El Rufai Ya Hango Babbar Matsalar da Za Ta Auku idan APC Ta Ci Gaba da Mulkin Najeriya
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bukaci 'yan Najeriya su tashi tsaye don kifar da gwamnatin jam'iyyar APC
- El-Rufai ya nuna cewa komawar APC kan mulkin Najeriya babbar barazana ce ga ci gaba da dorewar kasar nan
- Tsohon gwamnan ya bayyana cewa lokaci ya yi da 'yan Najeriya za su zo a hadu domin kifar da gwamnatin APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna, ya yi magana kan abin da zai faru idan jam'iyyar APC ta lashe zaben 2027.
El-Rufai ya bayyana cewa watakila ba za mu ƙara samun ƙasa ba dan jam’iyyar APC ta yi nasara a zaɓen 2027.

Asali: Facebook
El-Rufai ya faɗi haka ne a ranar Asabar a jihar Sokoto yayin wani gagarumin gangamin wayar da kan jama'a domin goyon bayan hadakar 'yan adawa ta jam'iyyar ADC, cewar rahoton TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan na Kaduna ya ce ya shiga hadakar ne domin tabbatar da cewa APC ta fice daga mulki.
El-Rufai ya shirya ganin bayan APC
Nasir El-Rufai, wanda tsohon jigo ne a jam’iyyar APC, ya bayyana cewa ya shirya tsaf don haɗa kan 'yan Najeriya domin kawar da “gurbatacciyar” jam’iyyar da ke kan mulki.
"Ni ba don na amfana da wani abu na kaina na shiga siyasa ba. Na shiga siyasa ne domin hidimtawa."
"Idan gwamnati ta kasa yi wa al’umma aiki, to a matsayin ɗan ƙasa nagari, ya zama wajibi a gareni na fito fili in soki wannan gwamnati tare da ɗaukar matakin gyara lamarin."
"Shi ya sa muka haɗu da sauran waɗanda ba sa goyon bayan manufofin wannan gwamnati domin ƙirƙirar haɗaka, wanda daga bisani ta haifar da rungumar jam’iyyar ADC."
"Muna nan a Sokoto domin fara shirin wayar da kan 'yan Najeriya su tashi tsaye su fuskanci gwamnatin APC a kowane mataki, ciki har da gwamnatin tarayya a Abuja."
"Ina da yakini cewa idan muka ƙyale wannan jam’iyya da gwamnatin nan su ci gaba da mulki na wa’adi na biyu, ragowar alakar zamantakewar ‘yan Najeriya da sauran ginshikan ƙasa za su lalace baki ɗaya."
"Kuma watakila ma ba za mu samu abin da za mu kira da sunan ƙasa ba. Wannan gwagwarmaya ce ta ceton rayuwarmu."
- Nasir El-Rufai

Asali: Twitter
El-Rufai na daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar APC, amma a watan Maris na shekarar 2025, ya fice daga jam’iyyar mai mulki ya koma jam’iyyar SDP.
An tura mutanen El-Rufai gidan kaso
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata kotu a jihar Nasarawa ta tura wasu magoya bayan Nasir El-Rufai zuwa gidan kaso.
Kotun ta tsare mutanen ne sakamakon rikicin sbugabanci da ya dabaibaye jam'iyyar SDP a jihar Nasarawa.
Kotun dai ta umarci a sakaya mata mutanen ne har zuwa lokacin da za ta ci gaba da sauraron karar da aka shigar a gabanta.
Asali: Legit.ng