APC Ta Yi wa Tinubu Alkawari yayin da Ta Jaddada Mubaya'a ga Ganduje a Kano
- Jiga-jigan APC a Kano sun sake jaddada biyayya ga Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayin wani babban taro da aka yi a jihar
- A jawabin bayan taro, shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas ya zayyano wasu daga cikin ci gaban da Ganduje ya kawowa jwam'iyya
- Amma an gano kusoshin APC da a gani a taron ba, daga ciki akwai mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Manyan jam’iyyar APC a jihar Kano sun sake jaddada biyayyarsu ga tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Sun kuma sha alwashin ƙarfafa ƙoƙarinsu na wayar da kan jama’a da tara mabiya domin samun nasara a zaɓen 2027 mai zuwa.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jam’iyyar ta yi wannan jawabi ne a wani babban taro da Ganduje ya shirya a gidansa da ke Kano a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babu wasu manyan APC a taron Kano
Daily Post ruwaito cewa an da rashin halartar mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin da kuma karamin Ministan gidaje na ƙasa, Yusuf Abdullahi Ata.
An bayyana cewa Barau na ƙasar waje ne saboda rasuwar surukarsa a birnin Landan, yayin da ba a iya tabbatar da dalilin rashin halartar Ministan ba.
A wata sanarwa da aka fitar bayan taron, shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya yabawa jagorancin Ganduje da rawar da ya taka wajen sake fasalin jam’iyyar a zamaninsa.
Ya ambato irin sauye-sauyen da aka samu kamar: Rajistar 'yan jam'iyyar ta intanet da shirye-shiryen tallafawa matasa da mata.
Taron ya nuna kwarin gwiwar cewa APC za ta ci nasara a zaɓukan cike gurbi da ke tafe, tare da tabbatar da Kano a matsayin mafakar jam’iyyar tare da tsaya wa don kawo wa Bola Tinubu Kano a 2027.
Manyan APC da suka halarci taron Kano
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila; ‘yan takarar gwamna da mataimakinsa a zaɓen 2023, Dr Nasiru Yusuf Gawuna da Murtala Sule Garo.
Sauran sun haɗa da karamar Ministar Abuja ta ƙasa, Dr Mariya Mahmoud Bunkure; da wasu ‘yan majalisun tarayya da na jiha.

Asali: Facebook
Yayin taron, sun sake jaddada goyon bayansu ga gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, tare da yabawa kokarin gwamnatin tarayya wajen kawo ci gaba a yankin Arewa, musamman Kano.
Shugaban kwamitin kasafi na Majalisar Wakilai, Hon. Abba Kabir Bichi, wanda ke wakiltar mazabar Bichi, ya bayyana wasu muhimman ayyuka.
Ya ce sun hada da hanyar Abuja-Kaduna-Zaria-Kano, hanyar Kano-Hadeja, da hanyar jirgin ƙasa ta Kano, waɗanda kudinsu ya haura biliyan 250.
Ya ce:
“A matsayina na shugaban kwamitin kasafi, na san abin da aka ware. Shugaban ƙasa ya yi abubuwa da dama. Dole mu faɗi gaskiya kan ci gaban da aka samu zuwa yanzu.”
Jam'iyyar APC ta caccaki nasir El Rufa'i
A baya, mun wallafa cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta bayyana tabbacin cewa ‘yan Najeriya za su sake zabar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027 mai zuwa saboda wasu dalilai.
A cewar jam’iyyar, wa’adin mulki na farko na Shugaba Tinubu na daga cikin mafi fice a tarihin Najeriya tun bayan samun ‘yancin kai saboda ayyukan ci gaba da ake samar wa.
Jam’iyyar ta APC ta bayyana irin nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu a fannonin tattalin arziki, tsaro da cigaban al’umma a matsayin dalilan da za a sake zabarsa kari na biyu.
Asali: Legit.ng