Kaduna: Rigima na Neman Ɓarkewa a Haɗakar ADC bayan Gano Shirin Nasir El Rufa'i
- Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya fara shan suka daga jiga-jigan ADC bisa zarginsa da yunƙurin tayar da rikici
- Ahmed Tijjani Mustapha, ɗaya daga cikin ƙusoshin ADC a Kaduna ya ce ba za su bari wani mutum ɗaya ya maida su ƴan amshin shata ba
- Ya buƙaci El-Rufai ya mutunta tsarin dimokuraɗiyya domin har yanzu bai zama cikakken ɗan jam'iyyar ADC ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Wani jigon ADC a Kaduna, Ahmed Tijjani Mustapha, ya yi zargi tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, da yunƙurin jawo masu rikici a jam'iyyar.
Ɗan siyasar ya gargaɗi El-Rufai ya kama kansa, ya daina yunkurin shiga tsoma hannu a harkokin ADC da nufin tayar da hankali da ruguza tsarin jam’iyyar a Kaduna.

Asali: Twitter
Ya zargi El-Rufai da shirya wata dabara ta kwace ikon jam’iyyar ta hanyar haɗa kai da wasu kungiyoyi, duk da cewa har yanzu bai yi rijistar zama mamban ADC a matakin mazaba ba, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan
"Shawarar da zan ba Atiku da ni ɗansa ne," Ministan Tinubu ya ɗauko tarihi tun daga 1999
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An zargi El-Rufai da shirin tayar da rikici
Da yake jawabi a taron manema labarai a Kaduna jiya, Ahmed ya gargadi El-Rufai da ya daina duk wani yunkuri da zai iya kawo rabuwar kai da durkusar da ADC a Kaduna.
Jigon ya ce:
"Ya kamata mu fahimci cewa jam’iyyar ADC reshen Jihar Kaduna ba za ta bari ta zama ƴar amshin shatan kowa ba, kuma ba za mu bar duk wanda zai ruguza mana zaman lafiyar cikin gida ba.
Ya zargi El-Rufai da hada kai da wasu tsofaffin abokan siyasarsa daga SDP da wasu 'yan siyasa wajen kokarin kafa tsaginsu a ADC
"Wannan abu bai dace ba kwata-kwata. Kuma kai tsaye barazana ne ga hadin kai, da’a, da kuma zaman lafiya wanda ya zama ginshikin ADC," in ji shi.
El-Rufai na fuskantar suka a ADC ta Kaduna
Ahmed Mustapha ya jaddada cewa duk da cewa ADC tana maraba da kowa, ba za ta bar masu halayen kama karya da danniya su mamaye ta ba, rahoton Vanguard.
Ya jaddada cewa za su ci gaba da goyon bayan muƙaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata David Mark 100%, yana mai cewa ADC ta shirya kawowa ƴan Najeriya mafita a 2027.

Asali: Twitter
"Muna kira ga Nasir El-Rufai da ya mutunta dimokuraɗiyya, ya bar tsarin da doka ta tanada ya gudana, kuma ya dakatar da duk wani yunkurin tayar da rikici,” in ji shi.
A karshe, ya jaddada cewa burin ADC shine haɗa kan jama’a a Jihar Kaduna da Najeriya baki ɗaya domin gina ƙasa mai adalci, dimokuraɗiyya da ci gaba.
El Rufai ya gargaɗi ƴan Najeriya kan zaɓen 2027
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bukaci 'yan Najeriya su tashi tsaye don kifar da gwamnatin APC a 2027.
Nasiru ya bayyana cewa idan aka yi kuskure barin APC ta ci gaba da mulki, ba dole ba ne Najeriya ta ci gaba da zama ƙasa.
Ya ce ya shirya tsaf domin haɗa kan duka ƴan Najeriya wajen kawo sauyi mai amfani, wanda zai ceto ƙasar nan daga rushewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng