Bayan Barin PDP, Dino Melaye Ya Fadi Makircin da APC Ke Kullawa Jam'iyyar

Bayan Barin PDP, Dino Melaye Ya Fadi Makircin da APC Ke Kullawa Jam'iyyar

  • Tsohon sanatan Kogi ta Yamma, Sanata Dino Melaye ya yi kalamai masu tsauro kan tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP
  • Dino Melaye ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ta zama wani reshe na APC mai mulki kuma ba ta da karfin yin adawa a halin yanzu
  • Tsohon sanatan ya yi zargin cewa mafi yawa daga cikin gwamnonin PDP ba su shirya yin adawa ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya yi kalamai masu kaushi kan jam'iyyar PDP.

Tsohon sanatan mai wakiltar Kogi ta Yamma, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta fada hannun jam’iyyar APC, kuma ba za ta ƙara zama ingantacciyar jam’iyyar adawa ba.

Dino Melaye ya yi kalamai kan PDP
Dino Melaye ya yi kalamai masu kaushi kan PDP Hoto: @OfficialSDM
Asali: Facebook

Tsohon ɗan takarar gwamna na jihar Kogi ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wata hira da aka yi da shi a shirin 'Politics Today' na tashar Channels Tv.

Kara karanta wannan

'Ta zama fanko,' NNPP ta dura kan PDP da ta soki mulkin Abba a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dino Melaye, wanda kwanan nan ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC, ya zargi APC da ƙulla makirci na rushewar PDP.

Me Dino Melaye ya ce kan PDP?

"APC ta saye PDP. PDP ta koma reshe ne na APC. PDP yanzu wani sashe ne na APC. A ma’aunin gaskiya, daga Aso Rock Villa ake gaya musu ranakun da za su yi tarurrukan NEC da NWC."
"Ka kalli adadin gwamnonin PDP a yau. Wadannan gwamnoni suna kama da ‘yan adawa kuwa? Shin suna taka rawar ‘yan adawa? Wadanda suka rage a PDP, a zahiri, suna aiki ne don APC."

- Dino Melaye

Meyasa Dino Melaye ya fice daga APC?

Dino Melaye ya bayyana cewa ya bar PDP ne saboda rashin ƙarfinta na yin hamayya da jam’iyyar APC mai mulki.

"Bisa girmamawa ga kawuna, Babangida Aliyu. Ka ji shi kwana biyu da suka wuce; Ya ce idan mun iya jure mulkin Buhari na tsawon shekaru takwas, to mu kara jure wa Tinubu na tsawon wasu shekara huɗu."

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka jawo Nasir El Rufai ya kasa zama a jam'iyyar SDP

"Shin wannan magana ya kamata ta fito daga bakin ɗan adawa? Abin da nake ƙoƙarin faɗi shi ne, muna rayuwa a wani mawuyacin lokaci mai haɗari."

- Dino Melaye

Dino Melaye ya yi raga-raga da PDP
Dino Melaye ya ce PDP ta mutu Hoto: Senator Dino Melaye
Asali: Facebook

Karanta wasu labaran kan Dino Melaye

PDP ta dakatar da Dino Melaye

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar adawa ta PDP ta dakatar da dan takararta na gwamnan jihar Kogi, Sanata Dino Melaye.

Jam'iyyar PDP a jihar Kogi ta dakatar da Sanata Dino Melaye ne bisa zargin aikata wasu laifuffuka da suka hada da cin mutuncinta.

Dakatarwar da aka yi wa tsohon sanatan kogi ta Yamma na zuwa ne bayan da kwamitin da aka kafa don binciken zarge-zargen da ake masa, ya gayyace shi amma ya ki zuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng