ADC Ta Yi Wa PDP Illa, Na Kusa da Bukola Saraki Ya Koma Tafiyar Su Atiku

ADC Ta Yi Wa PDP Illa, Na Kusa da Bukola Saraki Ya Koma Tafiyar Su Atiku

  • Tsohon jakadan Najeriya a kasar Jafan, Mohammed Yisa Gana ya tattara komatsansa ya fice daga jam'iyyar adawa ta PDP
  • Mohammed Yisa Gana wanda yake na kusa ne ga Sanata Bukola Saraki ya kuma sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC bayan ya raba gari da PDP
  • Tsohon jakadan ya nuna godiyarsa ga jam'iyyar PDP bisa damarmakin da ya samu a karkashinta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kwara - Tsohon jakadan Najeriya a kasar Japan, Mohammed Yisa Gana, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP.

Mohammed Yisa Gana wanda na kusa ne ga tsohon shugaban majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya koma jam'iyyar ADC bayan ficewa daga PDP.

Mohammed Yisa Gana ya fice daga PDP
Mohammed Yisa Gana ya koma ADC Hoto: @bukolasaraki
Source: Twitter

Tsohon jakadan ya sanar da ficewarsa daga PDP ne a cikin wata wasika da ya rubuta a ranar 16 ga Yuli, 2025, cewar rahoton jaridar The Cable.

Kara karanta wannan

Sanata na shirin barin APC watanni bayan komawa, an ji yadda lamarin yake

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasikar dai an mika ta ga shugaban jam’iyyar PDP na mazabar Kpada II da ke ƙaramar hukumar Patigi a jihar Kwara, rahoton Tribune ya tabbatar.

Tsohon jakada ya koma ADC daga PDP

Hakazalika, tsohon jakadan ya sanar da sauya shekarsa zuwa jam'iyyar ADC a cikin wasikar.

A cikin wasikar, Muhammad Yisa Gana ya nuna godiyarsa ga jam’iyyar PDP bisa damarmakin da ta ba shi wajen wakiltar ƙaramar hukumarsa, jiharsa da kuma Najeriya a matakai daban-daban.

Sai dai, ya ce yana jin lokaci ya yi da zai ci gaba da tafiya a wani sabon matsayi domin samun ci gaba mai ma’ana ga mutanensa da kuma ƙasa baki ɗaya.

"Daga yau, 16 ga watan Yuli, 2025, ina sanar da ficewa ta daga jam’iyyar PDP."
"Yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar ba abu ne da ya zo min da sauƙi ba, musamman ganin irin damarmakin da jam’iyyar ta ba ni a baya don wakiltar ƙaramar hukumata, jihata da kuma ƙasata a matakai daban-daban, wanda nake matuƙar godiya akai."

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya gano babbar matsalar 'yan hadaka, ya ba su.shawara kan 2027

"Amma, ya zama dole yanzu na ci gaba da neman ci gaba mafi girma ga mazabata da kuma Najeriya baki ɗaya."
"Yayin da nake barin PDP, zan koma jam’iyyar ADC a matsayin sabuwar jam’iyyata. Ina fatan alheri ga jam’iyyar PDP a dukkan abin da ke gabanta."

- Muhammad Yisa Gana

Jigo a PDP ya koma ADC
Tsohon jakada ya koma ADC daga PDP Hoto: Legit.ng
Source: Original

A baya-bayan nan, Bukola Saraki, wanda ke jagorantar kwamitin sulhu da shirye-shiryen babban taron PDP, ya yi gargadin cewa karin fitattun ’yan siyasa na iya ficewa daga jam’iyyar idan ba a magance rikice-rikicen cikin gida da wuri ba.

Sule Lamido ya gano kuskure a ADC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana cewa akwai garaje a cikin al'amuran 'yan siyasar da ke cikin hadakar ADC.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa da yawa daga cikinsu na yin gaggawa wajen neman takara ba tare da fitar da tsari mai kyau ba.

Sule Lamido ya bukaci 'yan hadakar da su tsaya su fitar da tsari mai kyau wanda zai sanya su kawar da jam'iyyar APC a zaben 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng