El Rufai Ya Debo Ruwan Dafa Kansa, Jam'iyyar APC Ta Yi Masa Martani Mai Zafi

El Rufai Ya Debo Ruwan Dafa Kansa, Jam'iyyar APC Ta Yi Masa Martani Mai Zafi

  • Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ba ta ji dadin kalaman da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi ba a kan mulkin Bola Tinubu
  • Sakataren jam'iyyar APC na kasa ya bukaci El-Rufai da ya jira a bude yakin neman zabe kafin ya fara yada manufofinsa na siyasa
  • Ajibola Basiru ya nuna cewa ba za su bari tsohon gwamnan ya dauke musu hankali ba domin suna da abubuwan da za su yi a gabansu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta yi wa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, martani mai zafi kan kalamansa na baya-bayan nan.

APC ta shawarci El-Rufai da ya dakatar da yaɗa manufofinsa na siyasa tare da jira zuwa shekarar 2027 kafin ya fara yaƙin neman zaɓe.

APC ta caccaki Nasir El-Rufai
APC ta yi wa El-Rufai martani kan sukar Tinubu Hoto: @DOlusegun, @elrufai
Source: Facebook

Sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sanata Ajibola Basiru, ne ya bayar da wannan shawara a ranar Lahadi yayin wata hira da ya yi da jaridar Tribune ta wayar tarho.

Kara karanta wannan

APC ta yi babban rashi, tsoho 'dan majalisar tarayya ya sauya sheka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufai ya soki gwamnatin Tinubu

Ajibola Basiru yana mayar da martani ne kan kalaman da aka danganta da El-Rufai a ranar Asabar a jihar Sokoto, inda tsohon gwamnan ke jawabi ga magoya bayan ADC a wani taron da jam’iyyar ke gudanarwa a yankin Arewa maso Yamma.

El-Rufai ya yi gargadi ga ’yan Najeriya da su yi hattara kada su sake zaɓar APC a babban zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.

Ya bayyana cewa Najeriya za ta fuskanci ƙalubale wajen tsira idan jam’iyyar ta sake ci gaba da mulki har tsawon shekaru huɗu a ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Wane martani APC ta yi wa El-Rufai?

Amma a martaninsa ranar Lahadi, sakataren APC na kasa ya shawarci tsohon gwamnan na jihar Kaduna da ya samu abin yi da zai ɗauke masa hankali har zuwa lokacin zaɓe mai zuwa.

Ya bayyana cewa ka’idojin gudanar da zaɓen 2027 ba za su fito ba sai zuwa watan Fabrairu na 2026, yana mai tambayar dalilin da yasa El-Rufai ke gaggawa tun da har yanzu akwai sauran shekaru biyu kafin lokacin.

Kara karanta wannan

2027: Bayan hukuncin SDP, ADC ta mika bukata ga El Rufa'i

Jam'iyyar APC ta yi wa El-Rufai martani
Jam'iyyar APC ta caccaki Nasir El-Rufai Hoto: @elrufai
Source: Twitter
"Meyasa yake gaggawa haka? 2027 tana da nisa. Ka’idojin zaɓen 2027 ba za su fito ba sai watan Fabrairun 2026. El-Rufai ya je ya samu abin yi."
"Zai iya komawa makaranta domin ƙara karatunsa, ko ya zauna ya rika wasa da jikokinsa. Mu mun maida hankali wurin gyaran jam’iyyarmu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kuma yana da aikinsa na shugabanci. Kada ya dauke mana hankali."

- Ajibola Basiru

Sanata ya musanta ficewa daga APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Katsina ta Tsakiya, Abdulaziz Musa Yar'adua ya musanta ficewa daga jam'iyyar APC.

Sanata Yar'adua ya bayyana cewa har yanzu shi cikakken mamba ne a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Hakazalika ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan manufofin da gwamnatinsa take aiwatarwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng