Gwamna Ya Rikita Jiga Jigan APC a Taro, Ya Taka Rawa a Waƙar 'Omologo' Ta Rarara

Gwamna Ya Rikita Jiga Jigan APC a Taro, Ya Taka Rawa a Waƙar 'Omologo' Ta Rarara

  • Gwamna Mohammed Umar Bago na Jihar Niger ya sha rawa a taron da aka yi a Minna yana murna da wakar yabo ga Bola Tinubu
  • Jam’iyyar APC ta jihar ta ayyana Bola Tinubu a matsayin ɗan takararta kaɗai a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
  • 'Yan Najeriya sun bayyana damuwa, suna cewa gwamnoni sun fi mayar da hankali kan siyasa fiye da matsalolin rayuwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Minna, Niger - An yi ta ce-ce-ku-ce kan goyon bayan Bola Tinubu da aka yi a jihar Niger da ke Arewacin Najeriya.

Jiga-jigan jam'iyyar APC sun amince da shugaban ƙasa Bola Tinubu a matsayin ɗan takararsu kaɗai a jihar.

Bago ya taka rawa yayin amincewa da takarar Tinubu
Gwamna ya taka rawa a waƙar 'Omologo' ta Rarara saboda Tinubu. Hoto: @Chiefpressngs.
Source: Twitter

Gwamna ya taka rawa a taron goyon bayan Tinubu

Matashi mai amfani da kafofin sadarwa, @Imranmuhdz ya wallafa bidiyon Gwamna Mohammed Umar Bago yana taka rawa a taron a X.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya taɓo mutanen Ganduje, ya maye gurbin Gawuna a Jami'ar BUK

A wurin taron da aka gudanar a Minna, babban birnin jihar Niger, an gano Gwamna Bago yana rawa da wakar mawaki Dauda Kahutu Rarara.

Rarara ya rera wakar ne saboda yabon Tinubu wanda ta ke yin tashe a 'yan kwanakin nan.

Wakar da ake wa lakabi da 'Omologo' ta karade kafofin sadarwa inda ake amfani da ita har a wuraren biki.

Wakar ta “Omologo” da mawakin Hausan ya rerawa Tinubu don neman wa’adi na biyu ta jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta.

Taron na APC da Tinubu an yi shi a ranar Juma’a, 1 ga watan Agusta, inda aka nuna goyon baya ga sake tsayawar shugaban takara.

A wurin taron, gwamnan da mambobin APC na jihar sun bayyana cewa Bola Tinubu ne ɗan takara kaɗai a zaɓen 2027 mai zuwa.

Gwamna ya yi rawar 'Omologo' a taron goyon bayan Tinubu
Gwamna ya sheka rawa a taron APC da goyon bayan Tinubu. Hoto: Mohammed Umaru Bago.
Source: Twitter

Tinubu: Martanin 'yan Najeriya kan rawar Bago

Wasu ‘yan Najeriya sun bayyana ra’ayoyinsu a sashin sharhi kan yadda Gwamna Bago ya yi rawa yana nuna goyon baya ga Tinubu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya amince da kashe sama da N712bn a yi wa filin jirgin Legas kwaskwarima

Sani Suleman Isah ya ce:

"Gwamnonin Arewa suna ba da tabbacin cewa za su zabi Tinubu, amma ba sa faɗa masa gaskiya."

Mazi Damola Williams ya ce:

"Shugaban kasa ya yi hankali, ka da ya bar kansa ga rawar da ake yi. Arewa na da karfin iko."

Aliyu Lemu ya soki gwamnan:

“Bago na rawa a yayin da hanyoyin Neja suka lalace da rashin wutar lantarki, Wannan ba shugabanci ba ne.”

Sir Tee ya koka:

“Kuna jin kunya kuwa? Har yanzu muna 2025, amma ku kuna maganar zaɓen 2027, Abin takaici ne matuƙa.”

Da McCoy ya ce:

“Kun cire tallafin fetur, kun ba gwamnoni kuɗi sun ci, me zai hana su raira wakar yabon ku da rawa?”

Adedejisam ya rubuta:

“O ti tan! An gama kawai 2027 zuwa 2031 ta tabbata.”

Gwamna Bago ya kai gwamnatin Tinubu kotu

Mun ba ku labarin cewa gwamnatin jihar Niger karkashin jagorancin Gwamna Umar Bago ta shigar da gwamnatin tarayya kara a gaban kotu.

Kara karanta wannan

ADC: El Rufai da manyan ƴan siyasar Kaduna da suka fice daga PDP, APC, suka shiga haɗaka

Bago ya shigar da karar ne kan kin sanya jihar cikin jerin jihohin da ke samun kaso 13% na daga abin da aka samu daga albarkatun da suke samarwa.

Gwamnatin ta bukaci kotun da ta umarci a sanya ta cikin jerin, duba da irin dumbim albarkatun da take samarwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.