba ayyukan Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, kuma zai yanke hukunci a mako mai zuwa.

PDP ta shirya hukunta Nyesom Wike
PDP ta gaji da halayen Nyesom Wike Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce a wata hira da aka yi da shi, Ogidi ya ce jam’iyyar ta gaji da yadda Wike ke tafiyar da al’amuransa, kuma yanzu ta shirya ta yanke hukunci a kansa.

Kara karanta wannan

'Tinubu zai kori Wike,' Sule Lamido ya fito da bayanai kan ministan Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya kafa sharudan sulhu a PDP

Idan ba a manta ba dai, a wata hira da Wike ya yi da manema labarai a ranar Litinin, ya gindaya wasu sharudda ga shugabancin jam’iyyar domin samun zaman lafiya.

Wike ya ce dole ne jam’iyyar ta amince da sakamakon zaben shugabannin yankin Kudu maso Kudu da bangarensa ya gudanar, wanda aka yi watsi da shi.

Haka kuma ya bukaci jam’iyyar ta ƙi amincewa da sakamakon zaben shugabannin yankin Kudu maso Gabas wanda ya haifar da shugabannin da suka hada da Ali Odefa, domin a samu zaman lafiya kafin babban taron jam’iyyar.

Jam'iyyar PDP ta gaji da halayen Wike

Amma a martanin da ya mayar, Emmanuel Ogidi ya bayyana cewa PDP tana da girman da ta fi karfin mutum daya ya tsaya yana juya ta.

"PDP gida ne babba, amma zan iya tabbatar muku cewa NWC za ta dauki mataki a kan Wike mako mai zuwa, domin ba zai yi wu kasance karkashin ubangida biyu ba."

Kara karanta wannan

Belin dilan ƙwaya: Kwamishinan Abba a jihar Kano ya yi murabus

"Ban san dalilin da ya sa APC ke jure masa ba, domin ko su kansu yana musu illa da kalamansa."
"Mun dade muna hakuri da shi, babu rikici a jam’iyyar. Abin da ya rage shi ne taron NEC a wannan wata da kuma babban taro."
"Ko da yana ƙoƙarin tayar da wani sabon rikici, to wannan kuma shi ta shafa, amma na fahimci fushin da yake yi."
"Yana yin aikin APC ne, amma mun jure masa ne saboda irin gudummawar da ya bayar a baya. A lokacin baya, ya yi abubuwa masu kyau da dama. Amma akwai wasu da su ma sun bayar da irin wannan gudunmawa."
"Ya kai kololuwa yanzu. Ni kaina ina dannewa ne, ba na son yin magana da zuciya, amma wani lokaci ya dace a fadi gaskiya.”

- Emmanuel Ogidi

Wike ya tsokanowa kansa rigima a PDP
PDP ta shirya daukar mataki kan Wike Hotp: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Wike ya yi wa Atiku shagube

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya yi wa Atiku Abubakar, shagube kan ficewa daga PDP.

Kara karanta wannan

APC ta yi watsi da kalaman El Rufai, ta fadi dalilin da zai sa Tinubu yin tazarce a 2027

Wike ya bayyana cewa Atiku Abubakar ya zama gwani wajen sauya sheka daga wannan jam'iyya zuwa wancan.

Ministan ya nuna cewa Atiku ya fice daga PDP ne bayan ya fahimci cewa ba zai samu takarar shugaban kasa ba a zaben 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel