Gwamna Ya Shirya Zama na Farko da Zai Shiga Jam'iyyar Haɗaka, ADC? An Samu Bayanai
- Bayan ayyana cikakken goyon bayansa ga tazarcen Shugaba Tinubu, an fara yaɗa labarin cewa Gwamna Adeleke zai koma ADC
- Jita-jitar ta nuna cewa Gamna Adeleke ya gama shirin shiga jam'iyyar haɗaka watau ADC ko haɗa kai da jiga-jiganta kafin zaɓen Osun 2026
- Amma a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Olawale Rasheed ya fitar, ya ce waɗannan rahotanni ba gaskiya ba ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Osun - Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya karyata rahotannin da ke cewa yana shirin komawa jam’iyyar haɗakar ƴan adawa watau ADC.
Gwmanan, wanda a baya aka yi raɗe-raɗin cewa zai koma APC, ya ce ko kaɗan bai taɓa tunanin shiga ADC ko kuma haɗa kai da wasu jiga-jigan jam’iyyar haɗakar ba.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai, Olawale Rasheed, ya fitar a ranar Juma’a,
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ademola Adeleke ya bayyana irin waɗannan jita-jita a matsayin marasa tushe, yana mai jaddada cewa yana nan daram a cikin babbar jam'iyyar adawa PDP.
Ya ƙara da cewa ba ya da wani shiri na shiga ko yin haɗin gwiwa da ADC kafin zaɓen gwamna jihar Osun wanda za a yi a shekarar 2026.
Gwamna Adeleke ya shirya shiga jam'iyyar ADC?
Sanarwar ta ce:
“Mun lura da rahotannin da ke yawo a kafafen yaɗa labarai dangane da zargin cewa Gwamna Adeleke zai koma ADC ko zai haɗa kai da wasu jiga-jigan jam’iyyar kafin zaɓen gwamna na 2026. Wannan ba gaskiya ba ne kwata-kwata.”
“Na farko, mu a PDP ta Osun mun riga mun amince da kuma goyon bayan tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027, don haka babu wani haɗin gwiwa da ADC.
“Na biyu, Gwamna Adeleke ba shi da niyyar haɗaka da kowa a cikin jam’iyyar ADC. Yana nan a PDP, zai tsaya takara a PDP, kuma ba ya buƙatar haɗin gwiwa da ADC domin samun nasara a 2026.”

Source: Twitter
Mutanen Osun na goyon bayan Adeleke
Kakakin gwamnan ya ƙara da cewa mutanen jihar Osun suna tare da Gwamna Adeleke saboda ayyukan alherin da ya zuba masu tun daga lokacin da ya karɓi mulki, rahoton The Cable.
Don haka, gwamnan ya bukaci mambobin PDP a jihar da su ci gaba da ƙarfafa tsarin jam’iyya a dukkan matakai domin samun gagarumar nasara a shekara mai zuwa.
ADC ta fara hango kujerar gwamnan Osun
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta bayyana matukar Gwamna Adeleke ya bar PDP, to za ta lashe zaɓen gwamnan jihar Osun cikin sauƙi a 2026.
ADC ta ce 'yan PDP masu yawa sun riga sun shiga jam'iyyarta, wasu kuma na shirin shiga saboda rashin jin daɗin yunkurin Adeleke.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jam'uyyar haɗakar ke ƙoƙarin ƙara karfi da kuma ƙafa gwamnati a jihohi da tarayya a zaɓuka masu zuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

