Da Gaske El Rufai Ya Shiga Coci Neman Yardar Fastoci kan Tinubu? Gaskiya Ta Fito
- An yi ta yada wasu hotuna sun nuna Malam Nasir El-Rufai a coci, inda aka ce yana kokarin jawo limamai don zaben 2027
- El-Rufai ya halarci jana’izar tsohon kwamishinan Anambra, Mathias Anohu ne, ba wai ya je neman goyon bayan Fastoci ba
- An tabbatar da cewa hoton daga jana’iza ne da aka gudanar a Okija, kuma El-Rufai ya wallafa hakan da kansa a kafar sadarwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Wasu masu amfani da kafofin sadarwa sun wallafa hotunan ɗan siyasar Najeriya, Nasir El-Rufai a cikin coci.
Rahotannin sun nuna cewa El-Rufai ya shiga cocin ne domin kokarin jawo Fastoci game da zaɓen 2027.

Source: Twitter
Menene ya kai El-Rufai cikin coci?
Sai dai binciken kwa-kwaf na Africa Check ya tabbatar da cewa hakan ba gaskiya ba ne ya halarci jana'iza ne a Anambra.

Kara karanta wannan
Masana'antar fina finan Najeriya ta yi rashi, matashiyar jaruma ta riga mu gidan gaskiya
Wasu daga cikin sakonnin da ake ta yaɗawa suka ce:
“Labari da duminsa. El-Rufai ya halarci coci yau domin fara tattara Fastoci da Rabaran don 2027 saboda kayar da Bola Tinubu.”
A matsayin hujja, sakon ya haɗa da hotunan El-Rufai a wani wuri da ya kama da coci wanda aka yi ta yada rahotanni kala-kala game da inda aka gano shi.

Source: UGC
Yadda El-Rufai ke sukar gwamnatin Tinubu
Nasir El-Rufai ya kasance gwamnan jihar Kaduna daga 2015 zuwa 2023 a matsayin ɗan jam’iyyar APC kafin komawa SDP.
Kafin ficewarsa daga APC, El-Rufai ya soki gwamnatin Tinubu bayan majalisar dattijai ta ƙi tabbatar da shi a matsayin minista.
Daga cikin masu yada hotunan suna zargin El-Rufai yana neman goyon bayan Fastoci domin zaben 2027 saboda hana shi mukamin minista.
Binciken da aka yi kan dalilin shigan El-Rufai coci
An gudanar da binciken hoto ta hanyar 'Google reverse image search', wanda ya kai ga asalin rubutun da El-Rufai ya yi a shafinsa.
A cewar rubutun da El-Rufai ya wallafa a shafin X a ranar 1 ga Mayu 2025, hotunan sun fito ne daga jana’izar Mathias Anohu, tsohon kwamishina a Anambra.
El-Rufai ya rubuta:
“Mun halarci jana’izar Cif Mathias Chidi Anohu da safe a Okija, a jihar Anambra Allah ya jikansa.”
Duk da cewa hoton ya nuna El-Rufai a coci, babu wata hujja da ke nuna yana neman taimakon Fastoci ne game da zaben 2027 saboda rashin jituwa da ke tsakaninsa da Tinubu.
An ƙaryata rahoton cewa Iran ta gargadi Tinubu
Mun ba ku labarin cewa an yi ta yada wani faifan bidiyo da ke nuna shugaban Iran yana gargaɗin Najeriya ka da ta tsoma baki a rikicin kasar da Isra’ila.
An tabbatar da cewa Ebrahim Raisi da aka nuna a bidiyon ya rasu tun a Mayun 2024, kafin rikicin ya fara cikin Yuni 2025.
Babu wata sanarwa daga shugaba Masoud Pezeshkian ko hukumomin Iran da ke nuna sun yi barazana ga Bola Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
