PDP ta Dura kan Atiku da Ya zama Jigo a Haɗakar Adawa Ta ADC

PDP ta Dura kan Atiku da Ya zama Jigo a Haɗakar Adawa Ta ADC

  • PDP ta Kano ta nesanta kanta daga haɗin gwiwar ADC, tana cewa ba ta wakiltar muradunta a siyasar Najeriya
  • Jam’iyyar ta caccaki Atiku Abubakar, tare da bayyana cewa haɗe wa da jam'iyyar haɗakar adawa ta ADC ba zai yi tasiri ba
  • PDP bukaci matasa su shiga jam’iyyar, tana mai cewa ita ce sahihiyar hanyar tabbatar da ceto Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoJam’iyyar PDP reshen jihar Kano ta nesanta kanta daga sabuwar kawancen siyasa da wasu tsofaffin ƴaƴanta suka shiga karkashin ADC.

Babbar jam'iyyar hamayyar ta caccaki waɗanda suka fita daga cikinta, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar
PDP ta caccaki Atiku Horo: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Atiku, wanda ya tsaya takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin PDP a zaɓen 2023, ya zo na uku a jihar Kano inda ya samu ƙuri’u 131,716.

Kara karanta wannan

An yi hasashen yawan ƙuri'un da Shugaba Tinubu zai samu a zaɓen 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bi bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP da kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC.

Jam'iyyar PDP ta raba kanta da ADC

Jaridar Daily Post ta kuma ruwaito cewa shugaban jam’iyyar PDP a Kano, Yusuf Ado Kibiya, ya bayyana hakan a wata ganawa da ‘yan jarida da aka gudanar a Kano ranar Litinin.

Ya ce kawancen da ake kokarin kafa wa ta karkashin ADC ba shi da wani tasiri ko muhimmanci, yana mai jaddada cewa PDP a Kano tana nan da ƙarfinta da haɗin kanta.

A cewarsa:

“Wannan kawance ba ya nuna matsayin PDP a Kano. Muna da haɗin kai, muna da hangen nesa, kuma mun himmantu wajen samar da shugabanci nagari da sauya rayuwar al’umma.”

PDP ta ce tana nan da ƙwarinta

Kibiya ya bayyana cewa PDP a Kano tana nan daram a ƙarƙashin jagorancin kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC), yana mai tabbatar da biyayyarsu ga shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa.

Kara karanta wannan

ADC ta yi bayani kan rashin sauya sheƙar El Rufa'i da Obi har yanzu

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar
PDP ta nesanta kanta da Atiku Horo: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Ya ce:

“Muna da cikakken biyayya ga kwamitin NEC na ƙasa, kuma muna tabbatar wa shugabancin jam’iyya cewa PDP a Kano na nan da haɗin kai da kuma hangen nesa.”

Shugaban jam’iyyar ya kuma bukaci jama’a, musamman matasa, da su yi rajista da PDP, yana mai cewa ita ce jam’iyyar siyasa mafi cancanta da za ta inganta makomar Kano da Najeriya.

Dino Melaye: 'PDP ta shiga wani hali'

A baya, mun wallafa cewa Sanata Dino Melaye, tsohon dan takarar gwamna a jihar Kogi, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, wanda ya girgiza siyasar Najeriya.

Melaye, a wata sanarwa da ya fitar ya ce jam’iyyar PDP ta rasa karfin da za ta iya ceto ‘yan Najeriya daga mawuyacin halin da suke ciki na matsaloli daban-daban a ƙasar.

Ya kuma zargi wasu manyan kusoshin jam’iyyar da haddasa durkushewar da jam’iyyar ke fuskanta a halin yanzu, saboda haka ya nemi sauya alkiblar siyasarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.