Abubuwan da Suka Jawo Nasir El Rufai Ya Kasa Zama a Jam'iyyar SDP

Abubuwan da Suka Jawo Nasir El Rufai Ya Kasa Zama a Jam'iyyar SDP

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai na ci gaba da zama a jam'iyyarsa ta SDP yayin da ake tunkarar zaben shekarar 2027.

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Nasir El-Rufai dai ya sauya sheka zuwa SDP ne bayan ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Nasir El-Rufai na ci gaba da zama a SDP
El-Rufai na fuskantar matsaloli a SDP Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Ana ganin cewa komawar El-Rufai zuwa jam'iyyar SDP na da nasaba da shirin tunkarar zaben shekarar 2027.

Meyasa El-Rufai ya fice daga APC zuwa SDP?

A ranar Litinin, 10 ga watan Maris 2025, Nasir El-Rufai ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna, ya bayyana cewa ya fice daga APC ne saboda rashin gamsuwa da inda akalar jam'iyyar ta nufa.

El-Rufai ya bayyana cewa ya dauki matakin barin APC ne bayan ya mika korafi a sirrance da kuma a bayyane kan yadda ake tafiyar da jam'iyyar ga mahukunta, amma aka yi biris da shi.

Kara karanta wannan

Bayan barin PDP, Dino Melaye ya fadi makircin da APC ke kullawa jam'iyyar

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya sanar da cewa ya koma jam'iyyar SDP bayan ya raba gari da SDP.

A wancan lokacin, ya yi kira ga sauran 'yan adawa da su zo a hadu waje daya don samar da jam'iyyar da za ta iya kifar da APC daga kan madafun iko.

Ya abubuwa suka kasance da El-Rufai a SDP?

Nasir El-Rufai ya samu tarba sosai bayan ya shiga jam'iyyar SDP daga manyan jiga-jigan da suke cikinta.

Shigarsa cikin jam'iyyar ta sanya dumbin magoya bayansa yin tururuwa zuwa cikinta domin yin rajista.

Sai dai, jim kadan bayan shigarsa SDP, sai rikice-rikicen cikin gida suka fara ballewa inda aka samu bangarori guda biyu a jam'iyyar.

Meyasa El-Rufai ke tsilla-tsilla a SDP?

Wasu na hasashen cewa abubuwa ba su tafi daidai ba El-Rufai bayan ya koma jam'iyyar SDP.

Bayan komawarsa SDP tarin matsaloli sun rika bullowa wadanda har suka kai ga dakatar da shugaban jam'iyyar na kasa daga kan mukaminsa.

Sai dai, daga baya shugaban na SDP ya fito ya yi watsi da dakatarwar da aka yi masa.

Kara karanta wannan

2027: Dino Melaye da wasu na hannun daman Atiku 2 da suka fice daga PDP zuwa ADC

Abubuwan da suke kawo cikas ga zaman El-Rufai

Akwai wasu abubuwa da ake ganin sun zama dalilan da suka sanya El-Rufai ke shan wuya wajen zama a SDP.

A lokacin da El-Rufai ya koma SDP, an yi zaton cewa zai jijjiga jam'iyyar ta zama babban wajen nuna adawa da kalubalantar jam'iyyar APC.

1. Kirkirar rikicin cikin gida

Ana zargin cewa akwai sa hannun El-Rufai kan rikicin cikin gida da ya balle a jam'iyyar SDP bayan ya koma cikinta.

Ana zargin cewa akwai hannunsa a cikin rikicin ne domin ya samu damar karbe ikon jam'iyyar.

Wannan rikicin ne dai ya kai ga dakatar da shugaban jam'iyyar na kasa, Alhaji Shehu Gabam daga kan mukaminsa.

Sai dai, shugaban na SDP ya fito ya yi watsi da dakatarwar da aka yi masa, cewar rahoton jaridar The Punch.

A bayanin da ya yi, ya nuna yatsa ga wasu 'yan siyasa da ke cikin hadakar 'yan adawa da kokarin kitsa rikici a SDP.

Kara karanta wannan

'PDP ta shiga wani hali,' Sanata Dino Melaye ya yi bankwana da jam'iyyar adawa

Ya bayyana cewa wadannan 'yan siyasan suna kokarin kwace ikon SDP ne ta kowane hali.

2. Kafa daya a ADC, daya a SDP

Duk da cewa yana cikin jam'iyyar SDP, El-Rufai ya kasance daya daga cikin jagororin da ke cikin hadakar 'yan adawa.

El-Rufai ya shiga gaba wajen kafa hadaka wacce daga karshe ta zabi jam'iyyar ADC a matsayin dandalin da za su yi amfani da shi.

Sai dai, har yanzu tsohon gwamnan na Kaduna bai koma cikin jam'iyyar ADC a hukumance ba.

A yayin wata hira da aka yi da shi da tashar Channels tv, sakataren yada labarai na kasa na ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa an ba El-Rufai dama ya ci gaba da zama a SDP.

Ya ce an an ba shi damar ya kammala wasu abubuwa da yake yi a jam'iyyar kafin ya shigo ADC.

An dakatar da El-Rufai daga SDP
El-Rufai na cikin hadakar 'yan adawa duk da yana SDP Hoto: @elrufai
Source: Twitter

3. Matsalar dakatarwa daga SDP

Zaman El-Rufai a SDP ya shiga matsala biyo bayan dakatarwar da aka yi masa daga jam'iyyar.

Jam'iyyar SDP dai ta dakatar da tsohon gwamnan na jihar Kaduna har na tsawon shekara 30.

Kara karanta wannan

Sabon shugaban APC ya kada hantar 'yan adawa, ya sha alwashi kan zaben 2027

An dakatar da shi ne bisa zargin cewa bai yi rajista da jam'iyyar ba kuma yana bayyana kansa a matsayin mamba.

Fadar shugaban kasa ta yi wa El-Rufai shagube

A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta yi wa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai shagube.

Fadar shugaban kasan ta yi masa shaguben ne bayan da aka dakatar da shi daga jam'iyyar SDP har na tsawon shekara 30.

Hadimin Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa El-Rufai ya kara zama dan gudun hijira a siyasa sakamakon dakatarwar da aka yi masa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng