Kano: Minista Ya Faɗi Wanda Suke Son ba Takara a APC domin Ƙwace Kujerar Abba
- Minista a gwamnatin Bola Tinubu daga jihar Kano, Yusuf Abdullahi Ata ya ce APC na da shirin lashe zaben gwamnan Kano a 2027
- Ata ya ce babu sabani tsakanin Sanata Barau Jibrin da Murtala Sule Garo, kuma Nasiru Gawuna na iya takarar Sanatan Kano ta Tsakiya
- APC ta fuskanci kalubale daga NNPP tun bayan nasarar Abba Kabir Yusuf a 2023, yayin da 'yan jam’iyyar ke komawa NNPP
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Karamin ministan mai kula da gidaje da raya birane, Hon. Yusuf Abdullahi Atta, ya yi magana kan zaben a Kano.
Ata ya bayyana shirin APC na kwace kujerar gwamna a Kano bayan rashin nasara a zaben 2023 da ta gabata a jihar.

Source: Twitter
A wata hira da aka yi da shi a Freedom Radio Kano da Legit.ng ta bibiya, Ata ya bayyana cewa Barau zai tsaya takarar gwamnan jihar Kano.
Tasirin jihar Kano a siyasar Arewacin Najeriya
Jihar Kano ta kasance fagen daga tsakanin yan siyasa a fadin kasar duba da tasirin da take da shi a Arewacin Najeriya baki daya a bangaren siyasa.
Jam'iyyar NNPP ce ke mulki bayan kwace ragamar jagoranci daga APC mai mulkin Najeriya a zabukan 2023 da suka gabata.
An tabbatar Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben kan abokin takararsa wanda shi ne tsohon mataimakin gwamnan jihar, Dakta Nasiru Gawuna.

Source: Twitter
Ata ya fadi wanda zai tsaya takarar gwamna
Ata ya ce APC na sa ran Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, zai tsaya takarar gwamna a zaben 2027.
Sanata Barau wanda ya dade a siyasa yanzu ana kallonsa a matsayin wanda zai iya hade APC don kalubalantar NNPP.
Ya kuma karyata jita-jitar da ke cewa akwai sabani tsakanin Barau da tsohon kwamishinan kananan hukumomi, Hon. Murtala Sule Garo.
Kano: Alwashin da Ata ya ci na karbar mulki
Atta ya jaddada cewa APC a Kano ta hada kai, kuma sun mayar da hankali kan dawo da mulki a jihar a 2027.
Ya ce:
"Babu rikici tsakanin Barau da Garo. Muna fatan Garo zai tsaya takarar Sanata na Kano ta Arewa."
Ya kuma ce dan takarar gwamna na APC a 2023, Nasiru Gawuna, na iya tsayawa takarar Sanatan Kano ta Tsakiya.
Ata ya ce duk dan jam’iyya na da ’yancin tsayawa takara, amma su na goyon bayan Sanata Barau don ya jagoranci Kano.
Ata ya fadi dalilin Tinubu na naɗa shi minista
Mun ba ku labarin cewa karamin ministan gidaje da ci gaban birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya ce burinsa shi ne dawo da Kano ga jam'iyyar APC a 2027.
Yayin ziyararsa ta farko a Kano bayan rantsar da shi, Yusuf Ata ya bayyana cewa nadinsa na da muhimmanci wajen karfafa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Ya gode wa Shugaba Bola Tinubu, inda ya jaddada kudurinsa na ciyar da APC gaba a Kano ta hanyar ziyartar jihar duk da tarin aikinsa.
Asali: Legit.ng

