"Kwankwaso Zai Iya Komawa APC", Shugaban NNPP Ya Fadi Dalili

"Kwankwaso Zai Iya Komawa APC", Shugaban NNPP Ya Fadi Dalili

  • Ana ci gaba da batun yiwuwar komawar madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso zuwa jam'iyyar APC
  • Shugaban tsagin jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano, ya bayyana cewa akwai yiwuwar Kwankwaso ya koma ya hade da Tinubu
  • Jibril Doguwa ya nuna cewa su dai za su ci gaba da zama a NNPP ko da akwai Kwankwaso da 'yan Kwankwasiyya ko babu su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Shugaban tsagin jam'iyyar NNPP a jihar Kano, Jibril Doguwa, ya yi magana kan batun komawar Rabiu Musa Kwankwaso jam'iyyar APC.

Jibril Doguwa ya bayyana yiwuwar cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, zai iya komawa jam’iyyar APC.

Ana yada jita-jita kan yiwuwar komawar Kwankwaso APC
Shugaban NNPP ya ce Kwankwaso na iya komawa APC Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Shugaban na jam'iyyar NNPP ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akwai yiwuwar komawar Kwankwaso APC

Kara karanta wannan

An zo gaɓar ƙarshe kan batun sauya sheƙar Kwankwaso daga NNPP zuwa APC

Jibril Doguwa ya ce ziyarar da wani jigo a Kwankwasiyya, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya kai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa, na iya zama alamar sabuwar daidaituwar siyasa da ke tafe.

"Akwai yiwuwar Kwankwaso yana son komawa APC. Babu wani mamba na Kwankwasiyya da zai gana da Tinubu ba tare da sani ko amincewar Kwankwaso ba."

- Jibril Doguwa

Jibril Doguwa ya rage muhimmancin sukar da Kwankwaso ya yi wa Shugaba Tinubu kwanan nan, yana mai cewa haɗin gwiwa a siyasar Najeriya na yawan sauyawa.

"Yin suka ga Tinubu ba yana nufin Kwankwaso ba zai iya yin aiki da shi ba. A siyasa, ba a dawwama da abokan gaba, sai dai bukatu na dindindin. Wataƙila kawai yana ƙoƙarin tunatar da shugaban ƙasa nauyin da ke kansa a matsayin shugaba ne."

- Jibril Doguwa

NNPP za ta ci gaba da zama ko ba Kwankwaso

Kara karanta wannan

Jibrin Kofa: NNPP ta yi magana bayan dan Kwankwasiyya ya gana da Tinubu

Shugaban na NNPP ya ƙara da cewa jam’iyyar har yanzu na ɗaukar mambobin Kwankwasiyya a matsayin ’ya’yanta, amma ya jaddada cewa NNPP za ta ci gaba da rayuwa ko da ba tare da Kwankwaso ba.

Kwankwaso na tsaka mai wuya kan komawa APC
Ana ta magana kan yiwuwar komawar Kwankwaso APC Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Ya ƙi amincewa da cewa akwai rikice-rikice a cikin jam’iyyar, yana mai cewa sauyin sheƙa ruwan dare ne a siyasar Najeriya.

"Muna ci gaba da ɗaukar mambobin Kwankwasiyya a matsayin mambobin NNPP. Amma za mu ci gaba da zama a NNPP ko da da Kwankwaso ko babu shi."
"Babu wani babban ɗan siyasa mai suna a Najeriya da bai taɓa sauya jam’iyya ba."

- Jibril Doguwa

Maganganun Doguwa sun zo ne a daidai lokacin da ake ƙara yawan hasashen yiwuwar haɗin gwiwa tsakanin Kwankwaso da Tinubu kafin zaɓen 2027, lamarin da ya tayar da hankulan wasu mambobin NNPP a Kano.

Fasto ya yi hasashen mataimakin Kwankwaso

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani sanannen fasto, Francis Udo, ya yi hasashe kan siyasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Sunan Kwankwaso ya fito: Malami ya samu wahayin wanda zai yi wa Madugu mataimaki

Fasto Francis Udo ya yi hasashen cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso zai gaji Shugaba Bola Tinubu a 2031.

Malamin addinin ya bayyana cewa Allah ya nuna masa.Godswill Akpabio a matsayin wanda zai yiwa Kwankwaso mataimaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng