An Yi Hasashen Yawan Ƙuri'un da Shugaba Tinubu Zai Samu a Zaɓen 2027
- Wani 'dan APC da ya nemi tikitin shugaban ƙasa, Nicolas Felix ya caccaki haɗakar ƴan adawa a inuwar jam'iyyar ADC
- Felix ya bayyana cewa duka ƴan siyasar da suka haɗa kai ba za su iya ja da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a 2027 ba
- Ya yi hasashen cewa Shugaba Tinubu zai yi nasara a zaɓe mai zuwa da ƙuri'un da ba su gaza miliyan 15 ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Suleja, jihar Neja - Tsohon mai neman tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Nicolas Felix, ya yi fatali da haɗakar ƴan adawa ta ADC.
Felex ya bayyana cewa haɗuwar da ƴan adawa suka yi a inuwar jam'iyyar ADC ba barazana ba ce ga shirin shugaban ƙasa, Bola Tinubu na neman tazarce a 2027.

Kara karanta wannan
Shirin kayar da Tinubu ya kankama, an bayyana wanda zai iya gyara Najeriya a 2027

Source: Twitter
Jigon APC ya faɗi haka ne yayin da yake rabon ɗaruruwar litar man fetur ga marasa ƙarfi a garin Suleja da ke jihar Neja ranar Alhamis, cewar rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nicolas Felix ya nuna cikakken kwarin gwiwa cewa Tinubu zai lashe zaben shugaban kasa na 2027 da kuri’un da ba su gaza miliyan 15 ba.
Shin ADC barazana ce ga Shugaba Tinubu?
A ranar 1 ga Yuli, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, dan takarar LP a 2023 Peter Obi, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da wasu manyan ‘yan adawa, suka kaddamar da ADC a matsayin jam'iyyar haɗaka.
Da yake tsokaci kan wannan haɗaka, Felix ya ce duk da cewa babu laifi idan shugabannin adawa suka hada kai, ya na ganin kawancen zai tarwatse nan kusa.
A ruwayar Vanguard, Felix ya ce:
“A tsarin dimokuradiyya, dole ne a samu adawa, saboda haka ba ma jin tsoronsu kuma ba wata barazana ba ce a wurinmu, sai dai har yanzu ba mu ji manufarsu ba.
"Wannan kawance ba shi da wani hatsari a gare mu. Muna son su hada kai, amma kamar yadda na fada a baya, za su taru ne su tarwatse, domin ba su da wata manufa mai kyau. Ba gaskiya ba ce zuƙatansu.”

Source: Twitter
Ƙuri'u nawa ake sa ran Tinubu zai samu a 2027?
Dangane da zaɓen 2027 da ke tafe kuma, Felix ya ce yana da ƙwarin gwiwa cewa Tinubu ba zai gaza samun ƙuri'u miliyan 15 ba.
“Mu a APC lokaci kawai muke jira, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba zai samu kasa da kuri’u miliyan 15 ba, mun san hakan zai faru.
"Don haka babu wata barazana daga ADC ko wani kawance na ƴan adawa, daidai muke da su. Idan lokacin kamfe ya zo, za mu fitar da jerin nasarorin shugaban kasa."
- Nicolas Felix.
Kungiyar Arewa, ATT ta goyi bayan Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu goyon baya daga ƙungiyar Arewa Think Thank (ATT) yayin da ake shirye-shiryen tunkarar 2027.
Kungiyar ATT ta ce Arewa za ta goyi bayan Shugaba Tinubu, duba da ci gaban da gwamnatinsa ta kawo a fannin tsaro da ababen more rayuwa a yankin.
Ta bayyana cewa shugaban kasan ya aiwatar da ayyuka masu muhimmanci a yankin Arewacin Najeriya, wanda ya cancanci a bashi dama ta biyu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
