An Fadi yadda Tinubu Ya Kafa Tubali Mai Karfi a Arewa don Doke Atiku da Obi
- Festus Keyamo ya ce Peter Obi ba zai iya samun goyon baya a yankin Arewa ba a zaben 2027 kamar yadda ake zato
- Ya bayyana cewa jam’iyyar APC da shugabanta Bola Ahmed Tinubu na da tsayayyun 'yan siyasa da gwamnoni a Arewa
- Keyamo ya ce hadakar jam’iyyun adawa da ke kokarin hada Obi da Atiku Abubakar ba za ta kai ko ina ba saboda wasu kalubale
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya bayyana cewa Peter Obi ba zai iya samun rinjaye a yankin Arewa ba a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Ya ce hadin gwiwar jam’iyyun adawa a karkashin tutar jam’iyyar ADC da ke kokarin hada Obi da Atiku Abubakar ba za ta yi tasiri ba a zabe mai zuwa.

Source: Twitter
Keyamo ya fadi haka ne yayin wata hira da aka yi da shi a Channels TV, inda ya ce Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyarsa ta APC sun riga sun kafa tubalin siyasa mai karfi a yankunan Arewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Obi ba zai yi nasara a Arewa ba" — Keyamo
Keyamo ya ce zaben 2027 ba zai kasance wa Obi kamar yadda ya samu karbuwa a 2023 ba, inda ya ce abubuwan da suka taimaka masa a baya ba za su yi tasiri a gaba ba.
Ya bayyana cewa:
“Duk sauran ‘yan takara Musulmai ne a 2023, Obi kadai ne Kirista, kuma yawancin Kiristoci sun koma gare shi.
"Na biyu, 'yan yankin Kudu maso Gabas sun ji ba a dama da su ba, suka yi tsayin daka don nasarar ɗan kabilar Ibo.
"Na uku kuma, matasa da ke cikin tafiyar ‘Obidients’ sun mara masa baya saboda yana da karancin shekaru a kan sauran 'yan takara."
Ya ce idan an hada Obi da Atiku a matsayin 'yan takara, to wadannan ginshikan uku za su rushe, saboda ba za su samu hadin kai irin na baya ba.

Source: Facebook
Keyamo: "Jam'iyyar APC ta kafu a Arewa"
Keyamo ya jaddada cewa Tinubu da jam’iyyarsa APC sun kafa tsayayyen tubalin siyasa a Arewa, ciki har da gwamnoni da sauran manyan shugabanni.
Vanguard ta wallafa cewa Keyamo ya ce:
“Yan adawa suna sanya mu muna kara ƙoƙari. Amma idan aka duba lissafi, babu alamar wannan hadakar adawa za ta iya doke mu.
"Sun yi tunanin hada Obi da Atiku don samun kuri’unmu fiye da miliyan 8, amma hakan ba zai yiwu ba.”
A baya-bayan nan, wasu fitattun ‘yan siyasa suka hadu domin kafa gagarumar kawancen adawa a karkashin jam’iyyar ADC domin tunkarar Bola Tinubu a 2027.
Legit ta tattauna da Muh'd Saidu
Wani matashi a jihar Gombe, Muhammad Sa'idu ya bayyana wa Legit cewa minista dan siyasa ne, saboda haka babu laifi ya fadi abin da zai gyara musu tafiyar siyasa.
Muhammad ya bayyana cewa:
"Zai iya cewa Tinubu ya kafu saboda yana da gwamnoni, amma ba lallai su jawo masa nasara ba.
"Amma idan za a yi amfani da kudi, a ruwan sanyi za iya samun hadin kan mutane."
An roki 'yan Arewa su zabi Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon hadimin shugaba Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya roki 'yan Arewa da su goyi bayan Bola Tinubu a 2027.
Ya bayyana cewa rashin samun wa'adi na biyu da Goodluck Jonathan ya yi a 2015 ya janyo matsaloli da dama a Najeriya.
Omokri ya yi gargadi da cewa rashin nasarar shugaba Bola Tinubu a 2027 za ta iya jawo karin samun masu neman ballewa daga Najeriya.
Asali: Legit.ng


