2027: Yaron El Rufai Ya Auna Peter Obi da Atiku a Sikeli, Ya Fadi Wanda Zai Iya Kayar da Tinubu

2027: Yaron El Rufai Ya Auna Peter Obi da Atiku a Sikeli, Ya Fadi Wanda Zai Iya Kayar da Tinubu

  • Ana ci gaba da maganganu kan 'yan takarar da za su fafata da mai girma Bola Tinubu idan har zai sake tsayawa a zaben 2027
  • Yaron Nasir El-Rufai, Bashir El-Rufai ya yi magana kan damarmakin da Peter Obi da Atiku Abubakar suke da ita kan kayar da Tinubu
  • Ya bayyana cewa Atiku na da karfi sosai, amma Peter Obi ya fi shi dama idan har ya yi abin da ya dace

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Bashir El-Rufai, ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi magana kan Atiku Abubakar da Peter Obi.

Bashir El-Rufai ya bayyana cewa Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, na da yuwuwar kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027 fiye da Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

An yi hasashen yawan ƙuri'un da Shugaba Tinubu zai samu a zaɓen 2027

Peter Obi na son yin takara da Tinubu a 2027
Bashir El-Rufai ya yi hasashen Peter Obi zai iya kayar da Tinubu Hoto: @PeterObi, @DOlusegun
Source: Facebook

Bashir El-Rufai ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, 31 ga watan Yulin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bashir El-Rufai a kan Peter Obi da Atiku

Bashir ya ce idan Peter Obi ya zaɓi mataimakin shugaban ƙasa daga Arewacin ƙasar nan da ke da ƙarfi da kima, zai fi Atiku Abubakar damar samun nasara a kan Shugaba Tinubu.

Ya ƙara da cewa Peter Obi zai zama babban kalubale ga burin Atiku na zama shugaban kasa, musamman saboda babban goyon bayan da yake da shi daga matasa da kuma karɓuwa daga jama’a da dama a ƙasa baki ɗaya.

“Atiku mutum ne mai ƙarfi sosai. Yana jin cewa lokaci ya yi da komai ke tafiya daidai da muradinsa."
“Ko da yake an ce shekarar 2019 ce ta fi zama lokacin da yake da damar hawa mulki, wannan na iya zama lokacin da ya dace da mutumin."

Kara karanta wannan

Shirin kayar da Tinubu ya kankama, an bayyana wanda zai iya gyara Najeriya a 2027

"Sai dai, yawan mutanen da ke goyon bayan Peter Obi da dumbin mabiyansa kalubale ne. Yadda matasa ke binsa na daga cikin damar da yake da ita."
"Peter Obi a matsayin dan takara tare da wani dan Arewa mai karfi sosai, zai kayar da Pablo a ranar zabe kafin mamarmu ta kasa, Gwaggo Remi ta gama masa abincin karin kumallo da misalin 12:00 na rana."

- Bashir El-Rufai

Bashir El-Rufai ya yi magana kan Atiku da Obi
Ana hasashen Peter Obi zai kayar da Tinubu Hoto: @BashirElRufai
Source: Twitter

Hadaka na ci gaba da samun karbuwa

Bashir El-Rufai ya bayyana wannan ra’ayin ne yayin da mahaifinsa, Nasir El-Rufai, ya kasance cikin manyan shugabannin adawa da suka kafa haɗaka a ƙarƙashin jam’iyyar ADC.

An dai ƙaddamar da hadakar ne a Abuja a ranar 20 ga watan Maris 2025 da nufin kayar da jam’iyyar APC mai mulki a 2027.

Sauran manyan ‘yan siyasa da suka shiga cikin wannan hadakar sun haɗa da Atiku Abubakar, Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi, tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark da sauransu.

Dalilin Peter Obi na kin shiga ADC

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta bayyana dalilin da ya sa Peter Obi da Nasir El-Rufai ba su shiga cikinta ba.

Kara karanta wannan

Ana shirya yadda za a shigo Arewa a kayar da Atiku, Kwankwaso da wasu jiga jigai a 2027

Sakataren yada labaran ADC na kasa, ya bayyana cewa an yi wa 'yan siyasan uzuri su ci gaba da zama a jam'iyyunsu.

Mallam Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa an bar su ne domin su kammala wasu abubuwan da suke yi kafin su shigo ADC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng