Kimanin Wata 1 da Rasuwar Buhari, Adamu Maina Ya Auna Mulkinsa da na Shugaba Tinubu

Kimanin Wata 1 da Rasuwar Buhari, Adamu Maina Ya Auna Mulkinsa da na Shugaba Tinubu

  • Tsohon ministan kula da harkokin ƴan sanda ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu ta fi ta Muhammadu Buhari maida Najeriya baya
  • Adamu Maina Waziri ya ce yana mamakin yadda waɗanda ke rayuwa a wuraren da ƴan bindiga suka hana zaman lafiya ke goyon bayan Tinubu
  • Jigon na jam'iyyar ADC ya buƙaci ƴan Najeriya su auna wannan gwamnati, ka da su sake a ruɗe su da labaran kafafen yaɗa labarai

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Jigo a jam’iyyar haɗaka watau ADC kuma tsohon Ministan Jin Daɗin ‘Yan Sanda, Adamu Maina Waziri, ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Ya bayyana gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a matsayin babban bala’i wanda ya gaza fiye da gazawar gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Tsohon minista ya ce gwamnatin Tinubu ta fi ta Buhari lalata Najeriya Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

A wata hira da ya yi da talabijin Trust tv, Alhaji Maina Waziri ya nuna damuwa matuƙa kan halin da Najeriya ke ciki a yanzu, yana mai gargadin cewa ƙasar na cikin haɗari mai tsanani a ƙarƙashin jagorancin Tinubu.

Kara karanta wannan

Minista ya kwadaitawa Ibo mulkin Najeriya, ya ce taimakon Tinubu zai kai su Aso Rock

An auna gwamnatin Buhari da ta Tinubu

Adamu Maina Waziri ya ce:

“Idan gwamnatin Buhari ta gaza, to gwamnatin Tinubu cikin shekaru biyu da suka wuce kaɗai ta zama masifa mai haɗari. Ta gaza a dukkan fannonin rayuwa, kuma ƙasar baya take ci.”

Tsohon ministan ya bayyana taɓarɓarewar matsalar tsaro, matsin tattalin arziki, da ƙaruwar cin hanci da rashawa a matsayin alamomin gazawar gwamnati mai ci

“Tattalin arziki na rushewa, nuna ƙabilanci da wariya ya kai matsayi mafi muni, kuma matsalar tsaro na ci gaba da addabar jihohi da dama,” in ji Waziri.

'Gwamnatin Tinubu ta kama hanyar rusa Najeriya'

Ya yi ikirarin cewa Shugaba Tinubu ya ƙara jawo rabuwar kai, kuma idan aka tafi a haka, Najeriya ta kama hanyar rushewa, rahoton Daily Post.

Adamu Maina Waziri ya nuna mamaki kan yadda wasu ke ci gaba da goyon bayan gwamnati mai ci alhali yankunansu ne ke fama da hare-haren ‘yan bindiga da rikice-rikice.

Kara karanta wannan

'Mene aka yi mana?' Hadimin Ganduje ya ce za su tuhumi Tinubu a Kano

"Na yi mamakin yadda mutane daga ƙananan hukumomin da ke ƙarƙashin ikon ‘yan ta’adda ke bayyana a talabijin na ƙasa suna goyon bayan wannan gwamnati,” in ji shi.
Muhammadu Buhari da shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Adamu Maina Waziri ya ce yana mamakin masu goyon bayan Tinubu Hoto: @MBuhari, @OfficialABAT
Source: Twitter

Tsohon ministan ya buƙaci ƴan Najeriya da suka yiwa kansu karatun ta natsu, su su auna wannan gwamnatin ta Tinubu ba tare da duba labaran da ake yaɗawa a kafafen watsa labarai ba.

A cewarsa, bai kamata gwamnatin da ta jawo wa ƙasa koma baya mafi muni ta iya fitowa tana neman tazarce ba.

Gwamnatin Tinubu za ta iya gyara ƙasar nan?

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu za ta iya warware duka matsalolin Najeriya a cikin shekaru takwas ba.

Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ne ya bayyana hakan ranar Litinin. ya ce babu gwamnatin da za ta iya gyara Najeriya ko da shekaru 20 aka ba ta.

Mista Wike ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Tinubu tana ƙoƙarin warware matsalolin da ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar ƴan ƙasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262