Ana Wata ga Wata: Jam'iyyar ADC Ta Dakatar da Ɗan Majalisar Tarayya Mai Ci a Kogi

Ana Wata ga Wata: Jam'iyyar ADC Ta Dakatar da Ɗan Majalisar Tarayya Mai Ci a Kogi

  • Jam’iyyar ADC ta dakatar da dan majalisar wakilai, Hon. Leke Abejide saboda zargin raina shugabannin jam’iyya a jihar Kogi
  • An ce Abejide ya shirya taro da wasu ‘yan ADC a Abuja ba tare da sahalewar shugabannin ADC ba, lamarin da ya tayar da kura sosai
  • Jam’iyyar ta kuma zargi Hon. Abejide da yunkurin jan shugabannin ADC zuwa hadaka da APC, wanda ya sabawa muradun ADC

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kogi – ADC reshen jihar Kogi ta sanar da dakatar da dan majalisar tarayya, Hon. Leke Abejide daga jam'iyyar na har abada.

Hon. Leke Abejide yana wakilatar mazabar Yagba ta Gabas da Yamma da Mopamuro, a majalisar wakilai ta tarayya.

ADC ta dakatar da dan majaisar wakilai a Kogi kan zargin zangon kasa da rana shugabannin jam'iyyar
Hon. Leke Abejide, dan majalisar wakilai daga jihar Kogi da jam'iyyar ADC ta dakatar. Hoto: Abraham Ibukun
Source: Facebook

ADC ta dakatar da dan majalisar wakilai

Bayani kan dakatar da dan majalisar wakilan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren ADC na jihar Kogi, Adaji John, ya fitar a ranar Juma’a a Lokoja, inji rahoton TVC News.

Kara karanta wannan

2027: Dino Melaye da wasu na hannun daman Atiku 2 da suka fice daga PDP zuwa ADC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ADC ta zargi Hon. Leke Abejide da “matsanancin rashin ladabi” da kuma “yin ayyuka na adawa da jam’iyya."

Baya ga wannan dakatarwar, ADC ta yi barazanar cewa za ta iya korar dan majalisar wakilan gaba daya idan ya ci gaba da raina shugabannin jam’iyyar.

“Jam’iyyar ADC reshen jihar Kogi ta dakatar da ɗaya daga cikin wakilanmu a majalisar tarayya. Wanda abin ya shafa shi ne Hon. Leke Abejide, wanda ke wakiltar mazabar Yagba ta Gabas da Yamma da Mopamuro,” inji sanarwar.

"Abejide ya raina shugabannin ADC" - Adaji John

Adaji John ya bayyana cewa dakatarwar na da nasaba da wani taron sirri da Hon. Abejide ya gudanar da wasu ‘yan jam’iyya a Abuja ba tare da sanin ko amincewar shugabannin ADC a jihar ba.

Arise News ta rahoto sanarwar Adaji John ta yi karin bayani da cewa:

“Domin karin haske, an dakatar da Hon. Abejide ne bayan an tabbatar da laifin rashin biyayya ga shugabanni da kuma yunƙurin kwace ikon shugaban jam’iyya da sakatare na jiha.

Kara karanta wannan

'PDP ta shiga wani hali,' Sanata Dino Melaye ya yi bankwana da jam'iyyar adawa

"Dakatarwar na da alaƙa da kalaman raini da ya yi wa shugabannin jam’iyyar a wani taro da aka gudanar a Abuja."

Jam’iyyar ta ƙara zargin cewa ɗan majalisar ya nemi jan ra'ayin shugabannin ADC a matakin ƙananan hukumomi da mazabu domin su mara wa APC mai mulki baya, wanda hakan ya ci karo da manufar ADC.

Ana zargin dan majalisa wakilai, Leke Abejide da yunkurin jan ra'ayin shugabannin ADC zuwa hadaka da APC a Kogi
Hon. Leke Abejide yana wakilatar mazabar Yagba ta Gabas da Yamma da Mopamuro, a majalisar wakilai. Hoto: @lekeabejide23
Source: Twitter

Ana zargin dan majalisar da aiki da APC

Sanarwar ta ce:

“Hon. Abejide ya zarce gona da iri lokacin da ya yi yunƙurin jan ra'ayin shugabannin jam’iyya a mazabu da ƙananan hukumomi zuwa wani taro da nufin hada hannu da APC a maimakon ADC.”

John ya ƙara bayyana cewa taron da Abejide ya kira a Abuja ya saba da kundin tsarin mulkin jam’iyya:

“Mun samu tabbacin cewa ya kira wani taro da shugabanninmu a mazabu da ƙananan hukumomi, wanda hakan ya saba da dokokin jam’iyya da ke ba shugaban jam’iyya da sakatare kawai damar kiran irin wannan taro.”

A ƙarshe, John ya buƙaci Hon. Abejide da ya daina kalaman batanci ga shugabannin jam’iyya, tare da daina duk wata mu’amala da jam’iyyar APC nan take.

Kara karanta wannan

ADC ta raba gardama kan batun kafa hadaka don cika burin Atiku Abubakar

"Ni ke daukar nauyin ADC" - Leke Abejide

A wani labarin, mun ruwaito cewa, dan majalisar wakila ɗaya tilo na jam'iyyar ADC, Hon. Leke Abejide ya ce haɗakar ƴan adawa a jam'iyyarsa ba za ta kai ga nasara ba.

Hon. Abejide ya yi ikirarin cewa shi ne mai ɗaukar nauyin ADC, kuma zai iya sauya sheƙa zuwa APC a duk lokacin da ya ga dama saboda yana da ƴancin haka.

Dan majalisar ya bayyana shakku kan ƙawancen 'yan adawa, inda ya ce bai ga alamar nasara a tattare da ƴan PDP, LP da ma jam’iyyar APC da suka koma ADC ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com