An Zo Wajen: Babban Jigo a APC Ya Fadi Abin da Zai Faru idan Tinubu Ya Sauya Shettima

An Zo Wajen: Babban Jigo a APC Ya Fadi Abin da Zai Faru idan Tinubu Ya Sauya Shettima

  • Ana ci gaba da maganganu kan batun shugaban kasa Bola Tinubu zai sauya Kashim Shettima daga matsayin mataimakinsa
  • Babban kusa a jam'iyyar APC, Saleh Zazzaga, ya tofa albarkacin bakinsa kan yiwuwar sauya Shettima kafin zaben shekarar 2027
  • Ya nuna cewa sauya Shettima ba zai kawo cikas ba ga tazarcen mai girma Bola Tinubu a zaben 2027

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban kungiyar APC North Central Forum, Saleh Zazzaga, ya yi magana kan yiwuwar Bola Tinubu ya sauya Kashim Shettima kafin zaben 2023.

Saleh Zazzaga ya bayyana cewa shugaban kasan ba zai yi rashin nasara ba saboda sauya Shettima a matsayin mataimakinsa.

Jigo a APC ya yi magana kan Tinubu da Shettima
Jigo a APC ya ce Tinubu zai ci zabe ko babu Shettima Hoto: @DOlusegun, @ShettimaSM
Source: Facebook

Jigon na jam'iyyar APC ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me zai faru idan Tinubu ya sauya Shettima?

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun fara kawo wa Shugaba Tinubu tangarɗa kan shirin canza Shettima a 2027

Saleh Zazzaga ya cika bakin cewa babu ficewar wani daga APC da za ta kawo cikas ga tazarcen Shugaba Tinubu.

“Babu wani mutum ko ƙungiyar mutane da za su fice daga jam’iyyar APC da hakan zai sa Shugaba Tinubu ya sha kaye a zaben 2027. Wannan ma ba zai faru ba domin yana da kyakkyawar alaka da Shettima da sauran jiga-jigan jam’iyyar."
"Mutanen ANPP kawai suna ƙoƙarin haddasa rashin jituwa tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa. Amma ko da hakan ta faru, Shugaban kasa zai ci gaba da jagoranci a zaben 2027."
"Muna da tabbacin cewa waɗanda suka kira taron manema labarai ba shugabanni ba ne na bangaren ANPP. Don haka ba za mu ɗauke su da muhimmanci ba."
"Bugu da ƙari, ko da shugaban kasa ya yanke shawarar sauya mataimakinsa, hakan zai kasance ne don maslahar jam’iyyar APC."
"Idan ka duba zaben da ya gabata, shugaban kasa kusan ya sha kaye a jihar Borno. Ya fadi a dukkan yankin Arewa maso Gabas. Don haka idan lissafi ya nuna cewa dole ne a canja mataimakin shugaban kasa, babu wani abu da zai faru.”

Kara karanta wannan

Shirin kayar da Tinubu ya kankama, an bayyana wanda zai iya gyara Najeriya a 2027

An nuna yatsa kan masu jita-jitar sauya Shettima

Jigon na APC ya bayyana cewa 'yan ANPP da ke tayar da jijiyar wuya kan sauya Shettima daukar nauyinsu ake yi.

Ana ta maganganu kan kujerar Kashim Shettima
Ana batun yiwuwar Tinubu ya sauya Shettima Hoto: Kashim Shettima
Source: Twitter
“Eh, daidai ne, kuma sun san masu daukarsu nauyi. Kawai suna son haifar da matsala ne a inda babu wata matsala."
"Saboda har yanzu babu wata sanarwa ta hukuma da ta nuna cewa Shugaba Tinubu zai sauya Shettima. Don haka masu tada jijiyoyin wuya su jira su gani. Idan Shugaban zai sauya Shettima, zai fitar da wata sanarwa da za ta gamsar da kowa."

- Saleh Zazzaga

Jam'iyyar ADC ta caccaki Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta yi suka kan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

ADC ta bayyana cewa ya kamata ya yi shugaban kasan ya maida hankali kan aikin da ke gabanshi maimakon sukar 'yan adawa.

Ta nuna cewa daga cikin matsalolin da ya kamata ya warware har da sabanin da ke tsakaninsa da mataimakinsa Kashim Shettima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng