'Dalilin da Ya Sa Ya Kamata Ƴan Arewa Su Marawa Tinubu Baya Gaba Ɗaya a 2027'

'Dalilin da Ya Sa Ya Kamata Ƴan Arewa Su Marawa Tinubu Baya Gaba Ɗaya a 2027'

  • Shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, Femi Gbajabiamila ya bukaci shugabannin Arewa su mara wa Bola Tinubu baya
  • Gbajabiamila ya bayyana irin kokari da Tinubu ke yi na hada kan Najeriya inda ya ce ya cancanci goyon bayan
  • Hakan ya biyo bayan samun goyon baya da Tinubu ke kara samu a jihohi da dama da ke Arewacin Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ya rokawa Bola Tinubu alfarma kan zaben 2027.

Gbajabiamila ya bukaci shugabannin Arewa su marawa Bola Tinubu baya a zaben 2027 mai zuwa.

An rokawa Tinubu alfarma a Arewa kan zaben 2027
An roki a sake ba Tinubu dama a 2027 daga Arewa. Hoto: Aso Rock Villa.
Source: Twitter

Tinubu: Gbajabiamila ya roki yan Arewa a 2027

Da yake jawabi a taron kungiyar tsofaffin ‘yan majalisa daga Arewa, Gbajabiamila ya ce Tinubu ya cancanci goyon bayan duka yankuna, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

2027: Kungiyar ATT ta samo mafita ga Arewa kan tazarcen Shugaba Tinubu

Ya bayyana Tinubu a matsayin shugaba mai tarihi da kishin kasa, yana mai cewa ci gaban Najeriya ya dogara da hadin kai da daidaiton mulki.

Gbajabiamila ya bukaci shugabannin Arewa da su kara karfafa goyon bayan gwamnatin Tinubu da burinsa na sake tsayawa takara a 2027.

Ya ce Tinubu ba na Kudu kadai ba ne, shugaba ne na kasa baki daya, inda Arewa ke cin gajiyar gyare-gyaren gwamnati da ayyukan ci gaba.

Gbajabiamila ya jaddada cewa ayyukan hanya, jiragen kasa da farfado da noma a Arewa suna tabbatar da adalcin gwamnatin Tinubu a kasa.

Ya ce:

“Muna gina tubalin cigaba ne a yau, kuma ya dace a bar shugaban kasa ya kammala abin da ya fara.”
An bayyana irin kokarin Tinubu a Arewa da Kudancin Najeriya
Gbajabiamila ya roki alfarmar yan Arewa kan zaben Tinubu a 2027. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Tsofaffin yan majalisa sun gana da Gbajabiamila

Shugaban kungiyar tsofaffin ‘yan majalisa, Hon. Nnanna Igbokwe, ya yaba wa matsayar da Kungiyar Arewa ta dauka a matsayin abin alfahari da kishin kasa.

Kara karanta wannan

Sunan Kwankwaso ya fito: Malami ya samu wahayin wanda zai yi wa Madugu mataimaki

Igbokwe ya ce wannan mataki na nuna kishin kasa ne, yana mai cewa ya kamata sauran yankuna su bi wannan misali na hadin kai da daidaiton mulki.

A cikin wata sanarwa bayan taron, kungiyar ta amince da shugabancin Kudu da kudurin Tinubu na tsayawa takara a wa’adi na biyu, Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta samu sa hannun Hon. Rufai Chanchangi da Hon. Atiwurcha, masu rike da mukamai a kungiyar.

Kungiyar ta ce tana maraba da komai da ke kara hadin kai da zaman lafiya a Najeriya, ciki har da tsarin jujjuyawar mulki tsakanin Arewa da Kudu.

Ta ce:

“Muna ganin cewar yana da amfani ga Arewa idan aka bar shugaban da ke kan mulki daga Kudu ya kammala wa’adinsa.”

Taron na 2025 Dialogue Session ya kasance wani bangare na tattaunawar kasa da kungiyar ke yi domin tabbatar da tsarin mulki mai cike da hadin kai.

Kungiyar ta kuma bukaci gwamnati ta kara himma wajen shawo kan matsalolin tsaro musamman a jihohin Zamfara, Katsina, Filato, Binuwai da Neja.

Gwamna, APC sun goyi bayan Tinubu a Niger

Kara karanta wannan

'A taimaka masa kamar Buhari': An roƙawa Tinubu alfarma wurin ƴan Arewa a 2027

Mun ba ku labarin cewa Gwamna Mohammed Umar Bago na Jihar Niger ya sha rawa a taron da aka yi a Minna yana murna da wakar yabo ga Bola Tinubu.

Jam’iyyar APC ta jihar ta ayyana Bola Tinubu a matsayin ɗan takararta kaɗai a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

'Yan Najeriya sun bayyana damuwa, suna cewa gwamnoni sun fi mayar da hankali kan siyasa fiye da matsalolin rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.