'A Bi a Sannu,' Jagora a APC Ya Yi Magana kan Fara Yi wa Tinubu Kamfe

'A Bi a Sannu,' Jagora a APC Ya Yi Magana kan Fara Yi wa Tinubu Kamfe

  • Jagora a APC, Charles Udeogaranya ya bukaci Bola Tinubu ya dakatar da kamfen 2027 domin mai da hankali kan cika alkawuran mulki
  • Ya bayyana haka ne a lokacin da INEC ta gargadi ‘yan siyasa su guji fara kamfen da wuri domin hukumar ba ta fitar da jadawalin zaɓe ba
  • Udeogaranya ya ce kamfen da wuri yana hana nagartaccen shugabanci kuma yana haddasa zafin siyasa, kuma jama'a za su galabaita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Tsohon mai neman takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, Charles Udeogaranya, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya dakatar da kamfen ɗin neman tazarce a 2027.

Ya bayyana cewa yanzu abin da ya fi dace wa shi ne ya mayar da hankali wajen cika alkawuran da ya ɗaukar wa ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Yadda Remi Tinubu ta raba tallafin N4.15bn a Najeriya a cikin shekara 1

Shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
An shawarci Tinubu kan zaben 2027 Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta rawaito cewa Udeogaranya ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar daga birnin Abuja a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jagora a APC ya shawarci Bola Tinubu

Udeogaranya ya ce fara neman goyon baya da yakar ‘yan adawa tun yanzu abin damuwa ne da kuma rashin da’a ga doka ne a kasar nan.

Shugaban kasa, Bola Tinubu
Kusa a APC ya ce ya yi wuri a fara batun 2027 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A cewarsa:

“Ya kamata Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rage gaggawar neman kuri'a, ya kuma dakatar da maganar takarar 2027, musamman ta bakin mukarrabansa, wanda a ganina hakan bai dace da lokaci ba.”
“Akwai lokacin komai. Yanzu lokaci ne na shugabanci har zuwa watan Yuni 2026, a kalla.”

2027: INEC ta ja kunnen ‘yan siyasa

Wadannan shawarwarin na Udeogaranya na zuwa ne kasa da kwana biyu bayan Hukumar INEC ta fitar da gargadi ga jam’iyyun siyasa da ‘yan takara su guji kamfen din da wuri gabanin zaɓen 2027.

Kakakin Shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi, ya bayyana cewa har yanzu hukumar ba ta fitar da jadawalin zaɓen 2027 ba.

Kara karanta wannan

Minista ya kwadaitawa Ibo mulkin Najeriya, ya ce taimakon Tinubu zai kai su Aso Rock

A kan wannan kira, Udeogaranya ya ce tuni alamomi su ka bayyana ganin yadda 'yan siyasa suka cika buri kafin babban zaben.

Ya ce:

“Akwai lokacin jingine maganganu a kan siyasa domin kar a gurbata harkokin mulki ko ƙara zafi a harkar siyasa, ta yadda gwamnati za ta samu isasshen lokaci ta yi aikinta.”

Ya shawarci 'yan siyasa da su sanya wa bukatunsu linzami domin a bayar da dama ga gwamnati ta sauke alkawarin da ta dauka na raimakon wanda su ka zabe ta.

Tinubu ya kashe kudi kan jiragen shugaban kasa

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta kashe kimanin Naira biliyan 26.38 wajen tafiyar da harkokin jiragen fasinjojin shugaban ƙasa a cikin watanni 18 na farkon mulki.

Wani rahoto ya nuna cewa an fitar da wannan kuɗi daga watan Yuli 2023 har zuwa Disamban 2024, inda aka yi amfani da su domin tafiyar da jiragen fadar Shugaban Kasa.

A cewar rahoton, ranar 14 ga Yuli, 2023, gwamnati ta biya Naira Miliyan 846.03 kan wasu bukatun tafiyar jiragen zuwa ƙasashen waje, bayan kwana biyu, aka kuma fitar da N674.82m.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel