Tinubu na tsaka Mai Wuya, PDP Ta Fara Nuna Wanda Za Ta Tsayar Takara a Zaɓen 2027
- Jam'iyyar PDP na ci gaba da aikin neman shawarwari da tattaunawa kan wanda za ta tsayar takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027
- Tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Jonathan na ɗaya daga cikin waɗanda PDP ke ganin za ta bai wa tikitin takara domin ceto Najeriya
- Sakataren kuɗin PDP na ƙasa, Daniel Woyengikuro ya ce akwai buƙatar Jonathan ya dawo cikin harkokin tafiyar da PDP gadan-gadan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Babbar jam’iyyar adawa, PDP ta fara tunanin dawo da tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Jonathan fagen siyasa tare da tsayar da shi takara a 2027.
PDP ta nuna cewa a shirya take ta ba Jonathan tikitin takarar shugaban ƙasa ba tare da hamayya ba matukar ya dawo, ya ci gaba da ba da gudummuwa a harkokin jam'iyya.

Kara karanta wannan
Bayan ya baro PDP, Sanata Melaye ya kawo hanyar da ADC za ta buga Tinubu da ƙasa a 2027

Asali: Getty Images
Daniel Woyengikuro, Sakataren Kuɗi na PDP ta ƙasa ne ya bayyana haka a cikin wata hira ta musamman da aka yi da shi a birnin Abuja, kamar yadda Vanguard ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP ta fahimci Jonathan ya karɓu a Najeriya
Ya ce har yanzu Jonathan yana da tasiri sosai tare da masoya a Kudu da Arewacin ƙasar nan, yana mai kiransa da jagoran jam’iyyar PDP na ƙasa.
"Shin kuna ganin a yanzu, ba shi ne mafi cancanta a gare mu ba? Ba kawai tsohon shugaban ƙasa ba ne shi ne jagoran jam’iyyar PDP yanzu.
"Idan ka cire tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, mutum na gaba da ya fi tasiri a PDP shi ne Goodluck Jonathan, shi ne jagoran jam'iyyarmu na ƙasa."
- inji Woyengikuro.
PDP ta fara ƙoƙarin dawo da Jonathan siyasa
Ya tabbatar da cewa PDP na ci gaba da tattaunawa da Jonathan da mukarrabansa domin jawo shi ya dawo cikin tafiyar jam’iyyar.
A cewarsa, hakan a wani shiri na sake farfaɗo da jam’iyyar PDP tare da fuskantar ƙalubalen siyasa da tattalin arziki da ƙasar ke ciki idan ta samu galaba kan Bola Tinubu a 2027.
“Najeriya ta kai wani mataki da dole ne mu tashi mu ceto ƙasarmu domin amfaninmu da zuriyarmu. Idan ana magana kan mulkin kudu, babu wanda ya ɗara Goodluck Jonathan.”

Asali: Twitter
Shin PDP za ta ba Jonathan takara kai tsaye?
A lokacin da aka tambaye shi kaan cewa ko PDP za ta ba Jonathan tikitin takarar shugaban ƙasa ba tare da hamayya ba, sai Woyengikuro ya amsa da ƙarfi cewa:
"A wurina, hakan shi na fi so, za ku iya yaɗa abin da na faɗa a ko’ina, ina son ya dawo. A yanzu ina ganin ya kamata ba shi tikiti kai tsaye domin dole ne mu ceci wannan jam’iyya da ƙasar nan gaba ɗaya.”
Ya ƙara da cewa dawowar Jonathan za ta canza salo da yanayin siyasar Najeriya gaba ɗaya gabanin zaɓen 2027, rahoton Guardian.
Ƴan Taraba sun roƙi ADC ta jawo Jonathan
A wani rahoton, kun ji cewa mazauna Jalingo, babban birnin jihar Taraba sun buƙaci haɗakar ADC ta tsayar da Goodluck Jonathan takara a zaɓen 2027.
Mutanen sun bukaci shugabannin kawancen jam’iyyar ADC da su kawar da son zuciya su tsayar da tsohon shugaban kasar don zai iya kayar da Bola Tinubu.
A cewarsu, Jonathan ne kaɗai ɗan takara daga Kudu wanda ƴan Arewa za su yi maraɓa da shi, kuma yana da ƙarfin kwace mulki daga hannun APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng